Imani da Samuwar Allah T.A:

Shin akwai shakku ne akan Akan samuwar Allah wanda ya halicci sammai da kassai? Ibrahim:10  Imani da samuwar Allah wani abu ne wanda yake a fili wanda babu kokonto a cikinsa, ko kafirai ma sun yi ikrari akan hakan. Inda Allah madaukaki yake cewa:"Da zaka tambaye su wane ne ya halicci samai da kassai, sanna ya hore rana da wata,? Tabbas zasu ce maka Allah ne, to me yasa suke yin karya?"Ankabuut:61

Don haka ne lokacin da aka tayar da manzo maitsira ya kirawo mutane ne akan bautar Allah shi kadai ba wai akan samuwar Allah ba. Domin kuwa dukkansu sun yi  imani da samuwarsa T.A. Dalilin wannan ikrari kuwa shi ne wani nau'in halitta da Allah ya yi wa mutum ta yadda zai iya gane cewa akwai Allah ba tare da wani kace-na ce ba, sai dai kawai idan mutum ya samu wata matsala ne wadda zata iya hana shi gane hakan.Allah yana cewa fitra ce wadda Allah ya halicci mutane akan ta."Rom:30

Dukkan wani mai hankali zai fahimta cewa lallai duniya tana cikin wani tsari na musamman wanda sakamkonsa ne take tafiya kamar yadda ya kamata hatta iskar da Dan Adam yake shaka. Sannan zai iya fahimatar cewa lallai duniya baki daya kasancewar tana cikin wani tsari guda daya ne, to lallai ta samu asali ne daga abu guda daya. Zamu iya gane wannan nau'in halitta da Allah ya yi wa mutum yayin da ya shiga wata matsala zaka ga yana neman taimako daga wani wanda yake ganin cewa shi kadai ne yake iya fitar da shi daga wannan matsala da bala'i da ya shiga a cikinsa.

Mutum tun bayan da ya zo duniya yana ganin abubuwa na ban al'ajabi wanda suke cike da duniya, mutum zai ga duniya gata nan ba ya ganin iyakarta shi kuma wani abu  ne wanda yake ganin kansa dan karami a cikin duniya , sannan ga ruwa nan da koguna marar iyaka idan dare ya yi zai ga sama cike da tarari gwanin kyau, sannan ga itatuwa nan masu tsawo da 'ya'ya da dai sauran abubuwan sha'awa wadan da suke cike da duniya.Sanan yana ganin ana halittar abubuwa sannan wasu suna tafiya da makamantan  hakan. Sannan mafi ban mamaki shi ne halittar shikansa yadda aka tsara shi cikin ban al'ajabi ta yadda duk da cigaban zamani har yanzu ba a gano sirrin da ke cikin halittar Dan Adam ba. Da haka ne mutum zai yi  ikirari da cewa Lallai akwai Allah madaukaki wanda shi ne ya halicci wannan duniya mai cike da ban mamaki.

Da wannan ne dan Adam zai yi saranda akan cewa lallai wanda ya yi wannan halitta ya cancanci a bauta masa. Akan haka ne Allah yake cewa:Ga Allah yake sujjada wanda ke  da sammmai da kassai"Ra'ad:16. sannan yana cewa:" lallai a cikin halittar sammai da kassai da sabanin dare da rana akwai abin lura ga masu hankali."Aali imran:188.

Dukkan mai hankali zai iya fahimtar cewa lallai dukkan abin  da ke duniya yana da  rai kuma yana fahimtar cewa akwai Allah kuma ya cancanci  a bauta masa.A kan haka ne Allah yake cewa:"yana tasbihi ga Allah wanda ke cikin sammai da kassai wanda yake mai mulki mai tarki kuma mabuwayi mai hikima." Jumu'a:1 Anan ne fa mutum yake nutsewa a cikin bautar Allah wanda yake mahaliccin kowa da komi. Anan kuma zai fara neman wanda zai kawo masa sako daga ubangiji madaukakin sarki. Ta yadda zai kusance shi ya nisanci abin ba ya so. Imam Ali a.s yana cewa: "ilimin mutane ya kasu gida hudu, ilimin sanin ubangiji, mutum ya san kansa, mutum ya san abin da hau kansa da sanin abin da yake kauce wa hanya ne." Sannan Imam Ali a.s. yana cewa:"Allah madaukaki ya aiko da mazanni domin su maida su zuwa ga abin  da aka halicce su akansa kuma su tunatar da su ni'imomin ubangiji, sannan su isar musu da hujjar ubangiji, sannan su fadakar da su sirrikan ubangiji dake a cikinsu a boye, sannan su nuna musu alamomin Allah dake cike da duniya."Nahjul balaga: huduba ta daya.

Allah ya sa mu dace, amin.