Mun yi imani ya wajaba a
kadaita Allah ta kowace nahya, kamar yadda ya wajaba a kadaita Shi a zatinSa,
kazalika Ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa
siffofinSa ainihin zatinSa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a
halitta da arzutawa haka nan babu mai azirtawa sai shi ba Shi da abokin
tarayya, a cikin dukkan kamala kuma ba Shi da tamka.
Kazalika mun
yi imani da kadaita Shi a bauta. Bai halatta a bauta wa waninSa ba ko ta wace
fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani ba a cikin nau'i na nau'o'in
ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba
ita ba na daga ibadoji.
Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to shi Mushiriki ne kamar
kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusancin wanin Allah Ta'ala,
hukuncinsa wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a
tsakaninsu.
Amma
abinda ya shafi ziyatar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa, da suka shafi
bayn Allah ba sa daga cikin
nau'in neman kusanci ga wanin Allah (ibada) kamar yadda wasu daga masu son suka
ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin
al'amarinsu. Sai dai ma wannan wani nau'i ne na kusanci ga Allah Ta'ala ta hanyar
kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya,
da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a addini, da kuma taimakon
fakirida makamantansu.
Don
haka zuwa gaishe da marar lafiya shi a kan kansa, kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan
samu kusanci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci ba ne ga marar lafiyar. Da zai
zamar da aikata wanann da niyyar bauta,ya zama bauta ga wanin Allah Ta'ala ko kuma shirka a
bautarSa. Kazalika sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a
cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa
kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa.Amma
kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan addini a matsayin kyawawan ayyuka a
shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin
tabbatar da Shi ba.
Manufa
ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar
yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin
nufin da su kawai shi ne raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma
girmama alamomin addinin Allah da tare da su Kamat yadda Allah yake fada a
cikin kur'ani mai girma"wancan duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah
to lalle wannan yana daga cikin takawar
zukata." Surar Hajj: 32.
Tabbatattun
siffofi kamarsu halitta da arzurtawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk
alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta Hakika, ita ce kasancewarSa mai
tafiyar da al'amuran bayinSa. Wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke
samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la'akari iri
dabam-daban.
Amma
siffofn da ake kira salbiyya wato korarru wadanda har wa yau ake kiran su
siffofn Jalala, siffofi girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya
guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarSa mai yiwuwar samamme ba wajibin
samamme ba, ma'anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore
rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu,
wato dai kore dukkan nakasa.
Sa'an
nan kuma tushen kore kasancewarSa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarSa
wajibin samamme, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na
kamala, don haka siffofin Jalala korarru dai a karshe suna komawa ne ga
siffofin kamala tabbatattu, Allah Ta'ala kuwa Shi kadai ne Makadaici ta kowace
fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawarwa a hakikaninSa
makadaici abin nufi da bukata.
Abin
mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra'ayin cewa siffofin tabbatarwa
wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru.
Saboda haka ne Siffofin da suke korarru. Saboda Ya yi masa wahala ya fahinci
cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka Ya kintata cewa siffofin
subutiyya, tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah, duk suna komawa ga
korarrun siffofi ne domin kawai Ya natsu da fadin kadaitaikar zati da rashin
yawaitarsa sai kawai ya auka a cikin abinda ya fi shi muni, domin zamar da
ainihin zati wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa, wanda ba shi da duk wata
nakasa, da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da samamme wajibin samuwa ba,
Ya sanya shi Ya aininin ma shi ne rashi kuma ainihin korarre, Allah Ya kiyayye
mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntubewar duga-dugai.
Kamar
kuma yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra'ayin cewa siffofinSa na
subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan
zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan
tarayya ke nan ga wajibin samamme, ko kuma kenan ya ce Shi mai hauhawa ne sashe
bisa sashe.
Sayyyidina
Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa Ya ce:
Cikar
Ikhlasi gare Shi kuwa shi ne kore siffofi gare Shi saboda shaidar cewa dukkan
abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukkan abin
siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya
gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi wanda ya tagwaita Shi kuwa
ya zamar da Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya
jahilce Shi."
Mazhabar Ja'afariyya wato Shi'a Isna Ashariyya ta dauki adalci a matsayin
jigo daga cikin ginshikan addini sai dai kuma alal hakika shi ba ginshiki ne
guda shi kadai mai zaman kansa ba sai dai shi yana kunshe ne a cikin siffofin
Allah Ta'ala kuma wajabcin samunsa ya lizimta tattara siffofin kyawu da kamala
saboda haka shi dai adalci yana daga cikin al'amuran tauhidi ne. Sai dai kuma
su Asha'irawa da suka saba wa Adaliyyawa, wato Mu'utazilawa da kuma `yan
Ja'afariyya, Shi'a Isna Ashariyya sai suka musa abu mai kyau da kuma mummuna
wadanda hankali ya tabbatar da su. Suka ce babu wani abu mai kyau sai wanda
shari'a ta ce mai kyau ne, babu mummuna kuma a sai wanda shari'a ta ce mummuna
ne kuma cewa idan da Allah zai dawwamar da mai biyayya a gidan wuta mai sabo
kuma a gidan aljanna to wannan ba mummuna ba ne saboda yana jujjuya al'amura ne
da ke karkashin mulkinSa kuma kamar yadda Alkur'ani ya ce: "Ba a
tambayarSa a kan abinda ya aikata su kuwa ana tambayar su" Surar Anbiya'i
aya ta 23. Su kuwa Adaliyyawa kuwa cewa suka yi: Mai yanke hukunci a wannan
al'amari shi ne hankali shi kadai dinsa, babu abinda zai shigar da shari'a a
cikinsa sai dai karin ta'akidi da kuma shiryarwa. Shi kuma hankali ya kebantu
da hukunta kyawun wasu ayyuka da hukumta munin wasu kuma yana hukumta cewa
danganta mummunan abu ga Allah abu ne da ba shi da kyau kuma ba zai yiwu ba
Allah Ya aikata shi domin Shi Mai hikima ne azabtar da mai biyayya kuwa zalunci
ne; zalunci kuwa mummunan abu ne kuma ba zai taba faruwa daga Allah Ta'ala ba.
Da haka ne suka tabbatar da siffar Adalci ga Allah suka kebance ta da ambato
banda sauran siffofn don ishara ga sabani da Asha'ira. Su kuwa Adaliyawa ta
hanyar ka'idar kyakkyawa da mummuna kamar yadda suke a hankali sun tabbatar da
wasu ka'idoji daga ka'idojin ilimin sanin Allah: Kamar su Ka'idar Tausasawa, da
kuma Wajabcin godiva ga wanda ya yi alheri da wata ni'ima, da kuma wajabcin
bincike da nazari a mu'ujiza, kuma a kan wadannan ka'idojin suka gina al'amari
tilasta wa da kuma `yancin zabi da ke daga cikin mafi wahalar matsaloli.
Domin karin bayani a duba: Aslus Shi'a da kuma Matarihun Nazar na Shaikh
Turaihi, Fasali na 4 shafi na 164.
[1] 1- Da dai sauran wadannan da Asha'irawa suka tafi a kai na daga maganganunsu na cewa Allah Ta'ala Ya aikata mummuna da maimaitawarSa na nau'o'in zalunci da shirka da dagawa da ketare haddi da kiyayya da yarda da su ya kuma so su -Allah Ta'ala Ya daukako ga haka, Tsarki ya tabbata gare Shi-, domin kara samun filla-fillan wadannan munanan ra'ayoyi'a duba littafi Nahjul Hak na Allama Hilli shafi na 85, da kuma sharhin Aka'ida da kuma Hashiyar na kistal, shafi na 109-113, da Milal wan Nahal Juzu'i 1 shafi na 85, 91 da kuma Al- Faslu na Ibin Hazm Juzu'i na 3 shafi na 66 da 69 da kuma Sharhit Tajrid na Kurshaji shafi na 373.