Akidarmu game da Takiyya:

An ruwaito daga Imam Sadik -Sadiku AhlulBait- (A.S.) a sahihin hadisi cewa: "Takiyya addinina ce[1] kuma addinin iyayena ce." Da kuma "Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi."[2]

Kazalika haka nan ta kasance taken Ahlul Bait (A.S.) wajen kore cutar da su kansu da kuma ga mabiyansu don kare jininsu sa'an nan da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hade kalmarsu da taro tsakaninsu.[3]

 Kuma Mazhabar Shi'a Imamiyya ba ta gushe ba ana saninta da takiyya ba kamar sauran jama'o'i da al'ummu ba, dukkan mutum kuma idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yada abinda ya yi imani da shi ko kuma fito da shi sarari babu makawa ya boye ya kare a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi'ar hankali ke hukunci da shi.

Abu ne sananne cewa Mazhabar Shi'a Imamiyya da Imamansu sun sha nau'o'in jarrabawa da matsa lamba da babu wata jama'a[4] da ta sha irinta. Saboda haka ne ya zamanto tilas gare su a yawancin lokuta su yi takiyya suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyana hakikanin abinda bayyanarwar ke jawowa a addini da kuma duniya. Saboda wannan ne suka bambantu daga wadanda ba su takiyya kuma aka san su da ita banda wasunsu.

Takiyya tana da hukunce-hukunce dangane da wajabcinta da rashin wajabcinta gwargwado sassabawan guraren tsoron cutarwar kamar yadda aka ambata a littafan malaman fikihu.

Takiyya ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya halatta kuma saba mata kan wajaba a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga addinin musulunci da jihadi a tafarkinsa, to a wannan lokacin sai a yi banza da dukiya kuma ba za a fifita rai ba.

Takiyya na iya zama haram[5] a ayyukan da ka iya wajabta[6] kashe rayuka masu alfarma ko kuma yada karya, ko barna a addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su ko kuma yada zalunci da ja'irci a tsakaninsu.

ma aukuwarta ba gagara badau ba ne.

An ruwaito daga Imam Sadik -Sadiku AhlulBait- (A.S.) a sahihin hadisi cewa: "Takiyya addinina ce6 kuma addinin iyayena ce." Da kuma "Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi."[7]

Kazalika haka nan ta kasance taken Ahlul Bait (A.S.) wajen kore cutar da su kansu da kuma ga mabiyansu don kare jininsu sa'an nan da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hade kalmarsu da taro tsakaninsu.[8]

Ko ta halin kaka dai takiyya a gurin Shi'a Imamiyya ba wai tana nufi zamar da su `yan wata kungiyar asiri ba ne domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi'a marasa fahimtar al'amura ke surantawa kuma ba sa dora wa kansu nauyin su zo su san ingantaccen ra'ayin daga garemu.9

Kamar kuma yadda ma'anarta ba ita ce a sanya addini ya zama wani sirri daga asirran da bai halatta a bayyana shi ba ga wanda bai dauke shi a matsayin addini ba, ta yaya zai zamanto haka alhali littafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu dangane da fikihu da hukunce-hukunce bayanai game da akida sun game duniya, sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al'umma da ke bin addininta?

E, gaskiya ce makiyanmu da ke nufin kiyayya da Shi'a sun munana amfani da takiyya sun sanya ta daya daga cikin abubuwan soke-soke ga Shi'a, tamkar ka ce ba sa wadatuwa har sai dai in an sassare wuyansu domin a ga bayansu baki daya a wancan zamanin da cewa mutum Shi'a ne kawai ya isa ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Bait daga Umayyawa da Abbasawa hatta zuwa Zamanin daular Usmaniyya.

Idan sukan mai suka ya dogara ne da abinda yake zaton cewa suka ba halas bane a addini to sai mu ce masa:

Na Farko: Mu dai masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S.) mu muna bin shiriyarsu ne su ne suka umarce mu da ita, kuma su ne suka farlanta ta a kanmu a lokacin bukata, kuma ita tana daga addini a gurinsu kuma lalle ka ji hadisin Imam Sadik (A.S.) da yake cewa: "Duk wanda babu takiyya gare shi babu addini gare Shi."

Na Biyu: Shar'anta ta kuma ya zo a Alkur'nai mai girma, wato fadar Allah Ta'ala cewa: "Sai dai wanda aka tilasta shi zuciyarsa kuwa tana natse da imani." Surar Nahli: 106.

Wannan aya ta sauka ne game da Ammar bin Yasir wanda ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan musulunci. Da kuna fadin Allah Ta'ala: "Sai dai in kuka ji tsoron su don kariya." Surar Ali Imran: 28.

Da kuma: "Kuma wani mutum daga mutanen fir'auna yana mai boye Imaninsa Ya ce." Surar Gafir: 28.


[1] Ishara ga maganar Allah Ta'ala Yana mai Shaidawa Manzonsa Muhammadu (S.A.W.A) cewa "Ya saukar da littafi a gare ka da gaskiya Yana mai gaskata abinda ya gabace shi kuma Ya saukar da Attaura da Linjila" Ali Imran: 3.

Da kuma da dama makamantanta da ke nuna cewa Manzon Allah (S.A.W.A) da Alkur'ani sun zo suna masu gaskata Annabawa da shari'o'i da suka gabata.

[2] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 174 hadisi na 12, Mukhtasarul Basa'irud Darajat shafi na 101 da al-Mahasin Juzu'i na 1 shafi na 397 hadisi na 890.

[3] Al- Kafi Juzu'i na 2 shafi na 172 hadisi na 2, da kuma Al Fikhul Mansub ilal Imam Ridha (A.S.) shafi na 338.

[4] Takiyya ita ce boye gaskiya da suturce imani da ita, da boye wa wadanda ake da sabani da su, da rashin fitowa sarari gare su da abinda zai jawo cutarwa a addini ko a (abin) duniya. Kuma tana daga cikin abubuwan da wasu ke kin Shi'a saboda ita, domin jahiltar ma'anarta da suka yi da kuma guraren da ta dace da su da hakikaninta, idan da sun tsaya daidai sun dakanta sun yi hakuri sun hakarkur-kurtar da sun san cewa takiyya ba wai ta takaita kawai ga Shi'a ba ne kuma ba su kebantu da ita su kadai ba, sai dai ita aba ce La budda sai da ita a bisa hukuncin hankali kuma a kanta dabi'un dan Adam suka tattara, hankali kuma shi mai mata jagora ne ilimi kuma shi ne mai kula da ita kuma ba'a taba rabuwa da su biyun koda gwargwadon kiftawar ido, domin kowane mutum dabi'arsa ne ya kare kansa ya kiyaye rayuwarsa.

Sahihul I'itikad daga Musannafatu Shaikh Mufid Juzu'i na 5 shafi na 137, Aslus Shi'a wa Usuliha shafi na 315, Waki'ut Takiyya indal Mazahib wal Firakil Islamiyya wadanda ba Shi'a Imamiyya ba, na Sayyid Samir Amidi, a ciki akwai bayani game da takiyya da kuma cewa batu game da ita bai kebanta ga Shi'a Imamiyya ba kawai.

[5] As- Shi'atu wal Hakimun, Shaikh Muhammad Jawad Mugniya.

[6] Domin ya zo daga Imam Bakir (A.S.): "An sanya takiyya ne domin a kare jini da ita idan kuwa har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce." Wasa'ilus Shi'a Juzu'i na ll shafi na483 hadisi na 1.

[7] Domin hadisi ya zo daga Imam Ridha (A.S.) "Don an sanya takiyya don kare jini ne kawai idan har ta kai ga jini to ba takiyya ba ce."

[8] Ta'alikin kausari a littafin Isfirayini, Attabsira fida din shafi na 185 da kuma Nash'atul Ash'ariyya wa Tatawwuriha shafi na 87-88.