Ziyartar kaburbura
- kaburburan Annabi da na Imamai da katange su da kuma yin gine - gine a kansu
na daga cikin manyan al'amura da mazhabar Shi'a Imamiyya (Masu bin Imamai 12)
ta kebantu da su kuma suna bayar da dukkan abu mai tsada da mai sauki cikin
imani da dadin zuciya.
Asalin duk wannan kuma shi ne wasiyyar Imamai
da kuma zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da take
da shi mai yawa a gurin Allah Ta'ala,[1] saboda kasancewarta mafifiyar
ayyukan biyayya da ibadu bayan ayyukan ibadu wajibai da kuma cewa wadannan
kaburburan na daga cikin mafifitan guraren amsa addu'a da juyawa ga Allah
Ta'ala.
Kuma suka sanya ta daga cikin ainihin cika
alkawura ga Imamai, domin, "ga kowane Imami akwai alkawarinsa a kan majibintansa
da mabiyansa, da kuwa cewa daga mafificin cika alkawari, ziyartar kaburburansu
na daga mafi kyawun cikawa, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da
kuma gaskata abinda suka kwadaitar a kai, to su Imaman nasu za su kasance masu
ceto gare su ranar Alkiyama."[2]
A cikin ziyarar kaburbura akwai fa'idoji na
addini da zamantakewa da suka sa Imamanmu himmatuwa da ita, domin a halin cewa
a lokacin da take kara kulla walaya da soyayya tsakanin Imaman da mabiyansu
tana kuma sabunta tuna hadisansu da dabi'unsu da jihadinsu saboda gaskiya kuma
tana hado kan musulmi wadanda suke a warwatse ta taro su guri guda, domin su
san juna kana kuma ta dasa ruhin jawuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu da
yankewa zuwa gare shi, da bin umarce-umarcenSa tana kuma cusa musu hakikanin
tauhidi a cikin ma'anonin addu'o'in ziyarorin da ke cike da fasaha wadda aka
samo daga Ahlul Bait (A.S.) tare da koya musu tsarkin musulunci da sakon
Muhammadu (S.A.W.A) da abinda ya wajaba a kan musulmi na daga matabbatan
halayen kwarai, da kankan da kai ga Mai tafi da halittu, da gode wa
ni'imominSa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu'o'in da
aka ruwaito wadanda bayaninsu ya riga ya gabata.
Hatta wadansunsu ma sun tattara ne a kan mafi zurfin addu'o'i da madaukakansu kamar
ziyarar "Aminullah" wato "Amintaccen Allah" wadda aka
ruwaito daga Imam Zainul Abidina (A.S.) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa
Amirul Muminin[3](A.S.).
Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito
suke fahimtar da matsayin Imamai (A.S.) da irin sadaukarwarsu a tafarkin
taimakon gaskiya da daukaka kalmar addini da dagewarsu a ibadar Allah Ta'ala
gashi kuma sun zo da salon larabci zalla, da fasaha madaukakiya, da ma'anoni
masu sauki wadanda kowa da kowa yake fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma'anonin
tauhidi kuma mafi zurfi tare kuma da addu'a da yankewa zuwa gare shi Ta'ala.
Alal hakika ita tana daga cikin mafi ingancin
laduban addini bayan Alkur'ani mai girma da Nahjul Balagha da kuma addu'o'in da
aka ruwaito daga garesu (A.S.) domin a cikinta an kunsa dukkan sanin Imamai
(A.S.) a takaice dangane da abinda ya shafi wannan sha'ani na addini da gyaran
zuciya.
Sa'an nan kuma a cikin ladubban ziyarar akwai
koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da wadannan ma'anonin addini
madaukaka wato irinsu daukaka tsarkin ruhin musulmi, da koya wa ruhinsa
tausasawa ga fakiri, da sanya shi tausasawa ga fakiri, da iya zama da jama'a da
kyawun hali, da son cudanya da jama'a, domin daga ladubanta akwai abinda ya
kamata a aikata kafin a fara shiga cikin gurin makabartar domin ziyartarsa.
Daga nan kuma akwai abinda ya kamata a yi a
tsakiyar ziyarar da kuma bayan ziyarar. A nan za mu kawo wasu daga cikin
wadannan laduban domin fadakarwa a kan abubuwan da take nufi kamar yadda muka
fada:
Ya Allah Ka sanya mani haske da tsarki gare, da kuma tsari wadatacce daga dukkan cuta da ciwo da kuma dukkan bala'i da musiba kuma Ka tsarkake zuciyata da gabobina da kashina da namana da jinina, da gashina da fatata, da bargona da kashina da kuma abinda kasa ta rage shi daga gare ni, kuma Ka sanya mai shaida gare ni ranar bukatata da fakircina da talaucina."
2-
Ya sanya mafi kyawun da mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa
da tsaftatattun tufafi abu ne da mutane ke so wa junansu lokacin bukukuwa, kuma
hakan na kusantar da su ga junansu tare da sanya soyayya a tsakaninsu, yana
kara sa musu daukaka da jin daukaka a zuciyarsu da jin muhimmancin bukin da
suke halarta.
Abu da ya kamata mu jawo hankali gare shi a
wannan koyarwa shi ne ba a wajabta cewa dole ne mutum mai ziyara ya sanya mafi
kyawun tufafi baki daya ba dungum, a'a sai dai ya sanya mafi kyawun abinda yake
da iko a kai domin ba kowa ba ne zai iya yin haka, kuma akwai kuntatawa ga
raunana wadda tausayawa ba ta bukatar a yi haka, wannan ladabin dai hakika ya
gwama tsakanin abinda ya kamata na ado da kuma mafi kyawun tufafin, da kuma
kiyaye yanayin fakiri da kuma mai rauni.
3- Ya sanya abinda ya saukaka gare shi na turare,
kuma fa'idarsa tamkar ta sanya sabin kaya ce.
4- Ya
yi sadaka da abinda ya saukaka gare shi, kuma fa'idar sadaka a irin wannan
al'amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimakawa ga gajiyayyu da kuma
sanya ruhin tausasawa gare su.
5- Ya tafi yana cikin natsuwa da kwanciyar hankali
yana mai takaita ganin idonsa. Abinda ke cikin wannan irin natsuwar da girmama
alfarmar wannan gurin da kuma wanda ake ziyarta din da kuma mai da hankali ga
Allah Ta'ala da yankewa zuwa gare shi, da kuma abinda ke tare da haka din na
nesantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munanawa
shashensu daga sashe a bayyane yake a sarari.
6- Ya
yi kabbara yana cewa "Allahu Akbar" ya yi ta maimaitawa yadda ya so,
kuma mai yiwuwa ne a wasu ziyarorin a kayyade kabbarar zuwa dari. Akwai fa'ida
a cikin yin haka wadda ke sanya wa ruhi jin girman Allah Ta'ala, da kuma cewa
babu wani abu da ya fi Shi girma, da kuma cewa ziyara ba wata aba ba ce illa
ibadar Allah da girmama Shi da daukaka Shi ta hanyar raya alamun Allah da
karfafa agginin Shi.
7-
Bayan kammala ziyarar kuma ga Annabi ko kuma ga Imamai to sai ya yi salla
akalla raka'a biyu nafila kuma domin ibada ga Allah kawai, saboda ya yi godiya
a kan muwafakar da Ya yi masa ya kuma bayar da
ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar.
A cikin addu'ar da aka ruwaito wadda mai
ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abinda zai fahimtar wa mai ziyarar
cewa wannan salla dai da duk abinda da ya aikata na Allah ne Shi kadai da kuma
cewa shi ba ya bauta wa wani baicin Shi kuma ziyarar ba wata abu ba ce face
wani nau'in neman kusanci gare Shi Ta'ala.
"Ya
Allah gare Ka na yi Salla, gare Ka na yi ruku'u, gare Ka na yi sujada, Kai
kadai ba Ka da abokin tarayya, domin babu salla da ruku'u da sujada sai dai
gare Ka, domin Kai hakika ne Allah babu abin bautawa sai Kai. Ya Allah Ka yi
dadin tsira ga Muhammaddu da zuriyar Muhammadu, kuma Ka karba mini ziyarata,
kuma Ka ba ni abinda na roka, domin Muhammadu da zuriyarsa masu tsarki."
A cikin irin wannan addu'ar akwai wani nau'in
ladabi da ke bayyana manufofin Imamai da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar
kabari ga duk wanda ke son ya san hakika, da kuma irin abinda masu jahilta ke
kagawa yayin da suke raya cewa wai ziyartar kaburbura ibada ce gare su da neman
kusanci gare su da kuma cewa shirka ce da Allah a ibada.
8-
Daga ladubban ziyara akwai cewa:
Mai ziyarar ya lizimci kyanutata abota da duk
wanda ya zama tare da shi, da kuma karanta magana, sai dai abinda yake alheri,
da yawaita zikirin l43 Allah, da kankan da kai, da yawaita salla, da
salati ga Annabi Muahmmadu da Zuriyar Muhammadu kuma ya runtse idandunansa,
kuma ya gaggauta zuwa gurin mabukata daga cikin yan'uwansa idan
ya ga abubuwa gare su sun yanke, kuma ya taimaka musu, ya kuma nesanci abinda
aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayyar da ta hada da
rantse-rantse.[5]
Sa'an nan kuma alal hakika ziyara ba wata aba
ba ce face salati ga Annabi ko kuma ga Imami saboda imani da cewa su "suna
raye a gurin ubangijinsu ana arzuta su."[6] Don haka su suna jin
magana kuma suna amsawa, kuma ya wadatar ka ce alal misali: "Assalamu
Alaika Ya Rasulallah." ("Amince Ya tabbata gare ka Ya Manzon
Allah".)
Sai dai kuma abinda ya fi shi ne ka karanta
abinda aka ruwaito game da addu'o'in ziyara daga Ahlul Bait, Saboda abinda ke
cikinta kamar yadda muka ambata na daga madaukakan manufofi, da kuma fa'idojin
addini, da zurfin ma'anarsu da fasaharta da kuma abinda ke cikinta na daga
addu'o'i masu zurfi da mutum yake juyawa ga Allah Ta'ala da su.