Akidar mu   Game da  Zalunci.

Ketare haddi ga wani da zaluntar mutane na daga cikin mafi girman abubuwan da Imamai (A.S.) ke girmama yawan zunubinsa, kuma yin haka na tafiya ne daidai da yadda ya zo a Alkur'ani na daga tsorotarwa game da zalunci da kuma kushe shi kamar yadda ya zo a fadar Allah Ta' ala:

"Kada ka tsammaci Allah Mai mancewa ne game da abinda azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai Yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna za su fiffito." (Surar Ibrahim: 42)

Abinda ke kai kololuwar bayyana munin zalunci da kore shi ya zo a maganganun Amirul Muminin Aliyu Bin Abi Talib (A.S.) kamar maganar sa shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga maganarsa a khutuba ta 219 a Nahjul Balagha.

"Wallahi idan da za a ba ni sammai bakwai da kuma abinda ke karkashin falaki-falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa in kwace mata sha'irin da ta jawo ba zan aikata ba."[1]

Wannan shi ne matukar abinda zai iya surantawa a kan kame kai daga zalunci da kuma nesantar ja'irci da kushe shi.

Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan konon sha'iri koda kuwa an ba shi sammai bakwai to yaya halin wanda ke yin dumu-dumu da jinin musulmi, yana handame dukiyoyin jama'a, yana tozarta mutuncinsu da karimcinsu ? Yaya za a auna tsakaninsa da cikin Amirul Muminin ? Kuma yaya matsayin zai kasance a fikihunsa (A.S.)

Wannan shi ne irin ladabin da Ubangiji ya yarda da shi wanda addini ke bukatarsa daga kowane mutum.

E, lalle zalunci na daga mafi girman abubuwan da Allah Ya haramta, don haka ne yake da matsayi na farko a hadisai da addu'o'in Ahlul Raiti (A.S.) wajen zarginsa da kuma kore mabiyansu daga gare shi.

Wannan ita ce siyasarsu (A.S.) kuma a kanta salon rayuwarsu yake har ma dangane da wanda ke ketare haddinsu, yake wa matsayinsu hawan kawara.

Kissar Imam Hasan (A.S.) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuwa ya kyautata masa ya tausasa masa har sai da shi ya ji laifin abinda ya aikata.[2]

Ka dai rigaya ka karanta abinda ya gabata a addu'ar Shugaban masu Sujada na daga madaukakan ladubba game da yafewa ga wadanda suka ketare haddi da nema musu gafara, wanda kuma shi ne matukar daukakar zuciya, da cikakkiyar 'Yan Adamtaka, koda yake ketare  haddi ga azzalumi gwargwadon irin yadda ya ketare din ya halatta[3] a shari'a, kamar kuma yadda yin addu'a a kansa ya halatta mustahabi ne, amma halattar abu daban kai hatta a gurin Imamai ma (a.s.) yawaita addu'a a kan azzalumai na iya zama keta haddi da zalunci, Imam Sadik (a.s.) na cewa: " Bawa na iya zama wanda aka zalunta sai ya yi ta yin addu'a har sai ya zamanto azzalumin."[4]

Wato har ya zamanto azzalumi a kan addu'arsa game da azzalumin, saboda ya waitata da yawa.

Subhanallah! Ashe yin addu'a ga azzalumi zai zama zalunci idan ya ketare iyaka? To menene halin wanda ya fara da zalunci da ketare iyaka, yana ketare haddin mutane, yana keta mutumcinsu, yana kwashe dukiyarsu, ko kuma ya yaudare su ya aukar da su a cikin halaka, ko ya kuntata musu ya cutar da su ko kuma ya yi leken asiri a kansu? Menene halin makamantan wadannan a fikihun Ahlulbait (a.s.).

Lalle makamantan wadannan su ne mutane wadanda suka fi kowa nesa da Allah Ta'ala, suka kuma fi tsananin sabo da ukuba, da mafi munin ayyuka da dabi'u.


[1] Nahjul Balagha, maganarsa game da nesantar mutum zalunci.

[2] Ka duba Manakib na Ibin Shahri Ashub Juzu'i na 4 shafi na 19 ya kawo wannan kissa ne daga Mubarrad Ibin A'isha, Ya ce: "Wani Mutumin Sham ya gan shi a kan abin hawa sai ya kama la'anar sa amma Shi Imam Hasan (A.S.) bai rama ba. Yayin da ya gama sai Imam Hasan (A.S.) ya fuskance shi ya yi dariya ya ce: "Ya dattijo ina tsammani kai bako ne, kuma la'alla an ruda ka ne, idan da ka nemi bain mu da mun biyar da kai idan da ka roke mu da mun ba ka, idan da ka nemi mu shiryar da kai da mun sa ka a hanya, da ka nemi mu dora ka a kan abin hawa da mun hawar da kai, idan da ka kasance kana jin yunwa ne da mun kosar da kai, idan ka kasance tsirara ne da muntufatar da kai idan da ka kasance mabukaci da mun wadatar da kai idan kuma kai korarre ne da mun sauke ka, idan da ka koro abin hawanka zuwa gurinmu da kai bakonmu ne har zuwa lokacin da ka tafi kuma kana iya dawowa, domin muna da guri wadatacce da fuska sakakkiya da dukiya mai yawa." Yayin da mutumin yaji maganarsa sai ya fashe da kuka, sa'an nan ya ce ni na shaida cewa kai Halifan Allah ne a bayan kasarSa, Allah shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa, kuma kai ka kasance kai da mahaifinka wadanda na fi ki a cikin halittun Allah, amma yanzu kai kai ne wanda na fi so a cikin halittun Allah. Daga nan sai ya kora abin hawansa zuwa cikin karafkarsa ya zama bakonsa har zuwa lokacin da ya tafi kuma ya zamanto ya yi imani da soyayyarsu.

[3] Surar Bakara: 194.

[4] Al-Kafi Juzu'i na 2 shafi na 250 hadisi na 17, ikabul A'amal: shafi na 274.