Akidarmu Game da Taimakekeniya da Azzalumai.

Saboda girman hatsarin da ke tattare da zalunci da muninsa har Allah Ta'ala Ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su.

"Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai har wuta ta shafe ku kuma ba ku da wasu majibinta baicin Allah sa'an nan ba za a taimake ku ba."

Wannan ita ce ladabtarwar Alkur'ani kuma ladabtarwar Ahlul-Bait (A.S.), ruwayoyi da dama da suka zo daga gare su game da hana karkata zuwa ga azzulumai, da sadarwa da su, da yin haraka tare da su a cikin kowane irin aiki da taimakekeniya da su ko da kuwa daidai da kwatankwacin tsagin dibino. Babu shakka mafi girman abinda aka yi hani a kansa a musulunci da kuma ga musulmi shi ne sassauci ga azzalumai da rufe ido game da miyagun ayyukansu, da mu'amala da su, ballantana ma cudanya da su da taimaka musu da taimaka musu a kan zaluncinsa.

Babu abinda ya jawo wa al'ummar musulmi bala'o'i illa wancan karkacewa daga kan tafarki madaidaci da gaskiya, har addini ya yi rauni tare da shudewar kwanaki, karfinsu ya zagwanye suka kai cikin halin da suke a yau. Addini ya zama bako musulmi kuma ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani Majibinci baicin Allah kuma ba su da wani mataimaki gare su hatta a kan mafi rauni daga makiyansu da mafi kaskanci masu yi musu hawan kawara, kamar Yahudawa wulakantattu, ballantana kuma a kan kiristoci mafiya karfi.

Lalle Imamai (A.S.) sun yi jihadi wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, sun kuma tsanantawa mabiyansu game da tafiya tare da ma'abuta zalunci da ja'irci da cudanya da su. Abinda aka ruwaito daga gare su game da haka a wannan babin ba zai kididdigu ba, daga ciki akwai abinda Imam Zainul Abidin (A.S.) Ya rubuta zuwa ga Muhammad Bin Muslim Az-Zuhri bayan ya gargade shi game da taimakon Azzalumai a kan zaluncinsu?

"Ashe kiransu gare ka yayin da suka kira ba su sanya ka dan dutsin nika suna juya zaluncinsu da kai ba, da kuma bango da suke ketarawa ta kanka zuwa bala'insu, da tsani na bi ta kai zuwa batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malami, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu da mafiya karin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen nuna ingancin barnarsu, da shigi da ficin kebatattu da gama gari zuwa gare su, abinda suka ba ka ya karanta matuka a kan wanda suka karba daga gare ka, abinda suka rayar gare ka ya karanta kwarai akan wanda suka rusa maka ka duba zuciyarka, domin babu wani mai duba ta baicin kai, ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya[1]."

Girman kalmar "Ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya", ya yawaita mutum yayin da son ransa ya gallabe shi sai ya mance darajarsa da ke tare da shi da sirrin karamarsa, wato ma'ana ya ji cewa shi abin tambaya game da ayyukansa, kuma ya kaskanta abinda zai gudana daga ayyukansa sa'an nan kuma ya raya cewa shi ba shi ne wanda za a yi masa hisabi ba a kan ayyukansa, wannan na daga cikin asirran zuciyar mutum mai umarni da mummuna, don haka Imam ya so ya fadakar da Zuhri game da wannan sirrin na zuciya wanda ke kunshe a cikinsa domin kada wahami ya yi galaba a kansa har ya yi sakaci game da abinda ya ke kansa game da kansa.

Mafi zurfi game da haka kuma game da suranta haramcin taimakekeniya game da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (A.S.) wanda shi ya kasance daga cikin mabiyan Imam din ne, masu ruwaito hadisi daga gare shi wadanda aka amince da su ya ce kamar yadda Kasshi ya ruwaito a littafinsa na Ilimin sanin masu ruwaya kamar yadda yake bayanin rayuwar Safwan:

Na shiga gare shi sai ya ce mini: "Ya Safwan duk wani abu daga gare ka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu guda daya."

Na ce: A sanya ni fansa gare ka, wane abu?

Ya ce: "Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Haruna Rashid.

Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai alfahari ko dagawa ko don farauta, ko wasa, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato don hanyar Makka- kuma ba na daukar sa ni da kaina sai dai ina tura shi da barorina."

Ya ce: "Ya Safwan kudin hayarka na kansu? "

Na ce: E, a sanya ni fansa gare ka.

Ya ce: "Shin kana so su wanzu har su dawo su biya ka kudin hayarka?"

Na ce: "E".

Ya ce: "To duk wanda ya so wanzuwarsu to yana tare da su, duk wanda ya kasance tare da su to ya kasance mai shiga wuta."

Safwan ya ce: "Sai na tafi na sayar da dukkan rakuma na baki daya."[2]

Idan har son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu a kan wannan matsayin yake, to yaya kuma ga wanda yake hada kai da su a kan zalunci, ko kuma yake taimaka musu a kan ja'irci, kuma yaya halin wanda yake shiga cikin jama'arsu ko kuma yake aikinsu ko kuma yake shiga tawagarsu, ko kuma yake bin umarninsu?


[1] Tuhful Ukul shafi na 275.

[2] Rijalul Kasshi shafi na 440 hadisi na 828.