|
||||||||||||||||
|
Tarihin Rayuwar Shehin malamin Ayatullahi uzma Muh.Fadhil LankaraniHaihuwarsa:An haifi Malamin a shekara ta 1935 a shahararren birnin ilminnan wato
Qom da ke kasar Karatunsa:Bayan gama karatunsa a matakin farko, sakamakon sha’awarsa da shaukinsa ga karatun addinin musulunci, bai yi wata-wata ba sai ya shiga makarantar nan ta nazarin addinin musulunci dake garin Qom. Kasancewar malamin mai hazakar gaske, ya kamala kartunsa matakin farko da na biyu, wato muna iya kwatanta shi da matakin digri, mastas da daktarin a cikin shekara shida a fanning shari’ar musulunci, a lokacin yna dan shekara 19 inda ya shiga cikin bincike da nazarin yadda ake fito da hukunce-hukunce daga kur’ani da sunnar manzo s.a.w.a. (ijtihad). Ya yi wannan bahsi ne kuwa a wajen mashahurin Malamin nan Ayatullahi Burujardi. Sakamakon kananan shekarunsa ga kuma kaifin fahimta, shi ya sa, ya samu kulawa ta musamman daga manyan malamai da sauran daliban da suke tare.Don kuwa kowa daga cikin dalibai yana so ya kasance suna bahsi tare don neman karuwa daga fahimatar da Allah ya yi masa. Daya daga cikin abokan karatunsa wanda shi ma ya kasance mai tsananin hazaka ne, wato shehin malamin nan Sayyid Mustafa khumaini dan Imam khumaini wanda Allah ya yi wa cikawa shekaru da suka gabata. Malamansa:Malamin yakasance tare da Ayatullahi burujardi har tsawon shekara 11 don koyon yadda ake fito da fatawoyi daga kur’ani da sunna kamar yadda muka fada a baya.sannan ya kasance tare da Iman khumai har tsawon shekara 9, shi ma duk a wannan fagen. Malamin bayan nazarin shari’ar musulunci ya halarci darussan falsafa da tafsirin kur’ani wajen babban malami tafsirin nan wato Ayatullahi Tabataba’i. Sakamakon kokarin malamin ya sami shedar zama malami mai ba da fatawa(mujtahidi) daga malaminsa Ayatullahi Burujardi wanda shi ne mai bad a fatawa a duk duniyar mabiya mazhabar ahlulbait a.s. kamar yadda yake a hauza ana samun wannan sheda ne daga irin wadannan manyan malamai.Wannan daraja ta zama mujtahidi kuwa muna iya kwatanta da matakin na saman farfesa. Malamin ya sami wannan matsayi ne kuwa yana dan shekara 25. Karantarwarsa:Malamin bayan ya kai wannan mataki na ilimi sai kuwa ya dukufa wajen koyar da nazarin shari’ar musulunci a matakai daban-daban na wannan fanni. Ya zuwa yanzu kuma yana cigaba da koyarwa a mataki na horar da mujtahidai a babbabr cibiyar nazarin addini musulunci dake Qum.Ya zuwa yanzu ya yi shekaru 35 yana koyarwa a wannan cibiya. Sakamakon kwarewarsa kuwa a fannin koyarwa da karfin iliminsa ya sanya manyan malamai masana masu nazarin shari’ar musulunci ruguguwa zuwa wajen darasinsa, wanda yawan daliban da ke halartar wannan darasi ya kai yawan mutum 700 a cikin dakin karatu guda daya. Mubarazarsa da hukumar sha ta :Daga lokacin da Imam khumaini ya fara fito na fito da hukumar dagutu ta sha, Ayatullahi Lankarani ya tsunduma cikin yaki da wannan azzalumar gwamnati karkashin kira Imam.Sakamkon haka ne kuwa ya shiga cikin matsaloli daban-daban, wanda ya kai an daure shi lokutta da dama. Daga karshe ya kai ga korar sa daga garin Qom wanda ake ganinsa wata cibiya ce ta addini, inda malamai suke aika sakonninsu cikin sauri su isa ga al’ummar kasar Iran.Bayan an kore shi zuwa wata gabar kogi da ake kira gabar Lange wanda daga karshe ya koma garin Yazd inda yakasance a can tsawon shakara biyu. Matsayin marja’iyya (mai ba da fatawa):Bayan rasuwar Imam khumaini musulmai da dama sun koma ansar fatawarsu daga malamin.Bayan wani lokaci kuma sai Allah ya yi wa Ayatullahi Araki rasuwa wanda shi ne Bababn malami mai ba da fatawa a lokacin, Sai majalisar koli ta malaman cibiyar nazarin shari’ar musulunci da ke Qom, suka ba da sanarwar komawa zuwa gare shi don neman fatawoyi, Kamar yadda yake a tsari dama su ne suke sanar da wanda ya kamata a koma zuwa gare shi don amsar fatawa. A halin yanzu malamin yana daya daga cikin manyan malamai wanda musulmin duniya suke amsar fatawa daga garesu. Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwar malamin. Da fatan Allah ya kara masa tsawon kwana da lafiya, ya kuma tsare mana shi, don yi wa addinin musulunci hidima kamar yadda yake shi ne, aikin bayin Allah. Amincin Allah ya tabbata garemu baki daya. |