Sakonnin Marja'in addini maigirma Ayatullahi Fadhil Lankarani dangane da shahadar Sayyida Zahra(a.s.)
1 Da sunan Allah mairahma maijinkai
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da
amincin Allah sun tabbata ga manzon tsira Muhammad s.a.a.w. da iyalansa tsarkaka,
musamman Siddikatu shahida Sayyida Fatimatu Zahra a.s. hushin Allah ya tabbata
akan makiyansu baki daya.
Wadannan kwanuka sun dace da lokacin zagayowar shahadar
sayyida Zahra a.s. wadda take wata hakika ce wadda ta gagari masana da masu
bincike su fahimci hakikanin samuwarta a.s. An ambace da Fatima domin ta gagari
halittu sanin hakikaninta. Itace wadda manzon Allah yake hushi da hushinta haka
nan Allah madaukaiki yake hushi da hushinta, sannan Allah da manzo suna farin
ciki da farin cikinta. Sayyida Zahra a.s. bayan kasancewarta a matsayin cibiyar
ma’abota kisa (mayafi) sanann itace matattarar Ahlulbait a.s. acikin ayar tathir
(33:Ahzab). Nufin Allah ya ta’allaka akan ya tafiyar da dukkan kazanta daga
ahlul bait ta hanyar samuwarta. A matsayinmu na masu alfahri da kasantuwarmu
mabiya wannan sayyida mai girma. Ya zama tilas akanmu a wannan zamani mu fahimci
hakikanin koyarwar wannan sayyida mai girma da daukaka, domin kada mu kasa
aiwatar da nauyin day a hau kanmu. Saboda haka dole ne malamai a dukkan
garuruwan musulmi da masu wa’azi su bada muhimmacin dangane da sanar da al’ummar
musulmi hakikanin wannan baiwar Allah, bayan tarurruka da zaman makokin akan
shahadar sayyida Zahra a.s su fadarkar da al’umma akan hakikanin koyarwa sayyida
a.s. Alhamdu lillah mazhabar shi’a tare da amfani da dalilai da hujjoji da suka
dace da hankali sun dauki nauyin wannan al’amari mai muhimamanci.
A yau makiya sun fahimci cewa idan har musulmi suna bisa
akidunsu na hakika, to ba zasu iya samun dammar iko akan al’amuransu ba, don
haka suka yi aniyar gusar da akidun gaskiya na musulunci ta yadda wata rana
musulmai zasu iya daukar makoki akan shahadar sayyidu shuhada a.s. da kuka akan
shahadar Zahra wani abu ne marar amfani da manufa, ko su yi shakku akan zaluncin
da aka yi wa Zahara a.s. duk da yake cewa wani abu ne wanda yake tabbace a
bayyane acikin tarihin musulunci.
Makiya su sani idan suna nufin su sanya shakkau da shubha
akan shahadar Zahra a.s. to sam ba zasu iya kawar da zalunci da aka yi akan
zahra a.s. ba abayan wafatin manzo a.s. gajartar rayuwarta da hudubobin ta
gabatar a massalacin manzo wadanda suke cike da hujjoji akan zalunci da aka yi
mata, da kukan dare da rana da ta kasance acikinsa, da kariyar da ta dunga yi
akan wilayar Imam Ali a.s. dukkan wannan dalilai ne akan zaluncin da aka aiwatar
akanta a.s. Ta wanan fuskar duniyar musulmi da mijinta wanda ya ka sance acikin
bakin ciki a koda yaushe.
Juyin musulunci na Iran ya samo asali ne daga muhimmanci
da al’ummar Iran suke bai wa wannan al’amari na shahadar Zahra a.s. da
makamantansu. Saboda haka a yau daya daga cikin abubuwan da zasu kare wanann
juyin musulunci shi ne bai wa irin wadanan abubuwa muhimmanci. Saboda haka
wajibi ne kan mumimani su bai wa ranakun shahadar Sayyida Zahra a.s. muhimmanci,
ka da su bari wannan waki’a mai muhimmanci ta bace tsakanin abubuwan yau da
kullum. Musammam ranar 3 Jumada thani ranar da jamhuriyar musulunci take yin
hutu na kasa baki daya wanann yana nuna muhimmancin wannan al’amari ga
jamhuriyar musulunci ta Iran. Muna fata Allah madaukaki ya yi mana muwafaka mu
kasance acikin wadanda suke bai wa wannan al’amari muhimmanci ta yadda zamu samu
ceton sayyida zahara a.s. da ‘ya’yanta tsarkaka.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga dukkan ‘yan’uwa
muminai da rahmarsa.
Muhammad Fadhil Lankarani 30-5-80
2 Da sunan Allah mairahma maijinkai
Allah madaukakin sarki yana cewa:Lallai wadan da suke cutar
da Allah da manzonsa tsinuwar Allah ta tabbata akansu acikin duniya da lahira,
sannan ya yi musu tanadin azaba mai kuna” Ahzab. Sannan manzo yana cewa Fatima
tsoka cedaga gareni duk wanda ya cutar da ita ya cutar da ni.
Daya daga cikin muhimmin alfahrin shi’a shi ne
kasantuwar shugaban matan duniya da suke da ita wato sayyida Zahra a.s. wadda
take da matsayin Isma. Bisa ga ayar Tathir wadda ta sauka akan mutane biyar
wanda a samansu shi ne manzo s.a.a.w. Allah madaukaki ya tafiyar da kazanta daga
gare su, sayyida Zahara tana daya daga cikin wadannan bayin Allah wadanda Allah
madaukaki ya tsarkake su. Saboda haka fahimtar hakikanin zatin sayyida Zahra
wani abu ne wanda yake da wahala ga sauran alumma.
Sayyida Zahra Itace Farkon wadda ta samu rabon shahada
daga cikin iyalan gidan manzo s.a.a.w. Sannan daga cikin alfahrin sayyida shi ne
ita ce uwar sauran ahlul bait a.s.
Sayyida Zahra a.s. ta kasance wata mata ce wadda ta
kasance a cikin matukar zalunci da bakin ciki, musamman rashin mahaifinta manzo
s.a.a.w. ammam acikin wannan halin ne wanda zai yi wa mutum wahala ya iya koda
Magana ne amma sayyida Zahra a.a.s ta kasance ta aiwatar da huduba mai girgiza
zukata a gaban masu iko na wanann zamani abin da ya gagari masana fahimtar
matukar wannann al’amri, wato ta yaya ya ksance mace zata iya aiwatar da wannan
huduba mai ratsa zukata a kuma cikin wannan yana yi da ta samu kanta. Hudubar
sayyida Zahra a masallacin manzo ta kunshi abubuwa masu dama wadan da suka hada
tauhidi, annabta da imamanci, haka nan ta yi tsokaci da Allah wadarai da abin
da masu neman duniya suka aikata na kin gaskiya sannan suka rufe bakinsu akan
ganin zalunci da aka yi wa wasunsu.
Babu shakka dole ne mu yi ikirari bayan shekara dubu da
dari hudu da cewa, ba mu iya sanin hakikanin wannan baiwar Allah ba, abin da
kuma ya fi komi bakin ciki shi ne ta yadda wasu ta fuskar dalilai daban-daban
suke neman su yi inkarin wannan zalunci da aka yi wa‘yar ma’aiki Zahra a.s.
Babu shakka wanann al’amari zai yi wuyar fahimta ga
sauran mutane, ta yadda wata mata sakamakon kamalar da ta samu ya zamana
yardarta yardar Allah madaukakin sarki ce.
Lokutta da dama an rububuta abubuwa da dama wadanda basu
da hakika akan sayyida Zahra a.s. bisa adawa da kiyayya, wanda dukkan mai son
gaskiya zai yi bakin cikin da hakan. Babu shakka al’amari hadin kai tsakanin
al’ummar musulmi wani abu ne mai muhimmanci wanda shugaban juyin musulun Imam
kohmain ya yi kira zuwa gare shi, amma wannan ba yana nufin cewa shi’a su bar
abinda suke da imani da shi ba, sannan su tsaya suna kallon irin karya da kage
da ake yi akan sayyida Zahra a.s. babu shakka abin da Imam yake nufin shi ne
al’ummar musulmi su hada kansu wuri guda ta yadda zasu tunkari makiya musulunci
baki daya, ta yadda makiya musulunci kada su samu damar cutar da muslunci.
Saboda haka ya wajaba ga al’umar musulmi kwansu da
kwarkwata ranar litinin wadda ta dace da uku ga Jumada Thani bisa ingantacciyar
ruwaya, wadda take nuni da cewa a wannan ran ace Sayyida Zahra a.s. ta yi
shahada, saboda haka ne gwamnatin musulunci ta Iran ta bayar da hutu domin masu
juyayi da wannan rana su fito domin nuna bakin cikinsu akan wannan zalunci da
aka yi wa Zahra a.s. wanda ya sanya ta yi shahada a wannan rana. Saboda haka
musulmi ya kamata su bayar da muhimmmaci wajen gudanar da juyayi a wannan rana
fiye da kowane lokaci. Babu shakka nuna ko-in-kula akan wannan al’amari yana
tasirinsa marar kyau ga dan Adam.
Tsarki ya tabbata ga dukkan bayi na kwarai.
Muhammad fadhil Lankarani 18-5-81.
3 Da sunan Allah mairahma maijinkai
Dangane da abin da na rubuta shekarar da ta gabata game da
abin da ya shafi shahadar Sayyida Zahra a.s. to wnanan cigaba ne akan hakan.
Girmama wanann rana ta shahadar Zahara wadda ita ce ta farkon acikin shahidan
iyalan gidan manzo s.a.a.w. yin hakan yana matsayain jaddada wilayarmu zuwa ga
iyalan gidan manzon tsira s. da nuna godiyar bisa cikar ni’mar da Allah
madaukaki ya yi mana na cika addininsa.
Fatima Zahra wadda yardarta yrdar manzo kuma yardar Allah
s.w.t ce,kuma fushinta fushin Allah da manzo ne.
Fatima zahara a.s wadda A’imma dinmu suke alfahri da
kasantuwar mahaifiya ce a gare su, wadanda su ne cikakkun mutane kuma halifofin
Allah a bayan kasa. Fatima a.s. duk da cewa ba ta rayu ba tsawon lokaci amma ta
yiwa shi’anci hidima ta har abada, Sayyida Zahra a.s. ta tsoratar da makiya ta
hanyar hudubarta mai raza zukata.
Zahra a.s. ta isar da bakin cikinta na rashin mahaifinta
da zalunci da aka yi wa mijinta, ta hanyar kuka acikin gari da wajen madina
wanda har yanzu akwai tasirin muryar kukanta a garin madina.
Mu ‘yan shia muna alfahri da cewa mun koyi hakikanin
addini daga ‘ya ‘yan sayyida Zahra a.s. ilimin da ya dace da hankali kuma ya
dace da kowane zamani da kowane wuri. Sanann yana kunshe da dukkan bukatocin bil
adama. Ta hanyar koyarwar ‘ya’yan Fatima ne al’ummar Iran suka samu damar
tsayuka da fito na fito akan azzalumai, ta yadda suka iya samun ‘yanci da izza.
Ta wannan fuskar ne makiya musulunci suka dauki alkawarin
cewa lallai sai sun raba mutane da Ashura, sha’aban da ramadhan ta haka ne zasu
iya cimma mummunan nufinsu.
Anan tunatar da wannan batu wani abu ne wanda ya wajaba,
rayar da wadannan ranaku da yin juyayi akan wadannan ranaku yana da ga cikin
ayyukan Imam khomain wanda babu wani wanda yake shakku akan haka. Sanann yin
hakan ba ya da akala da batun hadin kan al’ummar musulmi. Wanann hadin kai wani
abu wanda Ayatullahi Burujardi shima yake matukar ba shi muhimmanci, amma wannan
ba yana nufin cewa shi’a su manta da akidunsu ba, abin nufi anan shi ne hadinkan
musulmi ta yadda zasu fuskanci makiya addinin musulunci, wadanda bisa jagoranci
sahaniya suke neman suga bayan musulmi da muslunci baki daya.
Saboda haka ya zama wajibi akan akan al’ummar musulmi a
ranar uku ga wata wanda jamhuriyar musulunci take bayar da hutu don gudanar da
juyayin shahadar Zahra a.s. su gabatar da zaman makoki dangane da wannan rana.
Ta yadda zasu yi gungu a bisa tituna suna nuna bakin cikinsu da wannan rana.
“Suna so su gusar da hasken Allah, amma Allah ya ki domin yana son cika haskensa koda kafirai sun ki”.
Muhammad Fadhil Lankarani 7-5-1382
4 Dasunan Allah mairahma maijinkai.
Mun samu kanmu acikin kwanukan shahadar Fatima a.s. wadda
ta kasance mahaifiyar babanta wato manzo kuma mahaifiyar A’imma a.s. wadda ta
kasance cibiya ce ga iyalan gidan manzo, kuma wata alama ce ta sirrin halittar
Allah madaukai, wadda hatta ‘yan shi sun gagara su san hakikanin samuwarta.
Wadda take hakika ce ta haske wadda ta hanyar adawa da zalunci ta buya ga
muatane har ya zuwa ranar kiyama.
‘yan shia kai da dukkan halittu da mala’iku suna alfahri
da samuwar Zahra a.s. Alkauthar wadda ta zama sanadin wanzuwar addinin manzo
s.a.a.w. wanda ta haka ne duniya ta cika da koyarwar ‘yan ‘yanta tsarkaka. Shin
da Zahra ba ta ksance ba, wane irin duhu duniya zata kasance acikinsa.. bias
umurninin ayar nan da take cewa “ka ce ban tambaye ku lada ba sai son
makusantana” ta wajabta wa dukkan al’umma soyayya ga iyalan gida manzo wato
ahlul bait a.s. wadda a samansu it ace Fatimatu Zahra a.s. wannan wani taklifi
ne wanda ya hau akan dukkan al’ummar musulmi a kowane lokaci kuma a ko’ina suke,
saboda haka bai kebanta da wasu mutane ba sabanin wasunsu
Soyayya ga Zahra a.s. tana matsayin girmama manzon Allah
ne s.a.a.w. haka tunawa da musibar da ta auku akan sayyida Zahra a.s.
Saboda haka babu wani lokaci da zamu iya mantawa da wanann
musiba, sannan tarihi yana mai sheda akan irin zalunci da aka yi wannan baiwar
Allah Zahra a.s. Imam amirul Muminin Ali a.s. bayan wafatin Zahra ga abin da
yake cewa: “Bakin ciki da nake acikinsa wani abu na har abada wanda ba zai wuce
ba”. Shin tare da wannan Magana ta Imam a.s. shi’ar Ali a.s. suna iya kasancewa
ba tare da wanann bakin ciki ba?
Bisa wanann ne ya wajaba kan shi’a ranar laraba uku ga
watan Jumada thani wanda ya yi daidai da ruwaya ingantacciya cewa ita ce ranar
shahadar sayyida Zahra a.s. su fito kwansu da kwarkwata domin nuna juyayinsu da
wannan rana, acikin godiyar Allah jamhuriyar musulunci ta sanar da wannan rana a
matsayin hutu domin masoya Zahra a.s. su samu damar nuna juyajyinsu akan wannan
rana.
Muhammad Fadhil lankarani 29-4-1383
5 Da sunan Allah mairahma maijinkaiAmincin Allah ya tabbata ga siddikatu shahida Azzahra a.s.
Mun kasance acikin kwanakin shahadar sayyida Zahra a.s.
Fatimatu zahra a.s. wadda take masoyiyar manzon tsira Muhammad s.a.a.w. sannan
matar Shugaban muminai Ali a.s. kuma mahaifiyar Aimma goma sha daya a.s.
Sayyida Zahra a.s. ita ce shugaban dukkan matan duniya. Duk
da cewa acikin kur’ani Allah madaukaki dangane da Maryam a.s. yana cewa:”Na zabe
ki akan matan duniya” amma kamar yadda ya zo a ruwa abin nufi shi ne Allah ya
zabeta acikin matan duniya ta yadda ta haifi Isa a.s. ba tare da miji ba. Wannan
al’amari ya kebanci sayyida Maryam a.s. Amma damgane da girma da daukakar Zahra
a.s. ta fuskar ilimi da tsarki da isma da bautar Allah ta daukaka akan dukkan
matan duniya .
Saboda haka ya wajaba ga al’ummar musulmi ranar uku ga
watan Jumada thani wanda ya dace da ranar shahadar sayyida Zahra a.s. su
gudanar da taruka domin nuna juyayi da wannan ranar, domin nuna muhimmanci
wannan rana jamhuriyar musulunci ta bayar da hutu domin al’ummar musulmi su samu
damar gudanar da wannan taruka na makokin shahada Siddika zahra a.s. don haka
wannan ranar Ashura ce ta biyu. Saboda haka kamar yadda ya kasance a shekarun
baya ta yadda wannan al’umma masoya Zahra a.a.s suka aiwatar da nauyin da ya hau
kansu na girmama wannan rana, anan ya kamata in mika godiyata ta musamman ga
al’ummar musulmi. Babu shakka a fili yake girmama duk wani abu da ya shafi
sayyida Zahra a.s. girmama manzon ne s.a.a.w. sannan yana matsayin ladar
manzancin manzo s.a.a.w.
Al’ummar Iran mai girma ta hanyar riko da igiyar ahlul
bait a.s. kuka iya samar da daular musulunci a Iran kuma da wanann ne hukumar
musulunci ta Iran take samun karfin tafiya. Saboda haka ya zama tilas mu fahimci
cewa sirrin nasararmu shi ne riko da hanyar ahlul bait a.s. da kuma kai kukanmu
zuwa ga ruhunan wadanan bayin Allah ahlul bait a.s. saboda haka zatinmu shi ne
shi’anci da musulunci na gaskiya. Da fatar Allah madaukaki ya sanya mu
karakashin inwar zahra a.s.
Muhammad Fadhil Lankarani 15-4-1384
|