|
Sakon Ayyatullahi Alnkarani dangane da Kai harinAmerika a Kasar Iraki
Duniyar yau da dukkan musulmi suna cike da bakincikin zalunci
Amerika.gwamantin da take da'awar dimokradiyya da Karen hakkin dan Adam,
amma tarihinta yana cike da zalunci ta keta hakkin dan adam.amerika tare da
shirin la'ananniyar gwamnatin yahudawan isra'ila, tayi nufin kai haring a kasar
musul wato Iraki,don haka dole ne musan gurinsu na asali wanda shi ne,ta wannan
hanyar ne Yahudawa zasu samu damar iko akan wurare masu tsarki na ziyara kamar
Najaf Da karbala da daui sauransu.Al'ummar duniya a fili suna ganin duk da
rashin amincewar al'ummar dduniya tare rashin amincewar majalisar dinkin
duniya,amma duk da hakan 'yan koren Isra'ila wato Amerika da Engiland suka samu
damar samun ikon a ksar musulmi kamar Iraki.
Alummar musulmi Iraki duk da wahala da zaluncin da suka gain da hukumar
ba'as ta saddam, haka ma Jamhuriyar musulunci ta Iran ta gabatar da matasanta
domin kare musulunci daga zaluncin Saddam har tsawon shekara Takwas,amma har
yanzu tana fama da gyaregyaren banna da Saddam ya yi mata tare da Taimakon
wadannan Kasashen musamman Amerika. Shin Al'ummar Iraki zasu samu ceto ne daga
wadannan ya'n koren Isra'ila ko kuwa su ne da kanasu zasu tashi su nemi
hakkinsu?Lallai Amerika ta sani cewa sakamakon wannan zalunci nata ta sa dukkan
duniyar musulmi makiyanta kuma masu shirin fito na fito da ita .Haka nan Manyan
cibiyoyin nazarin addinin musulunci da manyan malamai na duniyar musulmi da
manyan masana na kasashen musulmi suna fata wannan matsala ta kasar Iraki a
warwareta ta hanya mai sauki.Amma Amerika wadda take shirin yaki da dukkan
kasashen musulmi to lallai su sani kuma tarihin Iraki ya nuna masu cewa al'ummar
musulmi ba zasu taba daukar kaskanci da zalunci ba.Sannan Amerika ta sanii ta
kawo kanta mahallaka ne da kanta.
Sannan yah au kan dukkan shuwagabannin kasashen musulmii da su ba wannan
matsala muhimmanci har zuwa lokacin da muka ga mutanen Iraki sun fita daga
wannan bakin zalunci na Amerika.Nima ta bangarena ina mai bayyanar da bakin
cikina dangane da wannan al'amari mai kunar rai,Sannan ina mai neman taimako
daga Imamuz-zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa don taimakon wadan da aka
zalunta.Sannan ya daukaka kalmar musulunci kamar yadda Allah ya yi mana
alkawali, kuma hannun Allah yana bias hannnayensu.
Muhammad Fadhil Lankarani
28-12-1382.Hij.shamsi
|