Sakon Ayatullahi Alnkarani dangane da shahadar Imam Askari da kuma
wasu malamai a Najaf
Da sunan Allah mai rahma.
Ina si in yi nuni zuwa ga abubuwa guda biyu a nan, na farko shi ne, gobe
Laraba wanda zai zama ran ace ta tunawa da kama wasu manyan malamai wadan da
Sadam ya ba da umurni a ka kama su wanda muta ne suna tsammanin cewa an
kaisu ne gidan kurku,duk da cewa ga dukkan alamu azzalumin nan mai
busassar zuciya wato Sadam ya gama da su ne,duk da cewa akwai wani
tsammanin cewa wasu daga cikinsu wadan da suke matasa ne 'yan uwansu na sa ran
cewa za'a sakosu su koma zuwa ga gidajensu.
Bayan wannan abin da ya faru na Iraki
kwanannan wato na korar sadam daga mulki sai ya bayyana cewa bayan an je
gidajen kurkuku sai a ka samu cewa ai lallai sadam duk ya gama da malaman nan
wadan da yawansu ya kai mutum dari da hamsin. Da yawa daga cikinsu Iraniyawa ne
wadansu kuma daga cikinsu ma sun kai matsayin marja'iyya.Sannan kuma akwai da
yawa daga cikinsu daga iyalin wani marja'i guda daya ne aka kama.
Wasu daga cikinsu sun kasance abokaina ne, shekarun wadan nan mutane kuwa
maban-banta ne wanda ya fara daga 40-90.Daga karshe ya tabbata wannan azzalumi
mashayin jinin bayin Allah duk ya gama da su.
Dangane da ilimimsu kuwa ni da kaina na san wasu daga cikinsu wadan da
suke lallai manyan malamai ne kuma marubuta amma duk an yi asararsu.wanda daga
cikin rubuce-rubucensu anan wajen karatunmu mun anfana da bahsinsu a cikin babin
hajj.
Don haka gobe Laraba domin tunawa da kuma girmama matsayin iliminsu an ba
da hutu a duk cibiyoyin nazarin addinin musulunci(hauza) dake cikin kasar
nan da sauran kasashe, domin wannan al'amari maigirma.
Dagutu zamaninmu ma haka ya so ya yi anan iran
ya gama da dukkan malamai da cibiyoyin nazarin addini, sai Allah bai ba shi iko
ba, sakamakon haka ma sai Imam khomaini (r.a) tare da taimakon Allah ya kawar da
shi daga cikin wannan al'umma.
Don haka dagutu duk inda yake abu guda ne, Dagutun Iraki
ma haka ya so ya gama da hauza a cikin iraki har ya zuwa karshen mulkinsa, kuma
lallai ya yi mana babban gurbi.Sai dai kaico yanzu mene ne sakamakonsa muna iya
cewa Allah ya fara kama shi kafin zuwa ga azabar lahira wadda itace mafi
tsanani, wato sakamakon kisan da zaluncin da ya yi wa malamai bayin Allah a
cikin iraki da yakin da janyo wa mutanen iran da na irakin baki daya
asarar rayuka da dukiya. Ya Allah kafin azabar lahira ka azabtar da shi
sakamakon zaluncinsa.
Saboda haka dangane da wannan ne gobe dukkan makarantu hutu ne saboda da
girmama wannan rana.
Amma abu na biyu da zanyi nuni zuwa gare shi, shi ne, ranar Asabar ranar
takwas ga wata ne wanda ya yi dai dai da shadar Imam Askari a.s wanda
kuma shi ne mahaifin Imamul hujja a.s, don haka ne kasuwanni ma gobe hutu ne.
Saboda haka dole ne mu kiyaye wannan ma'ana ta shahadar Imam mu kuma girmama
wannan hakikakanin girmamawa, saboda haka ranar Asabar babu karatu hutu
ne, Idan Allah T.A ya bam u iko zamu cigaba da karatu ranar Lahadi.
Wassalam.
|