Sakon Ayatullahi Lankarani Dangane da Kisan "yan shi'a a kuwaite Pakistan
Ina mai bayyana bakin cikina dangane da harin da Kafirai makiyya
Allah suka kai a kan al'ummar musulmi "yan shi'a suna cikin salla wanda ya janyo
shahadar mutane da yawa daga ciki.
Makiyya Ahlul-bait da 'yan shi'a su sani cewa irin wannan hare-haren ba
komi zan janyo wa wannan mazahaba ba illa cigaba da karfafawa.Don haka ina mai
mika gaisuwata zuwa ga Imam zaman Imamul mahdi Allah ya gaggauta bayyanarsa, Ina
kma mai mika gaisuwata zuwa ga Manyan malaman shi'a da sukkan al'ummar musulmi
na wannan bangare na pakistan, dangane da wannan bakin zalunci da ya auku ga
al'ummar musulmi.Sannan inamai kira ga hukumar Pakistan da ta gaggauta kama
wadan da suke da hannu a cikin wannan mummunan aiki, da kawar da duk ire-iren
wadannan kungiyoi masu aiwatar da irin wannan aiki.
Daga karshe ina mai rokon Allah ya tayar da wadan nan shahidai tare da Imam
Ali da "ya'yansa a.s.
Muhammad Fadhil Lankarani
1 jumada Ula 1424.
|