Sakon Ayatullahi Lankarani Dangane da sha biyar ga watan sha'aban 1423.
Bayan godiya ga Allah da satali ga manzon tsira da iyalansa,sha biyar ga
sha'ban ranar haihuwar haske ce wanda shi ne hujjar Allah ta karshe a bayn kasa,
ranar da ta zama digon farko na tabbatr da adalci a bayan kasa,ranar Allah
madaukaki ya baiwa bayinsa babbar ni'ima ya bas u mai ceto wato Imam Mahdi a.s.
Duk da cigaban dan Adam a rauwa wadda bata da iya kuma kullun sai karuwa
take,ta ydda dan Adam bai takita ba kawai a bias kasa hae zuwa bias duniyar wata
ya kai, dan Adam ya samu cin nasarori da dam ta wannan fanni,amma kaico duk
yadda dan Adam ya samu Karin cigaba ta fuskar kimiyya da fasaha kuma yakan kara
nisa day an adamtada ya kuma kara kaifin zalunci da nisa da hankalin da Allah ya
ba shi don rayuwar da ta dace.
A yau al'ummar duniya tana ganin yadda zalunci manyan kasashen duniya
wadan da suke kokarin zama ba wanda zai iya shiga a gabansu.Tare da labewa da
yaki da ta'addanci suna zaluntar al'umma masu raini marasa karfi, sannan suna
tsorata duniya da karfin da sule da shi,don haka ne dunoya take cike da bukatar
maiceto daga Allah domin ya cece su daga wannan bakin zalunci ya kafa hukuma ta
Allah ta yadda adalci zai game duniya baki daya.
Dan Adam ya nuna cewa duk da cigaban day a samu amma ya kasa tabbatar da
dalci a cikin al'umma,haka ma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun kasa kwato
hakkin masu rauni daga azzalumai, a hakikanin gaskiya ma sune suka kafa
su.Shinkasance mutum ya cigaba da shan wahalhaloli irin wadan nan har abada?Shin
Allah ba wata hanaya da tanada ta yadda zai cececi dan adam daga wannan zalunci,
ko kuwa Allah ya kasa ne? muna neman tsari daga wannan.Lallai ba haka ban e
wannan ya saba wa hadafin halittar dan Adam.Sannan alkawalin akan samun nasarar
addinin Allah akan sauran addininai ya saba wa hakan,hikimar Allah tana nuni da
cewa lallai dole ne a samu wani wanda yake shi ne mafi sani da adaukaka a cikin
mutane ta yadda zai dauki wannan nauyi na tabbatar adalci a bayan kasa.A yau
dukkan shi'a suna cike da gurin tabbatar gwamnain adalvci ta hanya Imam mahdi
a.s ta yada adalcin Allah zai tabbata kuma zalun yak au a doron kasa. Duk da
yake a shekarun nan na karshe an samu wannan kulawa dangane da Imam mahdi a.s.
daga sauran musulmin duniya.Don haka ne mutane suka cigaba da bayyanar alamomin
bayyanar Imam da yadda hukumarsa zata kasance.Don haka ta bangarena ina gabatar
da godiyata ta musamma zuwa ga wadan da suke irin wannan hidima.Sannan ina kira
zuwa gare su da dage kwarai da gasket wajen bayyana wannan hakika tare da kula
da samo bayanai daga littafai masu inganci.Tare da godiyar Allah muna da
littafai da dama a wannan fage,wadan da ba mu da shakku akan su.Muna da manayan
ingantattun littafai da suke bayani dangane da Imam a.s, wadan da suka hada tun
daga haihuwarsa hae ya zuwa hukumarsa, saboda haka masu bukata kuma masu zuciya
tsarkakka suna iya samunsu a ko,ina.
Ina kira ga dukkan musulmi masu himma da dage wajen fadada wannan tunani a
duk inda suke ta yadda al'umma zasu samu ilimi da kuma soyayya ga wannan Imam
a.s.Ta yadda Imam zai tabbatar da adalci ya kuma kawar da zalunci a doron kasa.
A yau aiki kowane musulmi shi ne,ya yi imani da cewa dukkan ni'imomi da
albakatu da muke samu dukkansu suna zuwa ne daga wannan shugaban adalci Imam
Mahdi a.s.Fadar Allah madaukaki"Ba don hujja ba da duniya ta ruguje da
abin da ke cikinta".Don haka dukkan albarku suna zuwa ne daga gare shi, saaboda
haka abin day a hau kanmu don godiya ga wannan ni'imomi shi ne, mu yi kokari
birane da kauyukla mu raya wanna akida da farkar da mutane daga barcin gafala da
suka shiga da koma wa zuwa ga Allah, ta hanyar gabatar da taruka don bahsi
dangane da Imam a.s. Don haka ina kra ga shuagabanni da su yi kokar su rika
shirya taruka a cikn gida da waje don raya wannan al'amari da yardarm Ubangiji
zai amfanar cikin sauri ta yadda mutane zasu samu masaniya dangane da Imam da
kuma hukumarsa.
Ina rokon Allah madaukaki da kawar da dukkan abin zai hana
bayyar sa a.s.Ta yadda zai 'yantar da al'ummar musulmi musamman sha'a daga
wannan bakin zalunci da tabbatar da hukumar adalci a bayan kasa insha
Allah ta a'la.
Muhammad fadhil lankarani
Sha'ban 1423.
|