Istihala
Daya daga cikin jinin dake fito ma mata shi ne jinin istihala,saboda haka
idan mace ta ga jinin istihala ya fito mata ta zama mai istihala kenan.
Mas'ala ta 392:Jinin istihala mafi yawan lokacin yana da ruwan dorowa
kuma yana da sanyi,sannan kuma ba tare da turowa yake fitowa ba,sannan kuma
jinin ba ya da kauri,duk da yake yana iya zama launinsa ja ne ko kuma mai kauri
da zafi a wani lokaci, sannan kuma ya kaance mai turowa yayin fitarsa, amma mafi
yawan lokaci yana da siffofin da muka yi bayani a sama.
Mas'ala ta 393:a takaice duk jinin da yake fitowa daga mace wanda kuma
ba jinin haila ko na haihuwa ba ne kuma ba na ciwo ba ne wannan jinin na
istihala ne koda bay a da siffofin da muka yi bayani.
Mas'ala ta 394:Istihala tana da nau'I guda uku:
Ta daya:Istihala kadan,wannan tana kasancewa ne jinin da zai fito daga mace
ba shi da yawa, idan da zata sanya auduga to zai bata saman audugar ne kawai,
wato ba zai shiga cikinta ba.
Ta biyu:Matsakaiciya:wanan kuwa jinin zai iya ratsa audugar ya shiga cikinta,
ammam ba zai bayyana a bayanta ba.
Ta uku:Mai yawa.wanna kuwa it ace wadda jinin yana da yawa ta yadda zai iya
zaece audugar har ya taba abin da aka daure adugar da ita.
Hukuncin istihala:
Mas'ala ta 395:Idan mace tana cikin istihala kadan, dole ne yayin
kowace salla ta yi alwalla,sannan ta wanke saman al'aurarta idan jinin ya bata
sama, sannan ihtiyat wajib shi ne ta canza audugar da ta sanya.
Mas'ala ta 396:Idan mace taga jinin istihala matsakaiciya kafin ta yi
salla ko kuma tana cikin sallar,dole ne ta yi wanka sannan ta yi sallar.Amma mai
istihala matsakaiciya idan ta yi wanka kafin sallar asuba, ba zata kara yi ba
sai kuma wata asubar, anan kawai yayin kowace salla sai ta gabatr da ayyukan da
muka fada a sama na mai istihala kadan.Amma idan da bisa mantuwa ya kasance bata
yi wankan ba yayin sallar asuba, anan dole ta yi wankan lokacin sallar azahar da
la'asar., haka nan idan ta manta ko kuma dagangan ba ta yi wankan ba yayin
sallarazahar da la'asar, anan dole net a ty wankan yayin sallar magrib da isha.
Mas'ala ta 397:Amma mai istihala mai yawa bayan ayyukan mai kadan da
matsakaiciya zata kara da wadan ayukan kamar haka,zata canza audugar da ta sanya
yayin kowace salla ko kuma idan ba auduga ba ce ta sanya sai ta wanke idan zai
yiwu.Sannan dole ne ta yi wanka yayin sallar zuhr da asr, sannan haka nan yayin
sallar magrib da isha..Sannan kada ta bata tazara tsakanin sallar azahar da
la'asar, haka nan tsakanin sallar magrib da isha, amma idan ta ba da tazara a
tsakaninsu dole ne ta sake yin wanka don gabtar da kowace salla.
Mas'ala ta 398:Idan kafin salla sai jinin istihala matsakaiciya ko
kuma mai yawa ya fito sannan kuma sai ya yanke,anan dole ne ta yi wanka ihtiyat
wajib kuma ta yi alwalla sannan ta yi salla,sai dai idan ta riga ta yi wankan
saboda yin wadannan sallolin,sannan kuma ya kasance lokacin da ta yi wankan
jinin ya riga ya yanke.
Mas'ala ta 399:yayin istihala matsakaiciya kamar yadda ak yi nayani a
sama dole net a yi wanka da alwalla akfin ta yi salla, anan duk wanda ta fara yi
babu matsala,duk da cewa idan da zata fara yin alwallar shi ne ya fi.
Mas'ala ta 400:Idan mace tana cikin istihsla kdan sai ya kasance bayan
sallar asuba sai ta koma matsakaiciya, anan dole ne ta yi wankan yayin sallar
zuhr da sr,haka nan idan bayan sallar zuhr asr ta zama matsakaiciya dole net a
yi wanka yayin sallar magrib da isha.Amma idan ta cigaba da matsayin
matsakaiciya har zuwa asuba, anan dole ne ta yi wanka sau biyu don yin sallar
asuba.
Mas'ala ta 401:Idan istihala kadan ko matsakaiciya bayan sallar asuba
ta koma mai yawa,anan dole ne mace ta yi wanka yayin sallar zuhr da asr,Sannan
ta yi sake wanka don yin sallar magrib da isha,Idan kuwa bayan sallar magrib da
siha ta koma mai ywa,sai ta yi wanka don yin sallar asuba, sai dai idan kafin
lokacin sallar ta koma kadan ko kuma ta yanke baki daya.
Mas'ala ta 402:Mace mai istihala dole ne yayin kowace salla ta yi
alwalla wato ta wajibi ce ko kuwa ta mustahabbi,Haka nan idan tana so ta sake
salla sakamkon ta yi salla ita kadai ne yanzu tana so ta yi tare da jama'a,ko
kuma tana so ta sake salla sakamkon wani dalili, anan shima done ta kiyaye
dukkan ayyukan mai istihala.Amma idan ya kasance zata yi sallar ihtiyat ne ko
kuma zata rama sujjada ko tashahhud, idan ya kasance bayan salla ne ba tare da
tazara ba, tana iya aiwatar da su ba tare da sake yin ayyukan mai istihala
ba.
Mas'ala ta 403: Idan jinin istihala ya yanke wa mace baki daya, idan
ya kasance istihala kadan ce, kawai sai ta tsarkake kanta ta yi alwalla don yin
salla,amma idan ta kasance matsakaiciya ce ko kuwa mai yawa, anan dole ne ta yi
wanka sannan ta yi alwalla kafin ta yi salla.Sannan tana yin wankan tun kafin
lokacin sallar ya yi koda tsakanin yana da yawa kawai lokacin sallar sai ta yi
alwalla.
Mas'ala ta 404:Idan mace bat a san wane nau'i ne na istihala ba take
yi,lokacin da take so ta yi salla dole net a sanya audugaa wajn al'aurarta tad
an dakata ta yadda idan fito da ita zat iya ganewa wace iri ce kadan ce ko
matsakaiciya ko mai yasawa,sannan sai ta aiwatar da ayyukan da suka yi dai-dai
da wadda take yi,Sannan idan ta san cea har lokacin salla istihalarta ba zata
canza ba, tana iya yin bincike akan hakan kuma ta yi ayyukan da suka dace da
hakan.
Mas'ala ta 405:Amma idan mace kafin ta yi bincike ta gano wane nau'i
ne na istihala take yi, sai ta cigab da salla, amma kafin ta yi sallar ta yi
ayyukan istihala kdan ne, idana bayan t agama sai ta yi bincike ta gano cewa
lallai kuwa kadan din ce anan sallarta ta inganta idan ta yi sallar ne tare da
niyyar kusanci zuwa ga Ubangiji. Amma idan bayan ta gama sai ta gano cewa
ayyukan da ta yi na kadan ne sannan kuma istihalarta mai yawa ce ko
matsakaiciya, ko kuma ba ta yi sallar bavne tare niyyar kusanci zuwa ga
Ubangiji, anan sallarta ta baci.
Mas'ala ta 406:Idan mace ba zata iya binciken halin da take cikiba ne
istihala,anan sai ta yi aiki da abin da take ganin cewa lallai shi ne ya hau
kanta, misali idan bat a sani ba shin istihalarta kadan ce ko kuwa matsakaiciya,
anan sai ta yi aiki da cewa kadan ce.Amma idan ta san wace ta gabata daga
cikisu, anan dole net a yi aiki da wadda take da tabbas a lokacin day a gbata
tana tare da ita,wato yanzu tana shakka akan cewa shin kadan ce ko matsakaiciya,
amma tana da tabbas a lokacin da ya gabata matsakaiciya ce, anan zata yi
aikinmatsakaiciya ne.
Mas'ala ta 407:Idan jinin istihala ya motsa daga wurinsa amma sai bai
fito waje ba,anan ba dole ba ne mace ta yi ayyukan mai istihala, Ammam idan ya
riga ya fito zuwa inda yake gudana koda bai fito wajen farji ba, dole ne ta yi
ayyukan da suka hau kan mai istihala.
Mas'ala ta 408:Idan mace mai istihala ta san cewa bayan ta yi alwalla
ko wanka jinni bai fito ba daga gareta, tana iya jinkirta sallarta kuma tana iya
yin salloli gaba ma da wannan wankan ko alwallar, idan har jinin bai fito ba.
Mas'ala ta 409:Maen da ke istihala idan ta san cewa kafin
lokacin salla ya fita jininta zai yanke,anan dole ne ta saurara har jinin ya
yanke ta yi wanka da alwalla sannan ta yi salla, ihtiyat wajib idan ma tana
tsammanin hakan dole ne ta saurara jinin ya yanke sannan ta yi wanka ta yi
salla.
Mas'ala ta 410: Mai istihala kadan bayan alwalla dole net a yi gaggawa
wajen yin salla haka nan mai matsakaiciya da mi yawa bayan wanka da alwalla dole
net a yi gaggawa wajen gabatar salla.Amma tsayawa don yin kiran salla ko yin
addu'a kafin salla babu matsala.Haka nan cikin sallar tana iya yin abubuwan
mustahabbai kamar kunut da makamantansa.
Mas'ala ta 411:Mai istihala idan ta ba da tazara tsakanin wanka da
salla dole ne ta sake yin wankan don aiwatar da salla,amma idan wannan tsakanin
jinin bai fito saman farji ba, ba sai ta sake wanka da alwallar ba.
Mas'ala ta 412:Dole ne mace mai istihala ta yi kokari ta hana jinin
fitowa bayan ta yi wanka da alwalla. Saboda haka idan ta takaita wajen tare
jinin ya fito bayan ta yi wanka da alwalla, dole ne ta sake yin sallar,sannan
ihtiyat wajib kafin ta sake sallar ta yi wanka da alwalla.
Mas'ala ta 413: idan jinin bai yanke ba lokacin wanka, wankan ya
inganta,amma idan lokacin wankan istihala matsakaiciya ta koma mai yawa anan
dole ne a sake wankan daga farko.
Mas'ala ta 414:Macen dake isthala, ihtiyat wajib ta hana jinin fitowa
a tsawon ranar da take yin azumi iya yadda take iyawa.
Mas'ala ta 415:Macen da take yin istihala azuminta yana inganta idan
ta aiwatar da wankan da yawajaba ta yi don yin sallolin rana,sannan kuma ihtiyat
wajib shi ne ta yi wankan sallar magrib da isha na daren da take so ta yi
azumin.
Mas'ala ta 416:Idanmace bayan sallar asr jinin istihala ya fito mata
koda ba ta yi wanka ba kafin faduwar rana, azuminta ya inganta.
Mas'la ta 417:Idan istihalar mace kafin salla daga kadan ta koma
matsakaiciya,dole ne ta gabatar da ayyukan matsakaiciya kafin ta yi sallar.Haka
nan idan matsakaiciya ta koma mai ywa dole ne ta gabatar da ayyukan mai yawa
kafin ta aiwatar da sallar, koda ta yi wankan matsakaiciya dole ne ta sake yin
wankan mai yawa.
Mas'ala ta 418:Idan mace tana cikin salla sai istihala matsakaiciya ta
koma mai yawa,anan dole ne ta yanke sallar ta yi wankan mai yawa sannan ta sake
sallar, idan kuma ba ta da lokacin yin wankan dolea yi taimama sannan ta yi
alwalla.Idan kuwa babu loakcin da zata iya yin alwallar sai ta kara yin
taimama guda, idan kuwa ba zai yiwu ba ta kara yin taimama guda ba,anan ba zat
katse sallar ba dole ne ta ida sallar sannan ta sake rama sallar.Haka nan idan
tana cikin sallar sai istihala kadan ta koma matsakaiciya ko mai yawa,amma idan
matsakaiciya ce da ai ta koma mai yawa bayan wanka dole ne ta yi alwalla sannan
ta yi sallar.
Mas'ala 419:Idan mace tana cikin sallar sai jinin istihala ya
yanke,sannan ba ta sani ba shin har cikin ciki jinin ya yanke ko
kuwa,anan dole ne ta yi wanka sannan ta sake sallar da ta riga ta gabatar.
Mas'la ta 420: Idan istihala mai yawa ta koma matsakaiciya, anan
wajen sallar farko sai ta yi ayyukan mai yawa, sauran salloli kuwa sai ta
gabatar da ayyukan matsakaiciya.Misali idan kafin sallar zuhr ta kasance mai
yawa sai ta koma matsakaiciya, anan sai tayi wanka da alwalla ta yi sallar zuhr
sannan ta yi sallar asr,magrib da isha da alwalla kawai ba sai ta sake wanka ba.
Mas'ala ta 421:Idan kafin salla sai istihala mai yawa ta yanke,sai
kuma ta sake dawowa,anan dole ne ,macen ta yi wanka don gabatar da kowace salla.
Mas'ala ta 422:Idan istihala mai yawa ta koma kadan, dole ne a yi
ayyukan mai yawa don yin sallar farko,sannan a yi ayyukan kadan ga sauran
sallolin baya.Haka nan idan istihala ta kaance matsakaiciya sai ta koma kadan,
dole a yi ayyukan matsakaiciya ga sallar farko sannan a gabatar da ayyukan kadan
ga sallolin baya.
Mas'ala ta 423:Idanmai istihala ba ta aiwatar da daya daga cikin
ayyukan da suka hau kanta ba koda kuwa canza auduga ne,sallarta ta baci.
Mas'ala ta 424:Idam mai istihala tana so ta aiwatar da wani aiki wanda
sharadi ne sai da alwalla, kamar tana so ta taba rubutun kur'ani, anan ihtiyat
wajib shi ne ta yi alwalla sannan,amma alwallar da ta yi don salla ba ta wadatar
ba.
Mas'ala ta 425:Babu matsala ga macen da take yin istihala ta aikata
wadan nan ayyukan: Zuwa masallacin ka'aba da na manzo. Haka nan tsayuwa a cikin
sauran masallatai da saduwa da miji duk babu matsala.Duk da cewa ihtiyat
mustahab shi ne ya zamana ta gabatar da wakan da ya wajaba akanta sannan ta iya
yin wadan nan ayyukan.
Mas'ala ta 426:Idan mai istihala mai yawa tana so ta taba kur'ani
kafin lokacin salla,anan dole ne ta yi wankan sannan ta taba kur'ani,amma mai
istihala matsakaiciya idan ta yi wanka wannan ranar alwalla ta wadatar idan tana
so ta taba kur'ani.
Mas'ala ta 427:Salar aya (idan rana yi ko kusufi ko wata ya yi
khusufi,girgizar kasa da dai sauransu) wajibi ce ga mai istihala, saboda haka
dole ne ta gabatar da yyukan da suka hau kanta wajen sallar yau da kullum don
yin sallar aya.
Mas'ala 428:Idan lokacin da mace take yin sallar yau da kullum sai
sallar aya ta wajaba akanta sannan tana so ta gabatar da sallar ayar bayan ta
gama sallar wajibi, anan dole ne ta gabatar da duk ayyukan da suka hau kanta don
yin sallar yau da kullum.Saboda haka ba za ta iya yin duka sallalin ba da wanka
da alwalla guda daya ba.
Mas'la ta 429:Haka idan mai istihala tana so ta gabatar da sallar
ramuwa dole ta gabatr da duk ayyuka da suka hau kanta don yin sallar wajibi.
Mas'ala ta 430:Idan mace ta san cewa jinin da ta fito daga gareta ba
na ciwo ba ne kuma ba na haihuwa ko haila ba ne, to anan sai ta yi aiki da
hukuncin da ayyukan istihala.Haka nan koda ta yi shakka akna cewa wanna jininmai
yiwuwa jinin wani abu daga cikin abubwan da muka fada, amma ba ya da alamominsu,
anan ihtiyat wajib shi ne ta yi aiki da hukuncin mai istihala.
|