Haila
Hila wani jinni ne da yake fita daga mahaifar mata mafi yawa karshen
kowa ne wata, idan mace ta ga wannan jinin ta zama mai haila kenan.
Mas'ala ta 431:Mafi yawan lokaci jinin haila yana da kauri kuma
launinsa ja ne yana karkata zuwa ga launin baki, sannan yana da zafi yayin
fitowarsa,Sannan yayin fitowarsa yana fitowa da karfi.
Mas'ala ta 432: Matan da suka hada jini da manzo sun agama jinin haila
bayan sun kai shekara 60,Sannan sauran matan da ba su ba bayan sun kai shekara
50.
Mas'ala ta 433:Jinin da yarinya take ganin kafin ta cika shekara tara
haka jinin da mace take gain bayan ta wuce shekarun haila, wannan jinin ba ya da
hukuncin haiala.
Mas'ala ta 434:Mace Mi ciki ko mai shayarwa tana iya yin haila.
Mas'ala ta 435:yarin da ba ta sani ba shin ta kai sheka tara ko
kuwa ba ta cika shekara tara ba, idan ta ga jini sannan ba shi da siffofin jinin
haiala, ba haila ba ce,kai koda ma yana da alamomin haiala ba za a ce masa
haiala ba.
Mas;ala ta 436:Macen da take shakka shin ta gama haila ko kuwa ba ta
gama ba,idan ta ga jini sannan ba ta sani ba shin haila ce ko kuwa, anan sai ta
yi hukunci da cewa haila ce.
Mas'ala ta 437:Mafi karancin haiala kwana uku,sannan mafi yawanta
kwana kwana goma,saboda haka idan jini bai kai kwana uku ba, to ba haiala ba ce.
Haka nan idan ya wuce kwana goma.
Mas'ala ta 438:Dole ne kwana ukun nan su zama a jere,saboda haka
idan da mace zata ga jini kwan biyu sai kuma ya yanke bayan kwana daya kuma sai
ya dawo, anan ba haila ba ce.
Mas'ala ta 439:Ba dole ba ne kwana uku a jere jinin ya zama yana
fitowa ba, idan jinin ya ya fito rana ta farko sai bai kara fitowa ba, amma yana
cikin farji wannan ya wadatar.Haka nan idan da jinin zai dan yanke na wani
lokaci sai ya dawo ta yadda za'a iya cewa cikin kwana ukun nan ta kasance cikin
jini, wannan shi ma ya wadatar ta zama mai haila.
Mas'ala ta 440:Ba doleba ne mace taga jini daren farko da daren kwana
hudu.amma dole ne ya zamana daren biyu da na uku ya kasance akwai
jinin.Saboda haka idan ya kasance tun daga fitowar ranar farko har zuwa har zuwa
faduwar rana ta uku, idan jinin bai yanke ba,ko kuma tsaakiyar rana ta farko ta
fara idan ya yanke a wannan lokacin rana ta hudu,sannan daren rana ta biyu da ta
uku jinin bai katse ba, duka wannan za a dauke shi matayin haila.
Mas'ala ta 441:Idan mace taga jinin tsawon kwana uku a jere ba sannan
ya yanke,sannan sai ta sake ganin jini bayan wasu kwanaki,sannan kwanakin ba su
wuce kwana goma ba,wadan nan kwanakin na takiya wadan da jinin ya yanke suma
za'a lissafa su cikin haiala.
Mas'ala ta 442:Idan mace ta ga jinin da ya wuce kwana uku amma bai kai
kwana goma ba,Sannan ba gane ba shin jinin haila ne ko kuwa na wani abu
daban,idan zata iya sanya auduga domin ta tabbatar,idan ta ga jinin daga
bangaren hagu yake to haila ce,amma idan daga bangaren dama yake ba haila ba ce.
Mas'ala ta 443:Idan mace ta ga jini sannan ya wuce kwana uku amma bai
kai kwan goma ba,sannan ba ta gane ba shin jinin haila ne ko kuwa wani ciwo,idan
kwankin da suka gabata ta kasance mai haila to anan sai ta dauka haila
ce,amma idan ta kasance mai tsarki sai ta dauka ba haila ba ce anan,Haka nan
idan ba ta sani ba shin da ta kasance mai haila ko uwa,anan sai ta kauracewa duk
abin da yake haramun ne ga mai haila,sannan ta aikata dukkan ayyukan da mace mai
tsarki take aikatawa.
Mas'ala ta 444:Idan mace ta ga jini amma tana shakka shin jinin haila
ne ko kuwa na haihuwa, idan ya kasance yana dukkan sharuddan jinin haila sai ta
dauke shi matsayin jinin haiala.
Mas'ala ta 445:Idanmace ta ga jini amma ba ta sani ba shin wannan
jinin na haila ne ko kuwa jinin gushewar budurci ne, anan sai ta bincika ta
hanyar ta sanya auduga a cikin farjinta ta dan saurara sannan ta fito da ita,
idan ya kasance gefen audugar ya baci da jini to wannan jinin ba na haila
ba ne na gushewar budurci ne.Amma idan ya bata dukkan audugar jinin haila ne.
Mas'ala ta 446:idan mace ta ga jinin da bai kai kwana uku ba sai ya
yanke, bayan kwan uku sai ta sake ganin jinin,sannan jinin ya cigaba har zuwa
kwana uku,anan jini na biyu na haila ne,amma jini na farko ba na haila ba ne.
|