Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Hukunce-hukuncen Haila

Mas'ala ta 447:Abubuwa sun haramta ga mai haila kamar haka:

Na daya:Ibadojin da dole ne sai da alwalla,kamar salla da dawafi da makamantansu.Amma sauran ibadojin dab a sai da alwalla ba, kamar sallar gawa babu laifi mai haila ta yi su.

Na biyu:Dukkan abubuwan da suke haram ga mai janaba.

Na uku:jima'i ta hanyar farji,haramn ne ga mace da na namijin,idan dai har hsjafa ta faku a cikin farji koda maniyyi bai fito ba,kai koda abin da bai kai hashafa ba ihtiyat wajib shi ne a kaice wa shigar da shi acikin farjin mai haila.Haka saduwa da mace ta hanyar dubura koda macen ta amince makaruhi ne mai tsanani.

Mas'ala ta 448:Jima' a ranakun da babu tabbas ga mace akancewa ranakun hailar ta ba ne amma shari'a ta nuna cewa ta dauki wadannan ranaku matsayin ranakun hailarta, annan ma jima'i haramun ne.Saboda haka macen da al'adarta ta wuce kwana goma dole ne ta yiaiki da hukunce- hukuncen da zamu fada anan gaba,wato ta sanya kwanakin da ya kamata ta sanya a cikin hailarta Saboda haka mijinta anan ba zai iya saduwa da ita ba a cikin wadannan kwanakin.

Mas'ala ta 449:Idan mutumya sadu da matrsa ga farjin alhali tana cikin haila,anan ihtiyat wajib dole ne ya bayar da kaffara,zamu fadi yawan kaffarar kamar haka:

Za a kasa kwanakin haila mace zuwa gida uku, idan mutum ya sadu da matsa a cikin kashi na farko  zai bayar 4.60g na zinari,idan kuwa cikn kashi na biyu ne sai baya da  2.30g na zinari idan kuwa cikin kashi na uku ne zai bayar da 1.15g na zinari  misali idan mace tana yin kwana shida,idan mjinta ya sadu da ita a cikin daren ko ranar farkoda ta biyu, wannan kashi nafrko kenan,ammaidan ya sadu da matarsa a cikin daren uku ko rana ta uku ko ta hudu,anan kashi na biyu kenan.amma idan ya sdu da matarsa a daren biyar ko ranar biyar da ta shida anan za'a lissafa shi a cikin kashi na uku kenan.

Mas'ala ta 450:Jima'i da mace maihaila ta dubura ba ya da kaffara.(amma makaruhi ne mai tsanani)

Mas'ala ta 451:Idan ya zamana kimar zinari ta canza tsakanin lkacin da mutum ya yi jmma'I da lokacin da biya kaffarar anan zai dauki kimar lokacin da zai bayar da kaffarar.

Mas'ala ta 452:Idan mutum ya sadu da matarsa tana haula. A cikin kashi na farko da bna biyu da na uku anan dole ne ya biya kaffarar duka gua uku.

Mas'ala ta 453:Idan mutum ya yi jima'i da matarsa tana haila sai biya kaffara sannan kuma sai ya sake yi  halin tana hailar,anan dole ne ya sake biyan kaffarar.

Mas'ala ta454:Idan mutum ya yi jima'i da mace tana ckin haila a lokutta da dama, anan dole ya biya kaffara guda a kowa ne jima'i da ya yi.

Mas'ala ta 455:Idan mutum yana cikin jima'I da mace sai ya fahimci cewa tana cikin haiala,anan dole ya rabu da ita cikin sauri idan kuwa ya jinkirta ihtiyat wajib   dole ne ya ya biya kaffara.

Mas'ala ta 456:Idan mutum ya yi zina da mace tana cikin haila ko kuma idan mutumya sadu da matar dab a ta shi ya dauka cewa matarsa ce alhali wannan matar tana cikin haila,anan ihtiyat wajib dole ne ya biya kaffara.

Mas'ala ta 457:Wanda ba zai iya biyan kaffara ba ya yi kokari ya ciyar da mabukacin da yake jin yunwa,idan kuma ba zai iya ba sai ya yi istigfari.

Mas'ala ta 458:Sakin mace tana cikin haila haramun ne,sannan kuma sakin bai inganta ba.

Mas'ala ta 459:Idan mace t ace tana yin haila kokuma ta ce t agama haila anan dole ne ya yarda da maganarta.

Mas'ala ta 460:Idan mace haila ta kama ta tana cikin salla.anan sallarta ta ba ci.

Mas'ala ta 461:Idan mace tana cikin salla sai ta yishakka akan cewa shin haila ta kamata ko kuwa? Anan ba zata kula da  shakkarta ba;anan kawai sai ta cigaba da sallarta amma idan sai da ta gama salla sai ta  kula cewa tana cikin salla haila ta kama ta, anan sallar da ta yi ta baci.

Mas'ala ta 462:Idan mace jininr hailarta ya yanke,anan dole net a gabatar da wanka don yi ibadojin da sai da alwalla ko taimama ake yinsu.sannan wanakan haiala kamar wankan janaba yake babu bambanci,sannan ana iya iya yin salla da shi ba sai an sake alwalla ba, kamar dai na janaba.Amma dai abin day a fi shi ne idan ya na so ya yi salla kafin ya yi wankan ko kuma bayan y agama ya kamata ya yi alwalla.

Mas'ala ta 463: idan mace ta samu tarki daga jinin haila, koda bat a yi wanka ba,idan mijinta ya sake ta sakin ya inganta,haka nan tun kafin mace ta yi wankan haila mijinta yana iya saduwa da ita madamar dai jinin ya yanke.sai dai ihtyat mustahab shi ne mutum ya kaurace wa sduwa da matarsa kafin ta yi wankan haila.Amma sauran abubuwan da suka haramta gareta lokacin da tana yin haila idan dai har  ba ta yi wanka ba su halarta a  gareta,kamar tsayuwa cikin masallaci da taba rubutun kur'ani.

Mas'ala ta 464:Idan mace tana da ruwan da kawai zai isa ta yi alwalla ne amma ba zai isa ta yi wanka ba,anan sai ta yi alwalla, sannan ta yi taimama maimakon wankan.Amma idan ba ta da ruwan da zata yi ko daya daga cikinsu ba, anan sai ta yi taimama guda biyu daya a matsayin wanka daya a matsayin alwalla.

Mas'ala ta 465:Ba sai mace ta rama sallolin da ba ta yi ba na yau da kullum a lokacin da take yin haila,amma zata rama azumin da ba ta yi ba.

Mas'ala ta 466:Idan lokacin salla ya isaa,sannan mace ta san cewa idan ta jinkirta haila zata zo mata,anan dole net a gaggauta ta yi sallar.

Mas'ala ta 467:Idan mace ta jinkirta yin salla, har haila ta zo mata,sannan lokacin da ya wuce tana iya yin abubuwan da suke wajibi a wajen salla,anan dole ne ta rama wannan sallar.Amma anan dole ne a kula da sauri da rashin saurin karatunta idan loakcin zai isa ta yi sallar dai-dai da yadda take yi kowa ne lokaci, anan shi ne zata rama.Misali mace da ba cikin tafiya take ba,Idan ta jinkirta ba ta yi slla, sannan lokacin da ya wuce zai isa ta yi salla raka'a hudu ta azahar, sannan kuma dai-dai da yadda take yi koda yaushe,anan shi ne zata rama sallar da ta wuce.Haka nan idan tana cikin tafiya ne ta yadda loakacin da ya wuce kafin haila ta zo mata zata uay yin salla raka'a biyu, anan shi ma zata rama sallal da ba ta yi ba.Sannan dole ne a kula da duk abi da ake bukata kafin a fara sallar kamar yn alwalla da sauransu.

Mas'ala ta 468: Idan mace ta gama haila a karshen lokacin salla,sannan lokacin da ya rage zai isa ta yi alwalla ta canza kaya da dai sauran abin da ake bukata,sanann loakacin da ya rage zai isa  a yi salla koda raka'a daya ce,anan dole ne ta yi wannan sallar idan kuma ba ta yi ba har lokacin ya wuce anan dole ne ta rama salla.

Mas'ala ta 469:Idan mace bayan ta gama haila lokacin da ya rage ba zai isa ta yi wanaka ba,amma  tana iya yin taimama,anan wannan sallar ba ta zama wajibi ba a kanta.Amma idan ya zama na bq saboda kurewar lokaci ba ne ba zata samu yin wankan ba, saboda uzuri ne ta yadda ba zata iya yin amfani da ruwa ba ne, anan idan ta bari lokacin salla ya wuce dole ne ta rama sallar.

Mas'ala ta 470:Idan mace bayan t agama haila sai take shakka akan cewa shin lkacin da take da shi ya isa ta yi salla ko kuwa ba zai isa ba, anan dole net a yi sallar.

Mas'ala ta 471:Idan mace tana tsammanin cewa lokacin da take da shi ba zai isa ba ta tanaji duk abin da take bukta don yin salla, sai ba ta yi sllar ba,amma bayan nan sai ta fahimci cewa lokacin zai isa ta yi sallar,anan dole ne ta ta rama salla.

Mas'ala ta 472:Mustahabbi ne mace a lokacin salla ta tsarkake jikinta daga jinin haila ta sake audugar,sannan idan ba za ta iya yi alwalla ba sai ta yi taimama ta zauna wurin da take yin salla ta kalli kibla ta cigaba da zikiri da salati:

Mas'ala ta 473:Makaruhi ne mace yayin da take cikin haila ta dauki kur'ani ko ta taba takardar kur'ani,haka makaruhi ne mace ta yi kunshi tana cikin haiala.