Rabe-Raben Mata masu Haila:
Mas'ala ta 474:Mata masu haila sun kasu zuwa gida shida:
Ta daya:Wadda take da lokaci tsayayye da kuma kwanaki tsayayyu,wannan
kuwa ana gane shi ne idan ta jera watanni biyu tana ganin jinni a lokaci guda
kuma kwanaki tsayayyu.Kamar misali ya kasance tana farawa daya ga wata zuwa
bakwai ga wata,idan ta maimaita wannan sau biyu ya zama al'adarta.
Ta biyu:Wadda take da tsayayyen lokaci kawai,amma kwanaki
mabambanta,Ita wannan tana gane haka ne ta hanayr maimaita hakan sau biyu,
misali kowane wata ta fara daya ga wata amma na farko ta yi kwana biyar na biyu
kuwa ta yi kwana bakwai.
Ta uku:wadda take da kwanaki tsayayyu, shima wannan ana gane shii ta
hanyar maimaita hakan sau biyu,wait ya zamana wata nafarko ta yi kwana shida na
biyu ma ta yi hakan. Ammaa lokutta mabambanta, misalai wannan watan ta fara daya
ga wata amma wata mai bi masa ta fara biyar ga wata.
Ta hudu:wadda take ba ta da tsayayyen lokaci haka nan ba ta da
tsayayyum kwanaki.wato tana iya faraway kowane llokaci sannan babu kwanaki
tsayayyu da zata gama.
Ta biyar:Macen da ta fara ganin jinin haila a lokacin na farko.
Ta shida:macen da take manta al'adarta,wato takan manta kwana nawa
take yi haka nan nawa ga wat take farawa,duktakan manta.Saboda wadan nan
rabe-raben da muka ambata zamu fadi hukuncin kowane anan gaba kadan.
Mai tsayayyen lokaci da kwanaki:
Mas'ala ta 475:matan da suke haka sun kasu kashi uku:
Ta daya:Matar da ta ga jinin haila sau biyu cikin lokaci tsayayye a kwanuka
tsayayyu.
Ta biyu:Matar da ta kasance jinin ba ya yankewa amma, amma jinin da
yake da alamomin haila yakan tsaya bayankwanaki tsayayyu. Misali wata biyu a
jere daga farkon wata zuwa bakwai jinin yana da almomin haila amma daga nana bin
ya yi gaba,ya kan canza kala, amma baya yanke wa, kamar yadda muka fada a baya
idan ya canza, daga nan zata dauka istihala ne.
Ta uku:Matar da taga jinni a wata biyu a jere a lokaci guda,amma
bayan kwana uku, sai jininta ya yanke, sannan sai ya sake dawowa, amma tsakanin
na farko da na biyu bai wuce kwana biyu ba,Idan ya zamana ta maimaita wannan sau
biyu,sannan ya zamana kwanakin da ta yi babu banbanci tsakanin na farko da na
biyu.Amma anan ba dole ba ne ya zamana kwanakin da ke tsakainin jini na
farko da na biyu su zama sun yi dai-dai, muhimmi anan shi ne ya zamana kwanakin
da ta kasance a cikin jinni yawansu ya kasance duk daya ne tsakanin wata na
farko da na biyu.misali ya kasance bayan kwana uku sai jini ya yanke sai bayan
kwana biyu sai ya sake dawowa,sannan ya dauki kwana uku sannan ya yanke baki
daya, haka nan wata na biyu shi ma kamar haka, wato ya zamana baki dayan
kwanakin kwana shida ne,duka wata biyun.
Mas'ala ta 476:Matar da take da la'ada ta lokaci da kwanaki, idan tag
a jinin a lokacin al'adarta ko kuma kwana biyu ko uku kafin lokacinta wato kafin
lokacinta ya yi kenan ko kuma wasu kwanaki bayan lokacin da ta saba yi, anan
koda jinin ba ya da alamomin jinin haila dole ne ta yi aiki da hukuncin mai
haila,haka nan idan bayan wasu kwanaki sai ta fahimci cewa ba jinin haila ba ne,
wato bai kai kwana uku ba sai ya katse,anan dole ne ta rama ibadar da ba ta yi
ba a cikin wadan nan kwanakin.
Mas'ala ta 477:Macen da take da al'ada ta lokaci da kwanaki,Idan tag a
jini kafin lokacinta ya yi sannan kuma ya cigaba har zuwa lokacin da ta saba yi
sannan ya wuce kwanakin da take yi, idan dai kwanakin duka bas u wuce kwana goma
ba, zata dauke su duka a matsayin haila.Amma idan kwanakin suka wuce kwana
goma,anan jinin da ta gani a kwanakinta na al'ada su kadai ne na
haiala,saurankuwa istihala ne,sannan dole net a rama ibadar da ba ta yi ba a
cikin kwanakin kafin hailer da bayan hailarta.
Mas'ala ta 478:Matar da take da al'ada lokaci da kwanaki, idan tag a
jini a cikin kwanakin hailarta da wsu kwanki kafin hailarta, sannan duka bas u
wuce kwana goma ba dukansu haila ce,amma idan sun wuce kwana goma,anan sai ta
dauki kwanakinta da kwanakin da ta fara ganin jinin kafin lokacin al'adarta idan
sun kai yawan kwanakin al'adarta sai ta dauke su matsayin al'adarta sauran kuma
da suka karu a sama sai ta dauke su a matsayin istihala.Amma idan duka ba su
wuce kwana goma ba sai ta dauke su duka a matsayin haila.
Mas'ala ta 479:matar da take da al'ada idan bayan kwana uku sai jinin
hailarta ya yanke,sai kuma ya sake dawowa,sannan tsakanin na farko da na biyu ba
su kai kwana goma ba,sannan duka kwankin da ta ga jini da wadan da jinin ya
yanke ba su fi kwana goma ba, anan yana da fuska guda hudu kamar haka:
1-Dukkan jinin da ta gani a lokaci na farko, ko kuma wani bangare daga ciki
ya shiga cikin kwanakin al'adarta,sannan jinin da ta gain bayan jini na farko ya
yanke bayankwankin al'adarta ya sake dawowa,anan sai ta dauki dukkan jini na
farko a matsayin na al'adarta,wanda kuma ya zo na biyun sai ta dauke shi a
matsayin istihala.
2-Jini na farko bai kasance a cikin kwanakin al'adarta ba,sannan dukan na
biyu ko kuma wani bangare daga ciki ya kasance cikin kwanakin al'adarta,anan
dole net a dauki dukkan jini na biyu a matsayin haila na farko kuwa a matsayin
istihala.
3-Wani bangare daga na farko da na biyu sun kasance cikin kwanakin
al'ada, sannan a cikin kwanaki na farko bas u gaza kwana uku ba daga cikin
kwanakin al'adarta, Sannan tsakanin yankewar jini na farko da na biyu bai kai
kwana goma ba,anan duka kwanakin na haila ne.Amma kwanakin dab a su kasance ba
cikin kwanakin al'ada a cikin kashui na farko, istihala ce,haka nan bangaren day
a fita daga cikinkwnakin al'ada a cikin jini na biyu.misali idan mace ta kan ga
jini daga uku ga wata,amma sai wani wata ta ga jini tun farkon wata zuwa shida
ga wata ta ga jini,sannan sai jini ya yanke tsawon kwana biyu,sannan sai ta
cigaba da ganin jini har zuwa sha biyar ga wata, anan daga uku ga wata zuwa goma
ga wata jinin haila ne,sannan daga goma zuwa sha biyar na istihala ne.
4-Wani bangare daga cikin na farko da na biyu sun kasance a cikin kwanakin
al'ada,amma kwanakin da suka kasance a cikin kwanakin al'ada daga cikin kashi na
biyu ba su kai kwana uku ba,anan tsakanin jini na farko da na biyu dole ne ta
bar duk abin da mai haila ba ta yi kamar yadda muka yi bayani a baya,Sannan
ayyukan ibada da suke wajibi sai ta yi aiki da hukuncin mai istihala kamar
yadda muka fada a baya.
Mas'ala ta 480:Matar da take da al'adar lokaci da kwanaki,Idan ba ta
ga jini ba a kwankin al'adarta,sai ta ga jini a wasu kwanki na daban, sannan
dai-dai da yawan kwanakin da take yi,idan ya kasance bayan kwanakin hailarta
ne,da ta ga jini kawai sai ta dauka hail ace, haka nan idan ta ga jinin kafin
kwanakinta sannan yana da alamomin haial, sai ta dauke shi haila,amma idan ba
shi da alamomin haila kuma bat a san cea ba shin zai kai kwana uku ko kuwa ba
zai kai ba,anan har zuwa kwana uku zata guji ayyukan da suka haramata ga mai
haila sannan dole ne ta aikata abubuwan suke wajibi, tare da yin amfani da
hukuncin mai istihala.
Mas'ala ta 481:Matar da take da al'adar lokaci dakwanaki, idan ta ga
jini a lokacin al'adarta, amma yawan kwanakin bas u kai yawan kwanakin al'adarta
ba, ko kuma sun fi yawan kwanakin al'adar,sannan bayan wannan jinin ya yanke sai
ta sake ganin wani jinin sannan yawansa ya yi dai-dai da yawan kwanakin
al'adarta,anan ihtiyat wajib shi ne ta yi aiki da hukuncin mai haila sannan ta
aikata abubuwan da suke wajibi a duka guda biyun.Sanan ta yi aiki da hukuncin
mai istihala a wanann tsawon lokacin.
Mas'ala ta 482:Matar da take da al'ada ta lokaci da kwanaki, idan ta
ga jini fiye da kwana goma,anan jinin da ta gani a cikin kwanakinal'adarta ko
dab a shi da alamomin haiala shi zata dauka hailarta,amma jinin da zata gani
bayan kwanakin al'adarta koda ya kasance yana da alamomin jinin haila jinin
istihala ne.Misali matar da take ganin jini haila daya ga wata zuwa bakwai ga
wata, sai ya kasnce tag a jinin fiye da kwana goma,anan daya zuwa bakwai kawai
zata dauka matsayin haila, bakwai zuwa goma kuma istihala, koda kuwa wasu daga
cikin daya zuwa na bakwai sun kasance ba su da alamomin haila,amma bayan bakwai
ga wata wasu daga ciki suna da alamomin haiala.Sai ta dauki wadan nan
matsayin istihala.
|