|
Mai tsayayyen lokaci
Mas'ala ta 483:Matan da suke da al'ada ta lokaci kawai sun kasu zuwa
gida uku:
Ta farko:Matar da ga jini a wani tsayayyen lokaci har sau biyu, sannan
bayan wani lokaci sai jinin ya yanke, amma kwanakin bas u yi dai- dai ba a
lokuttan guda biyu, misali duka watannin guda biyu ta ga jini ne a daya ga wata,
amma wata na farko kwana bakwai ya yi amma na biyun ya yi kwana shida ne,wannan
matar zata dauki farkon wata shi ne ranar ala'adarta.
Ta biyu:Matar dab a jini ba ya yanke mata,amma sai ta ga jini mai alamomin
haila a lokaci tsayayye har wata biyu a jere, misali jinin da yake da alamomin
haila ya kasance biyar ga wata yake farawa, sai ta ga haka har sau
biyu,Sannan duka watannin biyu yawan kwanakin sun bambanta da juna, anan wannan
,matar sai ta daki biyar ga wata shi ne al'adarta take farawa.
Ta uku:Matar da ta kasance har wata biyu a jere tana gani jini a lokaci
tsayayye,amma bayan kwana uku sai ya yanke, sannan sai ya sake dawowa bayan "yan
kwanaki,Idan dukkan kwanakin da tag a jini da kwanakin da suke a tsakiya wadan
da jinin ya yanek ba su fi kwana goma ba, dukkansu sai ta dauke a matsayin
haila.misali idan wannan ya kasance a daya ga wata har sau biyu, sai ta dauki
daya ga wata matsayin ranar fara al'adarta.
Mas'ala ta 484:Matar da take da tsayayyen lokaci idan tag a jinin
kafin lokacinta, misali kwana biyu ko uku kafin lokacin da ta saba gani, anan
koda ba shi alamomin haila sai ta bar duk abin da mai haila ya haramta gare ta
sannan idan bayan jinin ya yanke sai ta fahimci cewa ba jinin haila ba ne, wato
kamar idan ya kasance kafin kwana uku sai ya yanke, anan sai ta rama ibadar
wajibi da ba ta yi ba a wadan nan kwanakin.
Mas'ala ta 485:Matar da take da al'ada ta lokaci,Idan taga jini fiye
da kwana goma sannan bat a iya tantancewa ba shin hail ace ko ba haila
sabodarishin alamomin haila,anan sai ta tambayi wasu daga cikin danginta na uba
ko na uwa sai ta dauki kwanakin la'adarsu, suna da rai ne ko sun rasu,amma anan
zata iya sanya kwanakin haila dai-dai da kwanakin hailarsu idan ya kasance
kwanakin da suke yi sun yi dai-dai da juna,amma idan yawan kwanakinsu sun sabawa
juna, kamar idan ya kasance wasu daga ciki suna yin kwana biyar wasu kuma daga
cikinsu suna yin kwana bakwai,anan ba zata iya sanya kwanakinsu ba a matsayin
al'adarta,Sai idan wadan da al'darsu ta bambanta ba su da yawa wato wadanda suka
dace da juna suna da yawa kwarai fiye da wadancan,anan sai ta dauki al'adar
wadan da suka fi yawa ta sanya a matsayin al'adarta.
Mas'ala ta 486:Matar da take da tsayayyen lokacin haila,sannan ta
sanya kwanakin al'adar danginta a matsayin al'adarta,anan dole ne ta sanya ranar
farko da take ganin jinin haila kamar yadda ya kasance,kamar idan ya kasance
daya ga wata ne take faraway kuma tag a hakan har sau biyu,saboda haka anan daya
ga wata shi ne ranar fara al'adarta,saboda haka anan idan kwanakin da dauka daga
danginta kwana bakwai ne,anan koda ta ga jini fiye da kwana bakwai kwana bakwai
kawai zata dauka a matsayin al'adarta sauran kuma istihala ce.
Mas'ala ta 487:matar da take da al'adar tsayayyen lokaci, anan sai ta
sanya yawan kwanakin hailarta kamar yadda sauran danginta suke yi,amma
idan ba ta da dangi,ko kuma al'adarsu ta bambanta,anan ihtiyat wajib shi ne,
daga ranar farko zuwa bakwai sai ta dauke su a matsayin haila sauran kuwa
istihala ce.
|