Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Mace  marar tsayayyun kwanuka da lokaci

Mas'ala ta 490:Abin da ake nufi da irin wadan nan mata kuwa shi ne matan da zasu ga jinin haila sau da yawa amma sun kasa gane tsayayyen lokani da adadin kwanakin da suke yin al'ada, wato suna da lokaci da adadin kwanaki mabambanta.Irin wadan nan matan idan suka ga jini fiye da kwana goma sannan duka suna da  alamomin jinin haila,idan ya kasance sauran danginta suna yin kwana bakwai ne, to ita ma anan sai ta dauki kwana bakwai a matsayin kwanakin al'adarta sauran kuwa su kasance na istihala,idan kuwa ya kasance kwanakin da jinin yake da alamomin haila kwana biyar ne ba su kai kwana bakwai ba to sai ta  dauki wadan nan kwanaki da suka kasance suna da alamomin haila, sauran kuma kamar idan ya kasance danginta suna yin kwana bakwai ne, wadan nan kwana biyu da suka rage sai ta kiyaye ayyukan da suke haramun ga mai haila sannan ta yi ayyukan da suka wajabta tare da amfan da  hukuncin mai istihala. Amma idan al'adar danginta ya wuce kwanaki bakwai wato ya kasance kamar kwana tara ne,anan ma sai ta dauki kwana bakwai a matsayin al'adarta sauran kwana biyun kuwa dake tsakani, sai ta aikata ayyukan mai istihala sannan ayyukan da suka haramta ga mai haila ta kaurace masu.

Mas'ala ta 491:mace marar tsayayyen lokaci idan hailarta ta wuce kwana goma,sannan wasu daga cikin wadan nan kwanuka suna da alamomin haila wasu daga ciki kuma ba su da alamomin haila,sanna jinin da yake da alamomin haila bai gaza ma kwana uku ba, sannan bai wuce kwana goma ba, anan jinin da yake da alamar haila shi ne na haila wanda kuma yake da alamomin istihala sai ta dauke shi na istihala.Amma idan jinin da yake da alamomin haila bai kai kwana uku ba,anan sai ta  duba ta ga mene ne al'adar danginta idan ya kasance kwana bakwai ne, sai ta dauki kwana bakwai a matsayin hailarta sauran kuwa istihala ce,sai ta yi aiki da hukuncin mai istihala a cikin sauran kwanakin.Idan ya kasance kafin kwana goma tsakanin jini mai alamomin haila da kuma jinin da ya sake zuwa kuma shi ma yana da alamomin haila,misali ta ga jinin haila kwana biyar sai daga nan kuma sai ta cigaba da ganin jini wanda ba shi da alamomin haila har tsawon kwana tara, sai kuma jini mai alamomin haila ya sake zuwa, anan sai ta dauki na farko a matsayin haila sauran kuwa  sai ta yi aiki da hukuncin mai istihala.

yarinyar da ta  fara haila

Mas'ala ta 492:MAcen day a kasance loakci na farko net a fara ganin jinin haila, idan jinin ya wuce kwana goma,sannan kuma duka jinin yana da siffa guda daya anan sai ta dauki al'adar danginta sauran kuwa sai ta yi aiki da hukuncin mai  istihala.

Mas'ala ta 493:Idan wadda ta fara haila ta ga jini fiye da kwana goma sannan wasu daga cikin kwanakin suna alamomin haial wasu kuma ba su da su, sannan kwanaukan da suke da lamomin haila ba su gaza wa kwana uku ba, sannan ba su wuce kwana goma ba,anan kwanukan da suke da alamomin haila sune na hailarta wadan da kuwa ba  su da alamomin haila na istihala ne. Amma idan ya kasance kafin kwana goma su wuce tsakanin lokacin da ta ga mai  alamomin haial da wadan dab a su da na haila, sai kuma mai alamomin haila ya sake dawowa,kamar misali ta ga jini mai alamomin haila kwana biyar, sai wanda ba shi da lamomin haila ya yi kwanaki sai na haila ya sake dawowa, anan sai ta dauki kwana biyar na farko a matsayin na haila,sanan sai ta koma wajen danginta sai dauki yawan kwanakin da suke yi ta hada da wadan nan sauran kuwa na istihala ne.

Mas'ala ta 494:Idan yarinyar ta ga jini fiye da kwana goma,amma wasu daga cikin kwanakin suna da lamomin haial wasu kuma suna da alamomin istihala,sanan jinin da yake da alamomin haila sun gaza wa kwana uku ko kuma sun wuce kwana goma,anan ihtiyat sai ta dauki daga ranar farkon ranakun da suke da alamomin haila, dangane da adadin kwanakin kuwa sai ta koma zuwa ga danginta,sauran kuwa sai ta dauke a matsayin istihala.

Mace mai mantuwa

Mas'ala ta 495:matar da ta manta al'adarta, idan tag a jinni fiye da kwana goma anan sai ta dauki kwanakin da suke da alamomin haila har zuwa kwana goma a matsayin al'adarta,sauran kwanakin kuwa ta dauke su a matsayin istihala,amma idan bat a iya gane jinin da yake mai alamomin haila, anan ihtiyat wajib sai ta dauki kwana nakwai a matsayin hailarta sauran kuwa istihala ce.