Nifass:
Mas'ala ta 504:Daga lokacin jinjiri ya fara fitowa waje duk jinin da
zai fito daga uwa ana ce wa wannan jinin, jinin Nifass,idan wannan jinin kafin
kwana goma ko kuma lokacin da kwana goma ya cika sai ya yanke
dukkan wannan jinin ana ce masa jinin Nifass,Sannan macen da take cikin wannan
jinin ana ce mata mai nifass ko kuma mai biki.
Mas'ala ta 505:Jinin da mace zata gani kafin jinjiri ya fara
fitowa,wannan jinin ba a lissafa shi cikin jinin nifass.
Mas'ala ta 506:Ba dole ba ne kafin a ce mace tana cikin Nifass
ya zamana lokacin da ta ga jinin tare da yaro,ya zamana an gama halittar
yaron,koda ciki yana matsayin jini ne,ta yadda an tabbar da cewa wannan ciki ne
to za a lissafa shi cikin jinin nifass,matukar bai wuce kwana goma
ba.
Mas'ala ta 507:Yana iya yiwuwa jinin biki ko Nifass bai
wuce awa guda ba, wato baya da kadan, amma ba zai wuce kwana goma ba.
Mas'ala ta 508:Duk lokacin da mace ta yi shakka akan cewa shin wannan
jinin da ta gani bari ne ta yi, ta yadda idan da wannan jinin ya
tsaya akwai yuwar ya zama jinjiri,anan ba dole ne ba mace ta yi bincike,
saboda haka wannan jinin da ta gani ba jinin biki ne ba kuma
ba shi da hukuncin jinin biki.
Mas'ala ta 509:Tsayuwa a cikin masallaci ko shiga masallacin Haram ko
na manzo s.a.w.a. haka nan taba kur'ani da sauran ayyukan da suke haram ga mai
haila ita ma mai nifass sun haramta a gare ta.Haka nan duk abin da yake wajib,
mustahabbi da makaruhi ga mai haila, haka nan ita ma ga mai nifass hukuncin daya
ne.
Mas'ala ta 510:Sakin mace yayin da take cikin nifass, kamar hukuncin
lokacin da take cikin haila ne,wato sakin ba ya inganta,haka nan da
mijinta zai sadu da ita tana cikin jinin biki, hukun duk daya ne da matar da
take cikin haila,wato dole ne mijinta ya biya kaffara kamar yadda aka yi bayani
a cikin haila.
Mas'ala ta 511:lokacin da mace ta tsarkaka daga jinin nifass wato
lokacin da jinin ya yanke dole ne kafin ta gabatar da ayyukan ibada ta yi
wanakan nifass,yadda ake yin wanakan nifass kuwa kamar yadda ake yi wankan
janaba babu bambancin sai a cikin niyya.
Haka nan wannan wankan yana wadatuwa daga yin alwalla, wato ba sai mace ta yi
alwalla ba ta yi aikin ibada.Idan mace ta ga jini bayan jinin farko ya yanke,
idan dai tsakanin jinin na biyun da ranar haihuwa bai kai kwana goma ba,
to jini na biyun da nafarko duka nifass ne,Saboda haka idan da ta yi azumi
cikin kwanakin da jinin ya yanke dole ne ta rama azumin da ta yi.
Mas'ala ta 512:Idan mace ta yi shakka akan cewa shin jinin bikinta ya
yanke ko kuwa da saura a ciki, anan sai ta sanya auduga a cikin farjinta ta dan
saurara zuwa wani dan lokaci sannan ta fito da ita, idan ba ta ga jini ba to
anan sai ta yi wanka domin ta cigaba da ayyukanta na ibada.
Mas'ala ta 513:Macen da take da kwanaki na al'ada, idan kwanakin jinin
nifass suka wuce kwana goma, anan sai kawai ta dauki yawan kwanakin da take yi
yayin al'adarta sauran kwankin kawai sai ta dauke su a matsayin jinin istihala,
ta yi wanka ta cigaba da ayyukan ibadarta,Saboda haka idan jinin biki ya wuce
kwana goma sai ta koma ta dauki yawan kwanakin da take yin haila, idan ya
kasance kamar kwana shida take yi, kwankin da suka hau sama kenan sai ta rama
sallolin da ba ta yi ba, sannan ta kauracewa abubuwan da suke haram ko makaruhi
ga mai jinin biki,amma idan jinin bai wuce kwana goma ba, sai ta dauke shi
duka na nifass ne.Duk da yake abin da ya fi anan shi ne, daga kwana goma bayan
haihuwa har zuwa kwana na sha takwas mace zata yi aiki ne kamar yadda mai
istihla take yi idan jini bai yanke ba.Sannan ta bar sauran ayyukan da
suke haram ga mai nifass.
Mas'ala ta 514:Tsakanin jinin nifass da na haila dole ne ya zama mafi
karanci kwana goma.Saboda haka jinin da mace zata gani bayan nifass matukar bai
kai kwana goma ba tsakani, to wannan jinin na istihala ne, koda kuwa wannan
jinin ya kasance a cikin kwanakin da take yin al'ada.
|