Wankan taba gawa
Mas'ala ta 515:Idan mutum ya taba gawa bayan jikin mamacin ya yi sanyi
sanna kuma ba a kaiga yi wa gawar wanka ba, anan dole ne mutum ya yi
wankan taba gawa,anan kuwa ya kasance mautum cikin zabinsa ne ya taba gawar ko
ba cikin zabinsa ba, wato koda mutum yana barci ya taba gawa dole ne ya yi
wannan wanka.Sannan koda kuwa farcen mamacin ne mutum ya taba,amma
idan mutum ya taba gawar dabba ba dole ba ne ya yi wanka.
Mas'ala ta 516:Amma idanmtum ya taba gawa kafin jikinta ya yisanyi ba
dole ba ne ya yi wanka koda kuwa mutum ya taba bangaren kai ne inda ya riga ya
yi sanyi.
Mas'ala ta 517:Idan gashin mutum ya taba jikin gawa ko kuma gashin
gawa ya taba jikin mutum,anan wanka ba ya wajaba ga mutum,sai dai idan ya
kasance gashin mutum bay a da tsawo ta yadda za'a iya cewa ya taba jikin
mamacin.
Mas'ala ta 518:Idan mutum ya taba gawar yaro koda kuwa jinjirin da aka
yi barinsa ne , wato wanda ya kai wata hudu,wanka ya wajaba,koda wanda bai kai
wata hudu ba abin da ya a fi shi ne mutum ya yi wankan.Saboda haka idan
mace ta barar da cikin day a kai wata hudu dole ne ta yi wankan taba gawa,koda
wanda ma bai kai wata hudu ba abin da ya fi shi ne ta yi wankan.
Mas'ala ta 519:Yaron da aka fito daga cikin cikin mahaifiyarsa bayan
ta mutu, bayan ya balaga dole ne ya yi wankan taba gawa.
Mas'ala ta 520:Idan mtum ya taba gawa bayan an gama wankan gawa sau
uku kamar yadda zamu yi bayanin yadda ake yinsa anan gaba kadan, anan wankan
taba gawa ba ya wajaba ga mutum,amma idan kafin a yi wankan na uku mutum ya taba
gawar,anan dole ne mutum ya yi wankan taba gawa.
Mas'ala ta 521:Idan karamin yaro ko mahaukaci ya taba gawa,idan yaron
ya balaga ko kuma mahaukacin ya samu hankali dole ne ya yi wankan taba gawa.Idan
yaron koda bai balaga ba amma yana da wayo yana gane abubuwa,anan idan ya taba
gawa wankan taba gawa ya wajaba a gare shi a wannan lokacin sannaa kuma wankansa
ya inganta.
Mas'ala ta 522:Idan jikin mutum mai rai ko matacce amma ba kai ga yi
masa wanka ba, sai aka cirri wani bangaren jikinsa inda yake da kashi,idan mutum
ya taba wannan bangaren jikin da aka cira daga jikinsa, wankan taba gawa ya
wajaba a gare shi.Amma idan wannan bangaren ba shi da kashi wanka ba ya wajaba.
MAs'ala ta 523:Idan mtum ya taba kashi ko hakorin mamacin dab a a yi wa wanka
ba,ihtiyat wajib shi ne mutum ya yi wankan taba gawa.Haka nan idan mutum ya taba
kashin da aka cira daga mutum mai rai amma babu nama a bisa kashin, dole ne
mutum ya yi wankan taba gawa,amma idan mutum ya taba hakorin da aka cire daga
mutum mai rai, ba wajibi ba ne mutum ya yi wanka taba gawa.
Mas'ala ta 524:Ana yin wankan taba gawa kamar yadda ake yin wankan
janaba, sannan yana wadatarwa daga yin alwalla,wato mutum yana iya yin salla ba
sai ya yi alwalla ba bayan ya yi wankan taba gawa.
Mas'ala ta 525:Idan da mutum zai taba gawa da yawa ko kuma mutum ya
taba gawa sau da yawa,idan ya yi wanka daya ya wadatar.
Mas'ala ta 526:Wanda ya taba gawa idan bai yi wankan ba, ya
halatta ya tsaya a cikin masallaci,haka nan ya halatta ya yi jima'i
ko ya karanta daya daga cikin suroirn da suke da sujada ta wajibi.Amma dole ne
ya yi wanka idan yana so ya yi salla,sannan abin da ya fi shi ne ya yi alwalla
bayan ya yi wankan.
|