Hukuncin wanda ke gargarar mutuwa
Mas'ala ta 527:Musulmin da yake kana garagarar mutuwa,namiji ne ko
mace,babba ne ko yaro,dole ne a kwantar da shi a rigingine kafafunsa su kalli
alkibla ta yadda idan da za a tayar da shi zaune zai kalli alkibla,anan
yana iya yiwuwa fa wannan aikin ya zama dole ga shi marar lafiyar idan har yana
iya yin hakan da kansa.
Mas'ala ta 528:Ihtiyat wajib shi ne kafin a gama yiwa mamaci wanka ya
kaance yana cikin wannan hali, wato yana kallo sama kafafuansa na duban
alkibla,amma idan aka gama yi masa wanka abin da ya fi shi ne a kwantar da shi
kamar yadda ake kwanatar da shi yayin da za a yi masa salla.
Mas'ala ta 529:Kwantantar da musulmin da yake kan gargarar mutuwa
kamar yadda muka fata a baya, wajibi ne ga dukkan musulmi ba ya bukatar neman
izini daga waliyyinsa.
Mas'ala ta 530:mustahabbi ne a lakanta wa wanda ke cikin gargarrar
mutuwa kalmar shahada da A'imma guda sha biyu da sauran akidojin musulci,wato a
rika ambartar su ta yadda zai farga shi ma ya rika ambata,sannan mustahabbi ne
ya cigaba da mai-maita su har zuwa lokacin da zai cika.
Mas'ala ta 531:sannan mustahabbi ne a lakanta wa wanda ke cikin halin
garagarar mutuwa wanna addu'ar:
«اللّهمَّ اغْفِرْلِىَ الْكَثيرَ مِنْ
مَعاصيكَ وَاَقْبَلْ مِنِّى الْيَسِيرَ مِنْ طاعَتِكَ يا مَنْ يَقْبَلُ الْيَسِيرَ
وَيَعْفوُ عَنِ الْكَثِيرِ اِقْبَلْ مِنّى الْيَسِير; واعْفُ عَنّى الْكثيرَ
اِنَّكَ اَنْتَ الْعَفُوُّ الْغَفُورُ اللّهُمَّ ارْحَمْنىِ فَاِنَّكَ رَحيمٌ».
.Mas'ala ta 532: musta habbi ne, a canza wa wanda ke cikin
halin barin duniya wurin da yake kwance idan yana cikin jin jiki,wato a kai shi
wurin day a saba yin salla idan ba zai zama wahalarwa ba gare shi.
Mas'ala ta 533: mustahabbi ne a karanta wa wanda ke cikin halin mutuwa
wadan nan surorin:yasin,safaat,Ahzab,aytul kursiy da wannan ayar ta cikin
suratul A'araaf aya ta 54..
اِنَّ رَبَّكُمُ اللهُ الَّذى خَلَقَ
السَّماواتِ................................................................................
sannan da ayoyin uku na karshen Bakara da dai duk abin da ya sawaka daga
kur'ani mai girma.
Mas'ala ta 534:Barin wanda ke cikin hali gargara shi kadai
acikin daki ko a aza wani abu a bisa cikinsa makaruhi ne,haka nan kasancewar
wani mai janaba ko mai haila a inda yake makaruhi ne, haka nan barin mata su
kadai a wurinsa da magana da yawa ko kuka makaruhi ne.
|