Hukunce-hukunce bayan mutuwa
Mas'ala ta 535:Mustahabbi ne mutum bayan ya mutu a rufe bakinsa da
idanunsa,sannan mike hannayensa a rufe shi da wani mayafi,haka nan idan mtum ya
mutu da daddare sai a kunna fitila a inda yake,sannan a fada wa sauran muminai
don su halarci jana'izarsa,haka nan mustahabbi ne a gaggauta wajen rufesa,amma
idan ba a da tabbas a kan mutuwarsa wato ana tsammanin cewa ko bai mutu ba,anan
ya wajaba a dakata don a samu tabbas akan hakan,haka nan idan mamacin ya kasance
mace ce kuma ta mutu da ciki,sannan kuma jinjirin yana da rai,anan sai fasa
cikin a fito da jinjirin, sannan a maida cikin a dinke.
Mas'ala ta 536:Yiwa mamaci salla,wanka, da rufe shi wajibi ne ga
dukkan musulmi koda ba dan shi'a imamiyya ne ba.Amma idan wasu daga cikin
musulmi suka aiwatar sun dauke wa sauran,amma idan da za a ce ba wanda ya aikata
dukan musulmi sun aikata zunubi.
Mas'ala ta 537:Idan wani daga cikin musulmi ya cigaba da aikata
ayyukan da suka wajaba a yi wa mamaci, ya dauke wa sauran al'umma, amma idan da
zai yi wani bangare daga cikin sai ya bari, to anan ya hau kan sauran al'umma su
ida abin da ya ragu.
Mas'ala ta 538:Idan mutum ya samu tabbas akan cewa lallai wasu sun
cigaba da aiwatar da ayyukan jana'iza anan ba dole ba ne a kansa ya je ya yi
wannan aikin wadancan sun sauke masa.Amma idan ba shi da tabbas akan haka anan
dole ne ya je ya aiwatar da wannan aikin.
Mas'ala ta 539:Idan wani ya samu yakini a kan cewa ayyukan da aka
aiwatar na abin da ya shafi mamaci, ba su inganta ba,anan ya wajaba a kansa ya
aiwatar da wadannan abubuwan da aka yi ba dai-dai ba.Amma idan ba shi da
tabbas akan bacinsu ko yana shakka ne akan hakan anan bai wajaba akansa ya sake
yin wadannan ayyuka ba har sai idan yana da yakini akan cewa ba su inganta ba.
Mas'ala ta 540:Dole ne a nemi izini daga waliyyin mamaci don aiwatar
da wanka,likkafani da bisne mamaci ko yi masa salla.
Mas'ala ta 541:Waliyyin mace a wajen yi mata abubuwan da suka wajaba
ga musulmi su yi wa mamaci wato wanda za,a nemi izininsa shi ne, mijinta, daga
nan kuwa sai wadan da suke cin gadonta daga cikin maza, sannan wadan da
suke bin bayansu kuwa su ne sauran mata masu cin gadonta.Saboda haka duk wanda
yake gaba a wajen cin gadonta a wajen neman izini akan abin da ya shafi
yi mata wasu ayyuka shi ne a kan gaba.
Mas'ala ta 542:Idan wani mutum ya ce ni ne wanda wannan mamaci ya yi
wa wasiyya ko y ace ni ne waliyyinsa ko wanda ya ce ya iwatar da wadannan ayyuka
bayan ya mutu, sannan wani bai yi jayayya ba akan haka wato wani bai ce shi ma
ya ce ya aikata wadan nan ayyuka ba,anan sai a bar wa wannan mutum ya aiwatar da
wadan nan ayyuka.
Mas'ala ta 543:Idan mamaci ya yi umurni da cewa wani daga cikin mutane
wanda ba waliyyinsa ba idan ya mutu ya aiwatarsa masa da wadan nan ayyuka,anan
ihtiyat wajib shi ne duka su biyun wato waliyyi da wannan mutumin su ba da
izini, wato sai an nemi izini daga garesu su biyun baki daya.Idan mamaci ya yi
wasiyya akan wadannan ayyukan akan 'ya'yansa anan dole ne wadannan 'ya'yan nasa
su yi aiki da abin da mahaifinsu ya yi musu wasiyya da shi, ba zasu iya kin
amsar wannan wasiyyar ba.Amma idan mamaci ya yi wasiyya ga wani wanda ba dansa
ba akan ya aiwatar da wadan nan ayyuka gare shi bayan ya mutu,anan wanda aka yi
wasiyyar idan har ya sani kafin mutumin ya mutu kuma zai iya zuwa ya gaya masa
cewa ba zai iya ba, anan yana iya ce masa ba zai iya aiwatar da wadan nan ayyuka
da ya nema daga garesa ba. Amma idan mamacin a lokacin ba zai iya canza wani
wasiyyi ba anan dole mutumin da aka yi wasiyyar da shiaya yi aiki da abin da aka
yi masa wasiyya da shi.
|