Hukuncin wankan mamaci
Mas'ala ta 544:Wajibi ne ayi wa mamaci wanka uku:
Na daya:Da ruwan da aka gauraya da magarya
Na biyu:da ruwan da aka gauraya da Kafur.
Na uku: Da ruwa zalla wan da ba shi da gauraye.
Mas'ala ta 545:Magarya da kafur din da za a gauraya da ruwa kada su
kasance masu yawa ta yadda ba za iya cewa wannan ruwa ne ba, sannan kuma kada su
yi kadan ta yadda ba za a iya gane an gauraya ruwan da su ba.
Mas'ala ta 546:Idan ba a samu magarya ko kafur wanda zasu isa ba,anan
ana iya amfani da wanda aka samu,amma kada ya zamana sam ba za iya gane
cewa an gauraya ruwan da su ba.
Mas'ala ta 547:Idan mutum bayan ya yi haramin aikin hajji kuma kafin
ya ida sa'ayi tsakanin safa da marwa sai ya mutu, anan bai halitta ba a yi masa
wanka da kafur,anan maimakon kafur sai ayi masa da ruwa marar gauraye.Haka nan
idan mutum ya mutu ya na cikin haramin Umura kafin ya yi aski.
Mas'ala ta 548:Idan ba a samu kafur ko magarya ba,ko kuma akwai amma
ba zai yiwu a yi amfani da su ba, kamar a ce na kwace ne,anan a maimakon kowa ne
sai ayi amfani da ruwa zalla.
Mas'ala ta 549: Wanda zai yi wa mamaci wanka dole ne ya kasance dan
shi'a imamiyya,sannan mai hankali ihtiyat kuma ya zama baligi kuma ya san
hukuncin wankan gawa.
Mas'ala ta 550:Mutumimn da zai yi wankan gawa dole ne ya yi niyyar
kusanci ga Ubangiji, wato zai yi wannan wanka ne domin aikata umurnin Allah T.A.
Sboda haka idan mutum ya cigaba da wannan kudiri har zuwa karshen wanka na uku
ba sai ya sake wata niyyar ba a farkon kowa ne wanka.
Mas'ala ta 551:Yiwa Yaro musulmi wanka ko dan zina ne ya wajaba ga
sauran musulmi.Amma bay a halitta yi wa kafiri wanka da sauran duk abin da ya
shfi ayyukan mamaci haka nan dan kafiri . Wanda ya kasance tun yana
yaro mahaukaci ne sannan har ya balaga bai samu hankali ba, idan har daya daga
cikin iyayensa ko kakanninsa musulmi ne, idan ya mutu ya wajaba ayi masa duk
abin da ake yi wa sauran musulmi.Amma idan wani daga cikin iyayensa ko
kakanninsa ba su kasance mulmi ba, anan bai halita a yi masa wanka ko wani
abu da ake wa mamaci ba.
Mas'la ta 552:Jinjirin da aka yi barinsa idan har ya kai wata hudu ya
wajaba a yi masa wanka.Amma idan bai kai wata hudu ba, sai a lullube shi
cikin wani kyalle a rufe shi.
Mas'ala ta 553:Idan namiji ya yi wa mace wanka ko mace ta
yi wa namiji wanka, Wankan ya baci,amma miji ko mata suna iya yiwa daya daga
cikinsu wanka kuma wankan ya inganta amma, Ihtiyat mustahab shi ne mata
kada ta yi wa mijinta, miji kada ya yi wa matarsa wanka.
Mas'ala ta 554:Namiji yana iya yi wa yarinyar da ba ta wuce shekara
uku wanka ba,haka nan mace ma tana iya yi wa yaron da bai fi shekara uku wanka
ba.
Mas'ala ta 555:Idan ba a samu namijin da zai yi wa namiji wanka ba,
matan da suke maharramansa kamar uwa ko kaka ko kuma wadan da suka zama
maharramansa ta hanyar shayarwa suna iya yi masa wanka amma a karkashin
mayafi, wato kada su kware jikinsa, sai dai kawai su su yi masa wanka yana rufe
su sanya hannusu a ksarkashin mayafin.Haka nan idan mace ta rasu, kuma ba a samu
wata mata ba wadda zata yi mata wanka, anan ana iya samun wani daga cikin
maharramanta ya yi mata wanka kamar yadda muka yi bayani a sama.
Mas'ala ta 556:Idan wanda yake wa mamaci wanka da wanda yake taimaka
masa dukkansu maza ne kuma mamacin namiji ne,dole ne jikin mamacin ya kasance a
bude, sai dai kawai al'aurarsa dole ne a rufe ta.
Mas'ala ta 557:Kallon al'aurar mamaci haramun ne,Saboda haka wanda
yake yi masa wanka idan ya kalli al'aurarsa ya aikata haram amma wankan
bai baci ba.
Mas'ala ta 558:Idan wani wuri daga cikin jikin mamaci ya kasance yana
da najasa dole ne kafin a wanke wajen a tsabbatace shi sannan a wanke
wurin.ihtiyat mustahab shi ne a tsarkake dukkan jikin mamaci kafin a fara yi
masa wanka.
MAs'ala ta 559:Wankan mamaci kamar wankan janaba yake,saboda haka idan
har yana yiwuwa a yi wa mamaci wanka Tartibi to lallai ayi masa hakan, amma na
iya tsoma kowa ne bangarre daga cikin bangarorin wanka guda uku a cikin ruwa mai
yawa babu wata matsala.
Mas'ala ta 560:Wanda ya mutu yana cikin janaba ko haila, ba dole ba ne
a yi masa wankan janaba kom haila, wankan mutuwa duk ya wadatar da wannan.
Mas'la ta 561:Bai halita ba mutum ya amshi lada don ya yi wa mamaci
wanka,amma amsar lada don aiwatar da wasu ayyuka wadan da suka shafi gabatarwa
ne ga wankan kamar debo ruwa da makamantansu, wannan babu laifi akan hakan.
Mas'ala ta 562:Idan ba a samu ruwan da za a yi wa mamaci wanka ba ko
kuma amfani da ruwan zai iya cutarwa, anan ana iya yi masa taimama mai-maikon
wankan.sannan za a yi masa taimamar ne kamar yadda ake yin wankan, wato sau uku,
kuma ta farko da niyyar ruwa mai gauraye da magarya, ta biyu kuwa da ruwa mai
kafur, haka nan ta uku da niyyar maimaikon ruwa wanda ba shi da gauraye.
Mas'la ta 563:mutumin da zai yi wa mamaci taimama, dole ne ya buga
hannayensa a bisa kasa, sannan ya shafi fuska da bayan hannayen mamacin kamar
dai yadda ake yin taimama.Sannan idan zai yiwu a yi taimamar da hannayen
mamacin zai fi. Idan hakan ba zai yiwu ba shi ke nan .
|