Hukuncin likkafani
Mas'ala ta 564:Idan musulmi ya rasu wajibi ne a yi masa
likkafani,wannan likkafani kuwa yana da bangarori guda uku,gyafto riga da
mayafi.
Mas'alata 565:Gyafton kuwa dole ne ya kama daga cibiya zuwa
kwauri,haka nan riga zata kama daga kafadu zuwa kwauri,amma mayafi kuwa zai kama
tun daga saman kai har zuwa abin da ya rufe kafafu, sannan dole ne ya kasance
mai fadi ta yadda za linka shi a daure.
Mas'ala ta 566:Idan ya kasance magadan mamaci baligai ne kuma sun
amince a yi masa likkafani fiye da wanda muka fada na wajibi, anan ba matsala
ana iya amfani da dukiyarsa don yi masa likkafani na mustahabbi wato fiye da
wanda muka fada a sama.Amma ihtiyat wajib shi ne kada a yi amfani da kason wanda
ba baligi ba daga cikin magadan.
Mas'ala ta 567:Idan mamaci ya yi wasiyya ayi amfani da dukiyarsa don
yi masa likafani fiye da na wajibi, sannan abin da ya yi wasiyyar ya kai daya
bisa uku na dukiyar da ya bari, anan babu wani abu ana iya mafani da abin da ya
yi wasiyyar da shi.
Mas'ala ta 568:likkafanin mata yana akan mijinta, hakan idan mutumn ya
sakimatarsa sai ta mutu kafin ta cika idda, sannan kuma sakin wanda zai iya
maido ta ne wato ba saki uku ba ne da makamantansa,anan likkafaninta yana a
kansa.haka nan idan mijin ya kasance yaro ne wanda bai balaga ba, ko kuma ba shi
da hankali, anan likkfanin ya hau kan wanda yake waliyyinsa.
Mas'ala ta 569:Yin likkafani bai zama wajibi ba ga dangin mamaci, koda
kuwa sun kasance suke daukar nauyinsa kafin ya rasu.
Mas'ala ta 570:Ihtiyat wajib shi ne kada yadin da za a yi wa mutum
likkafani ya zamana ba ya da kauri ta yadda za a iya ganin jikinsa.
Mas'ala ta 571:Dole ne likkafani ya kasance na halas,ko da dukiyar
wanda ya amince a yi masa likkafanin.
Mas'ala ta 572:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da abin da yake
na haram.Don haka Idan a ka yi wa mutum likkafani da abin da ba na halas ba,
dole ne a tono shi domin a canza masa wannan likkafanin.
Mas'ala ta 573:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da fatar dabba
mushe,amma idan ba a samu wani abin da za a yi masa likkafani ba ana iya yi masa
da wannan din ba matsala.
Mas'ala ta 574:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da abin da yake
najasa,hakan nan bai halitta ba ayi wa mutum likkafani da abin da yadin da aka
saka da alhariri ko aka hada da zinari,amma idan ya zamana ba yadda za a yi
babu matsala.
Mas'ala ta 575:Bai halitta ba a yi wa mutum likkafani da yadin da aka
saka daga gashin dabbar da namanta haramun ne a ci sa, amma ida aka jeme fatar
dabbar da ake ci ana iya yin likfani da ita babu matsala,haka nan idan aka saka
yadi da gashin dabbar da ake ci ana iya yi wa mutum likkafani da ita babu
matsala,duk da cewa ihtiyat mustahab shi ne a kaurace wa hakan.
Mas'ala ta 576:Idan likkafani ya samu najasa daga mamacin ko kuma daga
waninsa,idan zai yiwu a wanke najasar to sai a wanke ta,amma idan ba zai yiwu a
wanke ba sai a yanke wurin da yake da najasar,haka nan idan an riga an saka shi
cikin kabari,ya zamana fito dashi daga kabari don a wanke najasar zai zama kamar
rishin girmamawa a gareshi, to ihtiyat wajib shi ne a yanke wurin da yake da
najasar.Amma idan zai yiwu a fito da shi kuma babu wata matsala don sake wani
likkafanin to hakan ya fi.
Mas'ala ta 577:Idan mutum ya mutu yana cikin haramin hajji ko umara
shima kamar sauran mutane za a yi masa likkafani babu matsala don an rufe
fuskarsa da kansa.
Mas'ala ta 578:Mustahabbi ne mutum ya tanaji kafur da magarya
wadan da za sanya wajen yi masa wanka tun yana da lafiya.
|