Hukuncin shafa kafur(hunut)
Mas'ala ta 579:Bayan
an yi wa mamaci wanka wajibi ne a shafa wa mamacin Kafur a goshinsa,tafukan
hannayensa,guyawun kafa da kan manyan yatsun kafa wato wuraren da ya wajab su
taba kasa yayin sujjada.Sannan mustahabbi ne a shafa kafur din a kan hanci,
kamar yadda yake mustahhabi ne hanci ya taba kasa yayin sujjada,sannan dole ne
kafur din ya zama sabo,sabida haka idan ya kasance sakamakon daewarsa kamshinsa
ya fita idan aka yi mafani da shi bai wadatr ba.
Mas'ala ta 580:A
wajen shafa wa mamaci kafur ba dole ba ne a bi jeri wajen gabban sujjadar,duk da
yake mustahabbi ne a fara shafa wa goshi.
Mas'ala ta 581:Abin da ya fi shi ne a shafa wa mamaci kafur kafin a sanya masa
likkafani,duk da yake idan aka shafa masa bayan an yi masa likkafani ma babu
matsala.
Mas'ala ta 582:Idan
mutum ya mutu yayin aiki hajji kuma kafin ya yi sa'ayi tsakani safa da marawa,
bai halitta ba a sanya masa kafur,Haka nan idan mutum yana cikin aikin umara ya
mutu kafin ya yi aski, shi ma bai halitta ba a shafa masa kafur.
Mas'ala ta 583:Matar
a mijinta ya mutu kuma ba ta kaiga cika idda ba,duk da cewa bai halitta ba ta yi
amfani da turare amma idan ta mutu wajibi ne a shafa mata kafur.
Mas'ala ta 584:
Ihtiyat wajib Bai halitta ba a shfa wa mamaci sauran nau'o'in turare ko kuma a
gauraya su da kafur don shafa wa mamacin.
Mas'ala ta 585:Mustahabbi ne a gauraya kafur din da za a shafa wa mamaci da
kasar kabarin Imam Husain a.s. wato karbala.Amma kada sanya ta da yawa ta yadda
ba za a ce wannan kafur ba ne.
Mas'la ta 586:Idan
ya zamana kafur din da ke akwai ba shi da yawan da za a yi masa wanka sannan a
shafa masa ga gaban sujjada anan sai a gabatar da wanka akan shafawar,haka nan
idan ba zai isa ba a shafa a dukkan gabban sujjadar sai a gabatar da goshi a kan
sauran.
Mas'ala ta 587:
Mustahabbi ne a sanya guntayen itatuwa danyu a cikin kabarin mamaci.
|