Mustahabban Sallar gawa
Masala ta 605:Abubuwa
goma ne suke mustahabbi wajen sallar gawa kamar haka:
NA daya:Mustahhabi
ne wanda zai yi sallar gawa ya kasance yana da alwalla ko wankan wajibi ko
taimama,ihtiyat shi ne zai yi taimama yayin da ba ya da ikon wanka, ko kuma yana
jin tsoron idan ya tsaya yi wanka ko alwalla zai iya rasa sallar.
Na biyu:Mustahabbi
ne idan mamaci namiji ne, liman ya tsaya dai-dai ttsakiyarsa amma idan mace sai
ya tsaya saitin kirjinta.
Na uku:Mustahabi
ne mutum ya fitar da takalmansa yayin da yake yin sallar gawa.
Na hudu:Mustahabbi
ne mutum ya daga hannunsa yayin kowa ne takbiri.
Na biyar:Mustahabbi
ne mtutum ya tsaya kusa da gawar ta yadda da iska zai kada tufafinsa zai iya
taba gawar.
Na shida:Mustahabbi
ne mtum yayi sallar jana'iza a cikin jam'i.
Na bakwai:Mustahabbi
ne liman ya daga muryarsa yayi da yake karanta addu'a,amma sauran mamu su yi a
hankali.
Na takwas:Yayin
sallar jana'iza a cikin jam'i koda mutum biyu ne dayan zai tsaya a bayan liman
ne.
Mustahabbi ne mai sallar jana'iza ya yi wa mamacin addu'a da yawa da sauran
muminai.
Na goma:mustahabbi
ne kafin mutum ya fara sallar ya ce assala sau uku.
Na sha daya:mustahabbi
ne ayi sallar gawar a wurin da mutane sukan cewa a can ne a yin sallar gawa.
NA sha biyu:Mustahabbi
ne macemai haila idan zata yi sallar gawa, ta tsaya ita kadai a bayan sahu.
Mas'ala ta 606:Yin
sallar gawa a cikinmasallaci makaruhi ne,amma amma a cikim masallacin Ka'aba ba
makaruhi ba ne.
Hukuncin rufe mamaci:
Mas'ala ta 607:Wajibi
ne a rufe mutum ta yadda warinsa ba zai fito waje ba,Haka nan dole a rufe shi ta
yada wasu dabbobi ba zasu iya tono shi ba,anan koda ba gudun cewa akwai muatane
a kusa ta yadda idan da ba a rufe shi da kyau ba zai iya yiwuwa su cutu dag
warinsa, ko kuma ba a tsammanin cewa za'a iya samun wata dabba wadda zata iya
tono shi,anan ma ihtiyat shi ne a rufe shi da kyau kamar kwatankwacin yadda ana
tsoron hakan.
Mas'ala ta 608:Idan
da an rasa wurin da za'a gina a rufe mutum,anan ana iya rufe shi ta hanyar a
kwaba kasa yabe shi,ko a sanya shi a cikin akwati a kwaba kasa a yabe.
Mas,ala ta 609:Za
a rufe maamci ne ta hanyar a kwantar da shi bisa hannun dama sannan yakalli
kibla.
Mas,ala ta 610:Idan
mtumya mutu a ciki jirgin ruwa kuma ta yadda jikinsa ba zai lalace ba,sanan kuma
zai iya yiwuwa a yi hakuri har fita daga ruwa,sannan a rufe shi a bisa kasa.Amma
idan ya kaance jikinsa zai iya lalacewa kafin a fita wajen ruwan,anan sai a yi
masa dukkan abin dake yi wa mamaci,sannan sai daura dutsi kafarsa sai saka shi
jikin ruwan,sannan za a saka shi wajen da babu dabbobin da zasu ci namansa da
sauri.
Mas'ala ta 611:Idan
aka ji tsoron kada makiya su tono mamaci daga kabari su wulakanta gawarsa anan
ana iya saka shi cikin kogi kamar yadda muka yi bayani a baya.
Mas'ala ta 612:Kudin
da za a yi amfani da su wajen saka mamaci a cikin kogi ko gyara kabarinsa da
makamantansa idan zai yiwu ana iya dauka a cikin dukiyar da ya bari.
Mas'ala ta 613:Idan
mace kafira ta mutu kuma ta mai ciki,sannan dan da yake ciki cikinta shima ba
shi da rai,idan baban yaron ya kasance musulmi ne,anan dole ne kwantar da ita ta
kalli bayan alkibla ta yadda fuskar yaron zata kalli alkibla.Koda kuwa ba a kai
ga busa masa rai ba.
ُُ
Mas'ala ta 614:Bai
halitta ba a rufe musulmi a makabartar musulmi kamar yadda bai halitta a rufe
kafiri a makabartar musulmi ba .
Mas'ala ta 615:Bai
halitta ba a rufe musulmi a wurin da yake zai iya zma rishin girmamawa a gare
shi kamar inda ake zubar da shara da makamantansu.
Mas'ala ta 616:Bai
halatta ba a rufe mamaci a wurin da aka kwata,haka nan bai halitta ba a rufe
mutum a wurin da aka ware don yin wani abu na musamman kamar masallaci ko wani
wurin taro ko kuma wurin da aka ware don rufe wasu mutane na musaman wato ba na
mutane gaba daya ba ne.
Mas'ala ta 617:Bai
halitta ba a rufe mamaci a cikin kabarin wani ba,sai dai idan wanda aka riga a
rufe a wurin ya riga ya zama kasa ta yadda hatta kasusuwansa ba'a gani.saboda
haka idan ana tsammani cewa akwai yiwuwar cewa wanda aka rufe a wajen har yanzu
bai zama kasa ba wato akwai yiwuwar akwai sauran kasusuwansa,anan bai halitta ba
a tone kabarin don rufe wani a wajen.Kai bai ma halitta ba a tone kabari, sai
dai idan kabarin ya tone da kansa a nan ana iya rufe wani a wajen wancan na
farko idan ya zama kasa babu sauran koda kasusuwansa.
Mas'ala ta 618:Abin
ya cire daga jikin mamaci koda gashinsa ne ko farce ko hakora, dole ne a hada
da shi a rufe yayin bisne sa.Amma idan wadan nan abubuwan da muka ambata a sama
sun rabu daga jikinsa ne lokacin da yake raye anan ba wajibi ba ne amma
mustahabbi ne a rufe su tare da shi.
Mas'ala ta 619:Idan
mutum ya mutu a cikin rijiya,sannan fito da shi ba zai yiwu ba,anan sai a rufe
wannan rijiya ta zama kabarinsa.
Mas'ala ta 620:Idan
jinjiri ya mutu a cikin cikin mahaifiyarsa,sannan kuma barinsa a cikin cikin
mahaifiyar yana da hadari wato zai iya zama barazana ga rayuwarta,anan dole a bi
hanya mafi sauki domin fito da shi daga ciki,koda ya zama dole a yi masa
guntu-guntu babiu laifi akan hakan.Amma wanan aikin mijinta ne zai yi sa idan
yana iya wa idan kuwa ba zai iya ba sai wata mata wadda ta san wannan aikin ta
aiwatar da shi,Idan kuwa ba a samu wata mace ba wadda zata ita wannan aikin sai
a samu wani namiji daga cikin maharramanta ya aiwatar da hakan,Idan kuwa ba a
samu wanda zai iya ba daga cikin maharramanta, wanda ba maharraminta wanda ya
san aikin yana iya fito da dan,Idan kuwa ba a samu wanda ya san aikin ba anan
koda wanda bai san aikin ba yana iya fito da dan domin kasancewar barinsa a
ciki yana da hadari ga ita uwar yaron.
Mas'ala ta 621:Duk
loakcin da uwa ta mutu alhali akwai jinjiri mai rai a cikin cikinta,koda babu
tabbas kan cigaba da rayuwar jinjirin anan sai a fasa cikin ta bangaren hagu a
fito da jinjirin sannan a maida a dinke cikin.
|