Mustahabban rufe mamaci
Mas'ala ta 622:Mustahabbi
ne a yi kabari dai-dai tsawo da fadin mutum matsakaici,sannan mustahabbi ne a
rufe mutu a makabarta mafi kusa, sai idan idan makabartar da take nesa a akwai
wani dalili wanda ya sa za a iya kai mutum a can,kamar idan ya zamana a
makabartar mutane sun fi zuwa ziyara don yi wa mamata addu'a, ko kuma saboda ana
rufe manyan bayin Allah a wurin. Mustahabbi ne bayan an saka mutum a cikin
kabari a kwance dauri da aka yi wa likkafanin,sannan a dangana fuskarsa ga
bangon kabari a sanya wani abu a bayansa ta yadda kada ya dawo baya.Sannan kafin
a rufe mamaci sai a kama kafadarsa ta dama da hannun dama sannan kafadar hagu da
hannun hagu sannan a girgiza shi sannan a ce ya kai wane dan wane,Sannan sai a
karanta wannan addu'ar…….
Mas'ala ta 623:
Mustahabbi ne wanda zai saka mamaci a cikin kabari ya kasance ya tube takalmansa
sannan ya zama kansa a bude,sannan ya kasance yana da alwalla.haka nan idan zai
fito daga kabari sai ya fito ta bangaren kafafun mamacin,Sanana idan akwai wasu
daga cikin wadan da suka halarci jana'izar wadan da ba su daga cikin dangin
mamacin idan zasu iya, sai su tura kasa da bayan hannunsu su rufe mamacin suna
masu cewa…… Idan mamacin ya kasance mace ce,wanda zai shiga cikin kabari ya
zamana daya daga cikin maharramanta wato wadan da suke danginta na kusa wadan da
ba zasu iya aurenta ba.Idan kuwa ba a samu daya daga cikin wadan nan ba sai wani
daga cikin dangi ya saka ta cikin kabarin.
Mas'ala ta 624:Mustahabbi
ne a gina kabari ta yadda tsawonsa ya fi fadinsa (Triangle), sannan ya tasa
sama kamar tsawon yatsa hudu daga kasa,sannan a sanya alama a bisa kabarinsa ta
yadda kada ya bata,sannan bayan an gama rufe mamacin sai a fesa ruwa a sama
sannan mutane daga suka halarci rufe mamacin su dora yatsunsu bisa kabarin su
karanta masa Inna anzalnahu kafa bakwai sannan su nemar wa mamacin
gafarar Allah madaukaki, sai su karanta wannan addu'ar:…
Mas'ala 625:Bayan
wadan da suka halarci jana'izar sun tafi mustahabbi ne waliyyin mamaci ko wanda
yake da izini daga waliyyinsa ya tsaya ya karanta masa addu'o'in da ake wa
mamaci.
Mas'ala ta 626:Mustahabbi ne a yi wa
wadan da aka yi wa mutuwa gaisuwa amma idan lokacin ya wuce don kada a tado masu
abin, bai kamata ba a yi masu gaisuwar.Sannan mustahabbi ne a aika abinci zuwa
gidan mutuwa har tsawon kwana uku,sannan makaruhi ne a ci abinci a gidan mutuwa
har tsawon kwana uku,(wato ga wadan da ba 'yangidan ba)
MAs'ala ta 627:Mustahabbi
ne mutum ya yi hakuri yayin da wani daga cikin danginsa ya mutu musamman idan
dansa ya mutu sannan idan ya tuna wanda ya mutu sai ya ce Inna lillahi
wa'inna ilahi raji'un, sannan mustahabbi ne a karanta wa mamaci kur'ani
sannan mutum yana iya neman biyan bukatunsa daga Allah madaukaki a kan kabarin
Iyayensa,sannan mustahabbi ne a gyara kabari da kyau ta yadda ba zai yi saurin
lalacewa ba.
Mas'ala ta 628:Bai
halitta ba sakamakon rasuwar wani daga cikin dangi, mutum ya yage jikinsa saboda
bakin ciki.
Mas'ala ta 629:Haka
nan bai halitta ba mutum ya yaga kayansa sakamakon mutuwar wani idan ba babansa
ba.
Mas'ala ta 230:Idan
mutum sakamakon mutuwar dansa ko matarsa ya yaga kayansa,ko kuma sakamakon
mutuwar wani, mace ta ji wa kanta ciwo,ta yadda jini ya fita, ko kuwa ta tsige
gashinta,anan dole ne mutum ya yantar da bawa,ko kuma ya ciyar da mabukata
goma,ko kuma ya yi masu tufafi,Idan kuwa ba zai iya aiwatar da wannan ba sai ya
yi azumi guda uku.Ihtiyat koda jini bai fito ba sai mutum ya bayar da abin da
aka fada a sama.
Mas'ala ta 631:Ihtiyat wajib kada
mutum ya daga murya sama da karfi yayin kukan mutuwa.
Sallar wahasha
Mas'ala ta 632:Mustahabbi
ne daren da aka rufe mamaci a yi masa sallar wahasha,wannan salla kuwa raka'a
biyu ce,a raka'a ta farko ana karanta Ayatul kursiyyi bayan Fatiha,a
raka'a ta biyu kuwa ana karanta Inna anzalnahu,sannan bayan an yi sallama
sai a karanta wannan addu'ar…….
Mas'ala ta 633:Ana
iya yi sallar wahasha a kowane lokaci bayan rufe mamacin da daddaren ranar,amma
abin da ya fi shi ne a yi sallar a wannan daren da aka rufe shi.
Mas'ala ta 634:Idan
ana so a kai mamaci wani gari don a rufe shi a can ko kuwa saboda wani dalili
ana so a jinkirta rufe shi,anan sai a jinkirta yi masa wannan sallar har zuwa
daren da aka rufe shi.
Tone kabari
Mas'ala ta 635:Haramun
ne a tone kabarin musulmi koda kuwa karamin yaro ne ko mahaukaci,amma idan jikin
mamacin ya zama kasa babu laifi don an tone shi.
Mas'ala ta 636:Haramun
ne a tone kabarin Manyan bayin Allah koda kuwa ya dauki tsawon shekaru kamar
yadda muka fada a sama.
Mas'ala ta 637:Halas
ne a tone kabari a wadan su lokutta kamar haka:
Na daya:Idan
aka rufe mamaci a wani wuri sai mai wajen bai amince ba.
Na biyu:Idan
ya zamana likafanin da ka rufe mamaci da shi ba na halas ba ne,sannan kuma mai
shi bai aminta ba,ko kuwa idan aka rufe mutum da dukiyar da ya kamata ya bar wa
masu gadonsa,sannan kuma masu gadon ba su aminta da a bar dukiyar ba,amma idan
mutum ya yi wasiyya akan a rufe shi da wani kur'ani ko zobe,sannan abin bai kai
yawan daya bisa uku na dukiyarsa ba anan ba sai an tono shi ba.
Na uku:Idan
aka rufe mamaci ba tare da an sanya masa likkafani ko an yi masa wanka ba ko
kuma aka fahimci cewa wankasa bai inganta ba, ko kuwa an sanya masa likkafani ba
kamar yadda shari'a ta bayyana ba,ko kuwa ba a sanya shi cikin kabari ba kamar
yadda ya kamata a sanya shi, kamar a sanya shi bai kalli kibla ba,amma anan ma
sai idan tone kabari ba zai zama keta alfarmar mamacin ba,amma idan zai zama
keta alfarmarsa kamar a samu jikinsa ya riga ya lalace ko wani abu makamancin
hakan,anan bai halitta ba a toneshi.Amma idan aka rufe mutum ba a yi masa salla
ba,anan bai halitta ba a tone kabarinsa don a yi masa salla,anan ana iya yi
masa salla akan kabarinsa.
Na hudu:Idan
za a tone mamaci ne domin a tabbatar da wani abu kamar binciken likita idan ana
so a tabbatar da wani abu a kansa.
Na biyar:Idan
ka rufe musulmi a wani wuri inda yake kamar rishin girmama wa ne garesa kamar
idan an rufe sa a makabartar kafirai ko wurin da ake zubar da kazanta, anan ana
iya tono shi domin a maida shi makabartar musulmi.
Na shida:Idan
za'a aiwatar da wani abu wanda yake muhimmi kamar a na so a ceto jinjirin da
yake cikin cikin macen da ta mutu,kuma dan yana da rai.
Na bakwai:Idan
aka samu wani bangaren jikin mamaci bayan an riga na rife shi kamar sakamakon
hadari sai wani bangare jikinsa ya bata sai aka gane shi daga baya,anan ana iya
tone kabarinsa don a hada a rufe.
Na takwas:Idanb
ana jin tsoron kada wasu dabbobi su tone gawarsa su cinye.
Na tara:Idan
mutu ya yi wasiyya akan cewa akai shi wuri mai tsarki a rufe,sai aka manta ko
kuma da gangan a ka rufe shi a wani wuri daban,anan anan iya tone shi don a kai
shi inda ya yi wasiyya a rufe shi a can.Amma idan tone shi zai zama kamar keta
alfarmarsa wato jikinsa ya riga ya fara lalacewa anan bai halitta ba a tone shi.
|