Taimama
Taimama tana wajaba a wurare guda bakwai wato
maimakon alwalla ko wanka dole ne a yi taimama.
Wuraren da ake yin taimama:
NA DAYA:Lokacin da mutu ba zai iya samun
rowan dazai yi alwalla ko wanka ba.
Masála ta 642:Idan mutum yana wurin da za
a iya samun ruwa,anan dole ne mutum ya yi iya kokaronsa wajen neman ruwan da zai
alwalla ko wanka sai idan ya yanke kauna akan cewa lallai ba zai samu ba.Idan
mutum ya kasance a cikin daji inda yanayin wurin yana tudu da kwari ta yadda ba
zai yiwu ba mutumya yi tafiya cikin jin dadi,anan sai mutum ya yi tafiya kowane
bangare tsawon nisan idan da za a harba kibiya zata iya zuwa wurin.Wato ya yi
tafiya gabas da yamma kudu da arewa,idan bai samu ruwa ba sannan ya yi taimama.
Masála ta 643:Idan ya zamana wurin da
mutum ya samu kansa yana da tudu da gangara, ko kuma tafiya don neman ruwa yana
da wuya a garesa,anan sai ya ya yi tafiya kamar nisan harbin kibiya a wurin da
yake ba ya da hawa da gangara,sannan ya yi kimanin hakan a wurin da yake da hawa
da gangara.
Mas'ala ta :644:Duk wurn da mutum yake da
tabba s ba za a samuruwa ba,anan ba dole ba ne ya yi tafiya kamar kimanin da
muka fada a sama.Anan kawai yana iya yin taimamarsa.
Mas'ala ta 645:Idan lokacin salla bai kure
ba kuma mutum yana da yakini akan cewa zai samu ruwa kafi lokacin salla ya
kure,anan dole ne ya yi kokari ya binciki ruwan idan har babu wani abu da zai
hana yin hakan kuma ba zai zama wahalarwa ba,amma idan mtum Kawai yana tsammani
ne kan samun ruwan,anan ba dole ba ne ya tafi neman ruwan koa kuwa lokaci bai
kure ba.Amma idan mutu ya natsu akan cewa zai samu ruwa a wani wuri anan ihtiyat
wajib shi ne ya ta fi wajen don ya samo ruwan da zai yi alwalla.
Mas;ala ta 646:Ba dole ba ne mutum ya tafi
da kansa don ya nemo ruwan da zai yi alwalla,idan ya tura wani ma don ya samo
masa ya wadatar.Saboda haka idan mutum daya ya tafi don ya samo wa mutane da
yawa ruwan da zsu yi alwalla hakan ya inganta.
Mas'ala ta 647:Idan mtutm ya yi tsammanin
cewa a cikin kayansa da yake tare da su yayin tafiya akwai ruwa ko kuma a cikin
gidansa,anan dole ne ya yi bincike ta yadda zai tabbatar da akwai ko babu,ko
kuma ya yanke kauna daga samun ruwan.
Mas'ala ta 648:Idan mutum tun kafin
lokacin salla ya isa ya nemi ruwa kuma bai samu ba,sanna kuma bai bar wurin da
yake ba har lokacin salla ya isa,anan ba dole ba ne ya sake binciken ruwan don
ya yi alwalla.
Mas'ala ta 649:Idan mutum ya nemi ruwa don
yin alwalla lokacin da salla ya isa,kuma sai bai samu ruwan ba,anan idan bai bar
wannan wurin ba har wani lokacin sallar ya sake yi, anan ba sai ya sake neman
ruwan ba.Amma idan yana tsammanin cewa za iya samun ruwan anan ihtiyat wajib shi
ne ya sake bincikawa.
Mas;ala ta 650:Idan mutum ya ji tsoron
wata dabba mai cutarwa ko barawo ko kuma akwai wahala mai tsanani akan neman
ruwan anan ba dole ba ne ya nemi ruwa don ya yi alwalla.
Mas'ala ta 651:Idan mutum bai tafi neman
ruwan da zai yi alwalla ba har sai da lokacin salla ya kure anan yana iya yin
salla da taimama kuma sallarsa ta yi amma kuma ya yi zunibi akan rishin neman
ruwan da ya yi.
Mas'ala ta 652:Wanda ya samu tabbas akan
cewa ba zai samu ruwa ba,sai ya yi salla da taimama ba tare da ya nemi ruwan
ba,amma bayan ya yi sallar sai ya fahimci cewa idan da ya binciki ruwan da ya
samu,anan sallarsa ta ba ci.
Mas'ala ta 653:Idan mutum ya yi salla
bayan ya binciki ruwa bai samu ba,bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa a
wurin da ya binciki ruwan bai samu ba akwai ruwa a wajen,anan sallarsa ta
inganta.
Mas'ala ta 654:Idan mutum ya kasance yana
da alwalla bayan lokacin salla ya shiga,sannan ya san cewa idan ya bata
alwallarsa ba zai samu ruwan da zai sake alwalla ba,anan idan har zai ya rike
alwallar dile ne ya rike ta har ya yi sallar.
Mas'ala ta 655:Idan mutu ya kasance yana
da alwalla kafin lokacin salla ya isa,sanna ya san cewa idan ya bata alwallarsa
ba zai samu wani ruwan da zai yi alwalla ba,anan idan zai iya rike alwallar
ihtiyat wajib shi ne ya rike alwallar har lokacin salla ya isa don ya yi
sallarsa da alwalla.
Mas'ala ta 656:Idan yana da ruwan da zai
yi alwalla ko wanka kuma ya san idan ya zubar da wannan ruwan ba zai samu wani
ba wanda zai yi alwalla ko wanka,anan idan lokaci salla ya isa ne haramun ya
zubar da wannan ruwan da yake da shi,haka nan idan lokacin sallar bai isa
ba,ihtiyat wajib shi ne kada ya zubar da wannan ruwan.
Mas'ala 657:Wanda ya ke da tabbas akan
cewa ba zai samu ruwa ba,Bayan lokaxcin salla ya isa sai ya bata alwallarsa ko
ya zubar da ruwaan da yake da shi, anan ya yi sabo,amma sallarsa da ya yi da
taimama ta inganta,duk da cewa ihtiyat mustahab shi ne ya rama wannan sallar.
|