NA BIYU
Mas'ala ta 658:Idan mutum sakamakon tsufa
ko kuam tsorn wata dabba mai cutarwa idan ya tafi neman ruwa, ko kuma ya rasa
abin da zai yi amfani da shi domin ya jawo ruwa daga rijiya,anan sai ya yi
sallarsa da taimama.
Mas'ala ta 659:Idan ya zamana mutum sai
ya biya kudi sannan a jawo masa ruwa,anan koda kudin da zai biya sun ninka
kudin da ya kamata,anan dole ne ya biya domin ya samu ruwan da zai yi alwalla ko
wanka,amma idan ya zamana kudin da aka nema daga gare shi zai iya cutarwa idan
ya bayar da su,anan ba dole ba ne ya biya wadan nan kudin don ya samu ruwan da
zai yi amfani da su.
Mas'ala ta 660:Idan ya zamana mutum sai ya
ci ba shi kafin ya samu ruwan da zai yi alwalla ko wanka, anan yana iya cin
bashi don ya samu ruwan.Amma idan mtum ya san ba zai samu kudin dazai biya
wannan bashi ba a cikin sauki,anan ba sai ya ci ba shiba,sai ya yi taimama ya yi
sallarsa.
Mas'ala ta 661:Idan ya zamana gina rijiya
ba zai zama wahalrwa ba ga mutum domin ya samu ruwan da zai yi alwalla anan dole
ya gina rijiyar donya samu ruwan da zai yi alwalla.
Mas'ala ta 662:Idan wani ya ba mutum ruwan
da yi alwalla ko wanka sannan mutumba zai yi masa gori ba daga baya,anan yana
iya kabar ruwan ya yi amfani da su.
NA UKU:
Mas'ala ta 663:Idan mutum ya ji tsoron
cutarwa idan ya yi amfani da ruwa,wato sakamakon hakan zai iya rishin
lafiya,kuma rishin lafiyar zata iya zama mai tsanani anan dole ne ya yi
taimama ya yi sallarsa. Amma idan ruwa mai zafi ba zai cutar da shi ba,anan dole
ne ya tanaji ruwan da zai yi amfani da su.
Mas'ala ta 664:Ba dole ba ne mutum ya zama
yana da tabbas akan cewa ruwa zan cutar da shi idan mutum yana tsammanin ma
hakan ko kuma mutanen da suka san hakan suka gaya masa,anan dole ne ya yi
taimama maimamakon alwalla ko wanka.
Mas'ala ta 665:Wanda yake da ciwon dio
kuma ruwa zai iya cutar da shi idan ya yi alwalla ko wanka,anan dole ne ya yi
taimama.
Mas'ala ta 666:Idan mutum ya yi taimama
sakamakon tsoron cutarwa,amma kafin ya yi salla sai ya fahimci cewa babu wata
cutarwa,anan taimamarsa ta baci.Saboda haka ba zai iya yin salla ba da wannan
taimamar,Amma idan sai da ya gama salla ta fahmci hakan anan sallarsa ta
inganta.Amma dole ne ya yi alwalla don yin sallar da zai a gaba.
Mas'ala ta 667:Wanda yake tunanin cewa
ruwa ba zai cutar da shi ba, idan ya yi wanka ko alwalla,sai daga baya ya
fahimci cewa ruwan yana da cutarwa a garesa,anan alwallarsa ko wanka sun
inganta.
NA HUDU:
Mas'ala ta 668: Duk lokacin da mutumya ji
tsoron cewa idan ya yi amfani da ruwan da yake da shi zai iya shiga matsala ko
iyalinsa ko wani wanda yake karkashinsa zai samu wata matsala kamar ta rishin
lafiya ko kishirwa da bai zai yiwu ba a daure mata,anan dole ne mutum maimakon
alwalla ko wanka sai ya yi taimama.Haka nan idan ya ji tsoron cewa wata dabbarsa
zata iya hallaka sakamakon kishirwa yana iya bata ruwan shi kuma ya yi taimama
maimakon alwalla ko wanka.Haka idan wani yana bukayar ruwan ta yadda idan ya
hana shi ruwan yana iya mutuwa,anan dole ne ya ba shi ruwan don ya ceci
rayuwarsa, shikuma sai ya yi taimama.
Mas'ala ta 669:Idan mutum yana da wani
ruwa ban ruwa mai tsarki wanda ya tanada saboda alwalla,wato yana da wani ruwan
amma mai najasa ne,anan sai ya yi amfani da ruwa mai tsarkin domin shi kuma ya
yi taimama maimakon wanka ko alwalla,amma idan yana so ya ba dabbarsa ne
ruwa,anan sai ya ba dabbar ruwan mai najasa shi kuma ya yi alwalla ko wanka da
ruwan mai tsarki.
|