NA BIYAR
Mas'ala ta 670:Mutumim da ya kasance
tufafinsa ko jikinsa yana da najasa kuma yana da ruwan da kawai zai ishe shi ya
yi awalla ta yadda idan ya yi alwalla da shi ba zai isa ba ya wanke tufafinsa,
anan sai ya wanke tufafin ko jikinsa mai najasa sai ya yi taimama don yin
salla.Amma idan ya kasance babu abin da zai yi taimama da shi,anan sai ya yi
wanka ko alwalla da ruwan sai ya yi sallar da tufafin ko jikinsa da yake da najasa.
NA SHIDA:
Mas'ala ta 671: Idan ya kasance babu wani
ruwa ko wurin alwalla wanda ya hallata mutum ya yi mafani da su, kamar ya
zamana sai ruwan da yake na kwace ko butar kwace,anan saimutum ya yi taimama
maimakon alwalla ko wanka.
NA BAKWAI:
Mas'ala ta 672:Duk lokacin da ya kure ta
yaddamutum ba zai iya yin alwalla ko wanka face sai idan ya yi hakan to zai yi
wanibangare daga cikinsallarsa wajen lokacin,anan mutum yana iya yin taimama
maiumakon wanka ko alwalla.
Mas'ala ta 673:Idan mutum ya yi jinkiri
wajen yin salla ta yadda mutum ba zai samu lokacin da zai yi alwalla ko wanka ba
kafin lokaci ya fita,anan mutum ya yi sabo amma idan ya yi salla da taimama ta
inganta.Duk da cewa ihtiyat mustahab shine mutum ya rama wanna sallar shi ya fi.
Mas'ala ta 674:Wanda yake shakka idan ya
tsaya yin alwalla ko wanka lokaci ba zai isa ba ta yadda zai iya yin salla cikin
lokaci,anan sai ya yi sallarsa da taimama kuma ta inganta.
Mas'ala ta 675:Wanda ya yi taimama
sakamakon kurewar lokaci,aiki da taimamar yana inganta akan abin da kawai
lokacinsa ya kure,saboda haka ba tare da bata wani lokaci bayan aiwatar da wanna
aikin taimamar ta baci.Saboda haka kodamutum bayanya gama salla sai ya rasa
ruwan da yake da shi, ko kuma wani uzuri ya same wanda dole taimama zai yi,anan
koda wannan taimamar da ya yi ba ta baci ba,dole sai sake wata domin yin wani
aikin da yake bukatar alwalla.
Mas'ala ta 676:Wanda ya ksance yana da
ruwa,Idan ya kasance sakamakon kurewar lokaci ya yi taimama ya ci gaba da yin
salla,a lokacin sai ya rasa ruwan da yake da shi,anan ba zai iya salla ta gaba
ba, da wannan taimamar da yake da ita,domin kua ya yi ta ne sakamakon kurewar
lokaci,saboda haka dole ya sake wata ataimamar don salla ta gaba.
Mas'ala ta 677:Idan mutum yana da lokacin
da zai ishe shi yayi wanka ko alwalla sannan ya gabayar da sallarsa, ba tare da
yin wasu abubuwa ba na mustahabbi,anan ya wajaba ya yi amfamni da wanna lokacin
ya yi wanka ko alwalla domin ya yi salla tare da alwalla.Haka nan kodalokacin da
yake da shi kawai zai ihse shi ne ya iyakarnta Fatiha ba tare da sura ba, anan
dole ne ya yi wanka ko alwalla ya yi sallarsa ba tare da karanta sura ba.
ABUWABUWAN DA YA INGANTA AYI TAIMAMA AKAI:
Mas'ala ta 678:Ya inganta a yi taimama
akan kasa dutse,yashi idan sun kasance masu tsarki.Haka nan ya inganta akan
tubali ko bulo din kasa ko da kuwa an gasa shi.
Mas'ala ta679:Ya inganata a yi taimama kan
marmara da dai makantansu, amma bai haloitta ba a yi taimama akan dutsin da ake
kwalliya da shi,Ihtiyat wajib shi ne,kada atyi amfani da fara kasa wajen yin
taimama.
Mas'ala ta 680:Idan mutu bai samu
kasa,yashi ko dutse ba,mutumyana iya taiama da kurar da take bisa shinfida ko
tufafinsa, da makamancinsa,haka nana idan da mtum bai samu kurara da zai iya
taimama da ita ba,yana iya yin taiamama da yumbu,idan yumbu ba bai samu
ba,ihtiyat wajib shi ne ya yi sallar ba tare da taimama ba.Amma wajibi ne ya
rama wanna sallar.
Masa'la ta 681:Idan mutum yana iya samun
kasa ta hanya kakkabe darduma da makamcinsa,bai inganta ba ya yi timama da
kura,haka idan da mutum zai iya busar da yumbu ta yadda zai iya samu kaar da zai
yi taimama, bai inganta ba ya yi da danyan yumbun.
Mas'ala ta 682:Mutum da ba ya da ruwan da
zai alwalla amam yana da kankara, idan zai yiwu yamayar da ita ruwan ya yi
alwalla,anan dole ne ya yi hakan don ya yi wanka ko alwalla,idan kuwa ba zai
hakan ba zai yiwu ba,kuma ba shi da abin ya ya inganta a yi taiamama
akansa,ihtiyat wajib shi ne aya yi salla ba tare da alwalla ko taimama ba,amma
daga baya sai ya rama sallar.
|