Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Abubuwan da taimama take inganta akai

Mas'ala ta 683:Idan kasa ko yashi ya gauraya da wani abin  da bai halita ayi taimama da ba,idan mutumya yi taimama da kasar ta baci,amma idan abin ya ksance dan kadan ne ta yadda ba za a iya cewa ba ma akwai shi,anan ba wani abu mutum yana iya taimamar da shi.

Mas'ala ta 784:Idan mutum ba shi da abin ya inganta a yi taiamama da shi,idan zai yiwu ko ta haryar saye ne ko makamancin hakan dole ya tanaji abin ya yi taimamar.

Mas'ala ta 685:Ya inganta mutumya yi taimama akan bangon kasa,Mustahabbi ne mutum yakauce wa yin taimama da kasa mai lema idan har akwai wadda ba ta da lemar.

Mas'ala ta 686:Dole ne abin da za a yi taimama akansa ya zama mai tsarki,Idan mutum ba shi da abin da yake da tsarki daga cikin abubuwan da ya halitta a yi taimama a kai,ihtiyat wajib shi nemutum ya yi sallar ba tare da taimama ba,amma bayan matsalar ta gushe sai ya rama sallar.

Mas'la ta 687:Idan mutum ya samu yakini akan ingancin alwalla akan wani abu,sai ya yi taiamama a kai,amma daga baya sai ya fahimci cewa bai inganta ba ayi taimama akai,anan sallolin da ya yi a kai sun ba ci dole ne ya sake su.

Mas'ala ta 688:Dole ne abin da mutum zai yi taimama a kai ya zama na halas.

Mas'ala ta 689:Idan mutum ya yi taimama a wurin da yake na kwace ne,wannan taimamar ta inganta,Saboda haka idan mutum ya bugi kasa a wurin da yake na shi ne,amma sai ya shiga wani wurin da yake ba na shi ba ne ya shafi hannu da fuskarsa,wannan ba ya bata taimamarsa

Mas'ala ta 690:Idan mutum ya yi taimama da abin da  bai san cea ba, ba na halas ba ne; ko kuma ya manta da cewa ba na halas ba ne,a nan taimamarsa ta inganta,sai dai i dan ya kasance shi da kansa ne ya kwacvi wannan abin daga wani,sannan ya manta  ya yi taimama da shi, a nan ihtiyat wajib shi ne taimamarsa ta baci.

Mas'ala ta 691:Wanda aka rufe a wuri ns kwace, sannan ruwa da kasar wurin dukkansu na kwace ne,a nan dole ne ya  yi salla da taimama.

Mas'ala ta 692:Mustahabbi ne abin da mutum zai yi taimama da shi ya kasance yana da kasa a kansa ta yadda kasar zata like a kan hannnayensa bayan ya buga kasa sannan ya kakkabe hannnyensa.

Mas'ala ta 693:Makaruhi ne mutum ya yi taimama akan kasar bisa titi ko kasar da take da gishiri amma babu gishirin a kanta.Idan kuwa akwai gishiri a kai a nan taimama ta baci.

Yadda ake taimama :

Mas'ala ta 694:Abubuwa hudu ne suke wajaba a taimama:

Na daya:Niyya

Na biyu:Bugun kasa a kan abin da taimama ta halitta a kai.

Na uku:Shafar goshi da gefensa da hannaye da mutum ya bugi kasa da su,wato daga wurin da gashi yake fitowa zuwa gira da saman karan hanci,ihtiyat wjib shi ne mutum ya shafi har saman girarsa.

Na hudu:Shafar dukkan saman tafin hannun dama da cikin tafin hagu,sannan shafar saman tafin hagu da cikin hannun dama.

Mas'ala ta 695:Taimar da mutum zai yi a matsayin wanka da wadda zai yi a matsayin alwalla ba ta da bambanci duk daya ne yadda ake yinta.Amma ihtiyat mustahab shi ne taimamar da mutum zai yi a maimakon wanka sai ya bugi kasa sau biyu,wato bugu na farko ya shafi goshinsa bugu na biyu kuwa ya shafi saman hannayensa.ihtiyuat mustahab ma shi ne koda taiamamar zai yi ta ne a matsayin alwalla kawai ya kamata ya yi bugun kasar sau biyu kamar yadda muka fada a baya.Sannan abin da duk ya fi ma shi ne ya yi bugun kasan sau uku,wato ya buga sau biyu a lokaci guda sai ya shafi goshinsa,sanna ya sake bugawa sau daya sai ya shafi bayan hannayensa.