hukuncin taimama
Mas'ala ta 696:Idan da mutum bai shafi wani bangare ba daga cikin
godhi ko bayan tafin hannunsa, a nan taiamarsa ta abci, wannan kuwa da angan ne
ko kuwa a halin antuwa ne.Duk da cewa ba sai mtum ya kwalailaice ba
a kan cewa ya shafi dukkan wuraren da zaran yana jin cewa ya shafi ko'ina din ya
wadatar.
Mas'ala ta 697:Domin mutumya samu tabbas cewa ya shafi dukkan bayan
tafin hannunsa,a nan yana iya danshafar saman wuyan hannunsa don ya samu yakini
a kan hakan.Amma ba dole ban e mutum ya shafi tsakanin yatsaunsa.
Mas'ala ta 698:Ihtiyat wajib shi ne a shafi goshi daga sama zuwa kasa
kamar yadda ake alwalla,haka nan wajen shafar bayan tafin hannaye.Sannan dole ne
mutum ya aiwatar da wadan nan ayyuka ba tare samun tazara ba a tsakanin
juna,saboda haka idan ya zamanaakwai azara da yawa taimamar ta baci.
Mas'ala ta 699:Dole nemutum ya ayyana cewa cewa zai yi taimama
ne a matsayin wanka kokuwa a matsayin alwalla,saboda haka da mutum zai kuskure
maimakon ya yi taimama a matsayin wanka sai ya yi a matsayin alwalla,ko kuma zai
yi taiamma ne a matasayin wankan janaba,sai ya yi niyyar taimama amatsayin
wankan shafar mamamci,a nan taimamarsa ta baci.Haka nana idan taiamama daya ta
hau kan mutum idan wajen niyya ya manata ya niyyar wani abu daban taimamar ta
wadatar.
Mas'ala ta 700:Dole ne a wajen taiamama ya zamana goshi da bayan tafin
hannaye su zama suna da tsarki,Saboda haka idan ya zamanaa tafin hannu akwai
najasa kuma mutum bai samun ruwan da zai tsarkake najasar ba,sai ya yi taiamamar
da haka nan idan dai najasar ba mai lema mace,idan kuwa mai lema ce,anan sai ya
yi taimamar da zira'in hannu.
Mas'ala ta 701:Idanmutum zai yi taiamama dole ne ya fitar da zoben da
yake a hannunsa,haka nan idan akwai wani abu a tafin hannunsa ko bisa goshinsa
ko bayan hannunsawanda zai iya hana shafar fatarsa dole ne ya gusar da shi kafin
ya yi shafar a kai.
Mas'ala ta 702:Idan ya zamana akwai ciwo a bisa goshi ko bayan tafn
hannu,ta yadda ba zai yiwu ba kwance abin da aka daure ciwon da shi,a nan sai a
shafi bisa kyallen da aka daure ciwon,haka nana idan tafin hannun wanda za a
bugi kasa da shi yana da ciwo ta yadda an daure shi da wani abu, kuma ba zai
yiwu ba a kwance,a nan sai ya bugi kasar da daurarren hannun ya yi shafar da
shi.
Mas'ala ta 703:Idan ya zamana a kan goshi ko bayan tafin hannu akwai
gashi babu wani abu a na iya yin shafa a kai.Amma idan gashin da yake akan goshi
ya sabko ne daga bisa kai,a nan dole ya ya janye shi sannan ya yi shafar a kan
goshin
Mas'ala ta 704:Idan mutum yana tsammanin cewa akwai wani abu a bisa
goshinsa ko bayan tafin hannunsa,wanda zai iya hana ya shafi fatar bayan hannun
ko goshi,sannan ya kasance zaton da yake yi ya zama abin kula ga sauran mutane,a
nan ya kamata ya bincika don ya tabbatar da cewa babu,idan kuma akwai ya kawar
da shi sannan ya yi shafar.
Mas'ala ta 705:Idan ya zamana mutum taimama ya kamata ya yi,amma ba ya
iya yin taimamar,a
nan dole ne ya samu wani a madadinsa ya yi masa taimamar,wato ya kama
hannunsa ya buga a bisa kasa sannan ya shafi goshinsa da bayan yafin
hannunsa.Idan kuwa hakan ba zai yiwu ba, a nan sai wakilinsa ya bugi kasar da
kansa ya yi masa shafar.wato ba dole sai ya sanya hannun marar lafiyar ba.
Mas'ala ta 706:Idan mutum bayan ya fara taimama sai yayi shakka a kan
cewa shin ya shafi sashen da ya kamata ya fara shafa ko kuwa,a nan kada ya kula
da shakkunsa taimamarsa ta inganta.
Mas'ala ta 707:Idan bayanmutum ya shafi bayan hannun hagu sa ya yi
shakka a kan cewa shin taimamarsa ta yi dai-dai ko kuwa,a nan ba zai kula da
wannan shakkar ba timamarsa ta inganta.
Mas'ala ta708:Idan ya kasance taimama ce ta hau kansa, ihtiyat wajib
bai kamata ba, ya yi taimama kafin lokacin salla,amma idan ya yi taimama saboda
wani aiki daban sannan ba ta baci ba har lokacin salla ya yi,kuma uzrin da yake
da shi bai kau ba,yana iya yin salla da ita.
Mas'ala ta 709:Wanda ya kasance taimama ce ta hau kansa,idan ya san
cewa har ya zuwa karshen lokacin salla wannan uzirin da yake da shi ba zai kau
ba,a nan yana iya yin taimamarsa ya yi salla,amma idan ya san cewa zuwa karshen
lokaci uzirinsa zai gushe, a nan dolene ya jinkirta zuwa karshen lokacin don ya
yi sallarsa da alwalla ko wanka.
Mas'ala ta 710:Wanda ba zai iya yin alwalla ko wanka ba,yana iya yin
sallolin da ake binsa da taimama,duk da cewa yana tsammanin cewa uzirinsa zai
iya gushewa da sauri,amma idan yana da tabbas akan cewa uzirinsa zai gushe kafin
lokacin ramuwar ya guhse,anan yana iya jinkirtawa don ya yi ramuwarsa da
alwalla.Amma idan ya tsammanin cewa zai iya rasa sallar ramuwar a nan yana iya
yin sallarsa da taimama.(misali kamar yasan cewa zai iya mutuwa kafin lokacin da
zai iay samun damar yin alwalla ko wanka).
Mas'ala ta 711:Mutumin da ba zai iya yin alwalla ko wanka ba,Yana iya
yin sallolinsa na mustahabbi da taimma, wadan da suke da lokaci ayyananne,amma
da sharadin cewaya san uzirinsa ba zai gushe ba harzuwa karshen lokaci.
Mas'ala ta 712:Idan mutum sakamakon rishin ruwa ya yi taimama,idan ya
samu ruwa wannan taimamar ta baci.
Mas'ala ta 713:Abubuwan da suke bata alwalla suna bata taimama,Haka
nan abubuwan da suke bata wanka idan mutum ya yi taimama maimakon wanka,idan
daya daga cikin wadan baubuwan suka faru,taimamarsa ta baci.
Mas'ala ta 714:Mutumin da ba zai iya yin wanka ko alwalla
ba,Idan yana da wanka da yawa da suka wajaba a kansa,a nan ihtiyat wajib sai ya
yi taimama a maimakon kowane wanka daya,wato duk wakan daya taimama daya.
Mas'ala ta 714:Mutumin da ba zai iya yin wanka ba,Idan yana so ya yi
wani bau wanda wajibi ne sai da wanka,a nan sai ya yi taimama maimamkon
wankan,haka nan idan yana so ya yi wani bau wanda dole sai da alwalla,a nan
wajibi ne ya yi taimama maimakon alwallar.
Mas'ala ta 716:Idan mutum ya yi taimama maimamon wankan janaba,anan ba
dole ba ne ya yi alwalla donyin salla.Amma idan mtum ya yi taimama maikon wani
wanka da ya wajba a kansa,wanda ba na janaba ba,a nan dole ne ya yi alwalla
kafin ya yi salla.idan ba zai yiuwuba ya yi alwalla sai ya yi taimama maimamakon
alwallar.
Mas'ala ta 717:Idan mutum ya yi taimama maimakon wanka,sannan sai ya
yi wani abu wanda yake bata alwalla,sannan ba zai iya yin wanka ba don sallolin
da zai yi a gaba,a nan dole ne ya yi alwalla,idan kuwa ba zai iya yin alwalla
ba,sai ya yi taimama maimakon alwallar.
Mas'ala ta 718:Mutum da ya kasance dole ne ya yi taimama maimamkon
alwalla da wanka,wannan taimamar ta wadatar da shi, yana iya sallolimsa da ita.
Mas'ala ta 719:Mutum da ya kasance taimama ta hau kansa,idan ya yi
taimama don wani aiki,idan har uzirin da yake da shi bai gushe ba, kuma wannan
taimamar ba ta baci ba, yana iya sauran abubuwan da dole sai da alwalla ko
wamka.Amma idan ya yi wannan taimamar ne saboda kurewar lokaci,wato yana ruwan
da zai yi alwalla,a nan aikin da ya yi taimamar saboda shi kawai zai iya yi.
Mas'ala ta 720:Wuraren da yake mustahabbi ne idan mutum ya yi
sallolinsa da taiama ya sake:
Na daya:Idan mutum yana jin tsoron amfani da ruwa sai kuma da gangana
ya yi janaba,sai ya yi salla da taimama.
Na biyu:Idan mutum yana tsammanin cewa ba zai samu ruwa ba, kuma sai
ya yi janaba da ganagan,sai ya yi sallarsa da taimama.
Na uku:Idan mutum har zuwa karshen lokaci bai nemi ruwa ba,sai ya yi
sallarsa da taimama,bayan ya gama sai ya fahimci cewa da ya nemi ruwan da ya
samu.
Na hudu:Idan mutum ya jinirta salla da dangan sai karshen lkacin sai
ya yi sallar da taimama.
Nabiyar:Idan mutum ya san ba zai samu ruwa ba sai ya zubar da ruwan da yake
da shi sai da lokacin salla ya isa,sai ya yi sallar da taimama.
Mas'ala ta 721:Wajibi ne mutum ya sitirta al'aurarsa ya yin da yake
biyan bukatarsa(zagayawa) daga idanun wadan da suke sun balaga,koda kuwa na kusa
da shi kamar Kanwa,uwa ko wani dan'uwansa ne,haka nan koda yaro bai balaga
ba amma yana gane abin da ake ciki ko mahaukaci,wajibi mutum ya boye al'aurarsa
daga idanunsu.Amma ba wajibi ba ne tsakanin miji da mata.
Mas'ala ta 722:Duk lokacin da mutum ya tsarkake wurin da kashi yake
titowa da da dutsi ko wani abu makamancinsa,duk da cewa akwai matsala wajen
kasancewar wurin mai tsarki nr amma mutum yana iya yin salla hakan.
Mas'ala ta 723:Idan mtutm yana so tsarkake abin ya samu najasa daga
fitsari da ruwa kadan,anan idan ya zuba ruwa kan abi sau daya sannan ya gusar da
ruan daga abin,idan idan fitsari ya gushe sai zuba ruwa sau daya abin ya
tsarkaka.Amma idan tufafi ne ko darduma dole ne ya matse abin bayan ya zuba
ruwan.
Mas'ala ta 724:Idan mutum ya kasan ce yana daciwo akan fuska ko
hannu,sannan kuma ciwon yana bude,sannan zuba ruwa a kan abin zai iya cutarwa,a
nan sai ya mutum ya wanke gefen ciwon sannan idan shafar bisa ciwon ba zai
cutarba sai ya shafi saman ciwon.idan kuwa zai iyacutarwa sai ya dora wani
kyalle sai ya shafi samansa da hannunsa mai lema.Amma idan ya zamana wannan ma
zai iya cutarwa,ko kuma akwai najasa akan ciwon,a nan sai ya wanke gefen ciwon
daga sama zuwa kamar dai yadda ake alwalla,sannan ya yi taimama.
Mas'ala ta 725: Idan mutum ya shafi jikin gawar data yi sanyi sannan
kuma ba a kai ga yi mata wanka ba,a nan dole ne mutum ya yi wankan taba
gawa,anan kuwa koda mutum ya taba gawar ne yana cikin barci ko yana farke cikin
niyya ne ko ba cikin niyyarsa ba ne, koda kuwa farcensa ne ya taba ko kashinsa
ya taba gawar dole ne ya yi wanka.Amma idan mutum ya taba gawar dabbar ba dole
ba ne ya yi wanka.
|