|
Hukunce-Hukuncen Salla
Salla ita ce mafi mahimmancin daga cikin bautar Ubangiji
madaukakin sarki,sannan idan aka karbi sallar mutum zaá karbi sauran
ibadojinsa,idan kumwa baá karbi salla ba to ba za a karbi sauran ibadojinsa
ba.Haka nan ta bangaren tsabta yayin da mutum ya yi salla saura biyar a rana
wato ya ya kan tsarakake jikin sau biyar kenan. Haka nan salla guda biyar a rana
takan tsarkake zuciyar mutum daga zunubi.Sannan ya kamata mutum ya yi salla a
farkon lokacin sallar,saboda haka wanda yake wulakanta salla ko ba ya ba ta
muhummanci kamar wanda ba ya yin salla ne.Manzo mai tsira yana cewa:"Duk wanda
ba ya ba salla muhimmanci wannan mutumin ya canci azabar lahira." Wata ran manzo
s.a.w.a yana zaune a cikin masallaci sai wani mtum ya shigo masallaci ya cigaba
da salla,sannan ya kanyi rukuú da sujada ba kamar yadda ya ya kamata
ba,sai manzo ya ce:"Idan wancen mutum ya mutu a wannan halin da yake bai mutu ba
kana addinina".Saboda haka ya kamata mutum ya hankali ta yadda ba duk yadda ya
ga dama ba ne zai gabatar da salla, ya kamata mutum ya yi kokari ya gabatar da
salla kamar yadda ya kamata.wato ya kasance yana salla tare da tunanin Allah
madaukaki kuma kamar yadda Allah ya umurta a yi sallar.Wato mutum ya fahimci da
wa ya ke ganawa,Sannan ya san cewa yana gaban wanda yake shi ne Allah mai girma
da daukaka wanda komi yake a hannunsa.Saboda haka idan mutum ya kasance kamar
haka yayin salla,Mutum zai manta da kansa ba wani abu da yake tunani sai Allah
Madaukai,Kamar yadda aka cire kibiya daga jikin Imama Ali a.s. yayin da yake
salla ba tare da ya sanya abin da ake yi ba.
Haka nan dole ne mai salla ya rik a tuba ga Allah wato ya kaurace wa
dukkan abin da zai hana karbar sallarsa,kamar hassada yi da mutane karya da
makamantansu.haka nan mutu ya lizimci yin sauran abubuwan da Allah madaukaki ya
wajab a kansa kamar bayar da zakka da khumusi da makamantansu.Wato a takaice mai
salla dole ne ya kauce wa duk abin yake Allah madaukaki ba ya si bayinsa su
aikata shi, sannan ya riki dukkan abin da Allah ya hori bayinsa da su rika
aikatawa.Sannan mutu ya kaurace wa dukan abin da suke rage ladar salla wato
kasan ce cikin tsabata,haka nan mutum ya kaurace wa kallon sama yayin da yake
cikin salla.haka nana mutum ya riki abubuwan da suke kara ladar salla, kamar
sanya zoben Akik da sanya tufafi masu tsabta da sanya turare, haka nan mutum ya
lizimci tsabtace bakinsa da dai makamantansu.
|