Sallolin Wajibi
Salolin wajibi guda shida ne:
Na daya:Sallolin yau da kullum.
Na biyu:Sallar aya(sallolin da ake yayin girgizar kasa da lokuttan da wani
abu dai ya faru na ban tsoro)
Na uku:Sallar janaíza.
Na hudu:Sallar dawafin wajibi yayin aikin hajjin(kamar lokacin dawafin umurar
Tmattu da umura kawai ba tare da aikin hajji ba,da kuma sallar dawafin Nisaa)
NA biyar sallar ramuwa akan babban da yayin da mahaifinsa ya mutu ana binsa
sallar da bai yi ba.
Na shida:Sallar da ta wajaba akan mutum sakamkon kudi da ya masa don ya rama
wa wani mutum salla,ko kuma ya yi alwakawali zai aiwatar da wata salla sai ta
wajaba akansa.
Sallolin wajibi na yau da kullum:
Sallolin wajibi na yau da kulum guda biyar ne,sune kamar haka,Azahar rakaá
hudu.la'ásar raka'a hudu,magrib raka'a uku, isha, da asubah raka'a biyu.
Mas'ala ta 726: Dole ne a yi sallolin da suke da raka'a hudu rakaá
biyu yayin tafiya.(kasr)tare da wasu sharudda da zamu fada a nan gaba.
|