Lokacin sallar Azahar da laásar:
Masála ta 727:Likacin sallar zuhr da asar shi ne lokacin da rana da ta
karya daga tsakiya, saboda haka idan rana ta karya lokacin sallar azahar ya yi
bayan an gama sallar zuhr daga lokacin sallar asr zai fara.
Masála ta 728:Ana ioya san ya wani icce don ya nuna inwa idan ta
karkata wato alamar rana ta karya,wannan iccen ana kiransa Shakis wato mai
bayyana lokaci.
Masála ta 729:Sallar Zuhr da Asr dukkan kowane yana da lokaci na
musamman sannan kuma suna da lokacinn da suka hadu da juna,wato lokacin da bai
kebanta ba da daya daga cikinsu.Lokacin da ya kebanta da sallar Zuhr shi ne
fdaga farkon karyawar rana zuwa iya lokacin da za a iya yi salla rakaá hudu.Amma
lokacin da ya kebanci Sallar Asr shi ne idan lokacin ya rage dai-dai wanda za a
iya yin salla rakaá hudu kafin faduwar rana.Amma tsakanin lokacin da ya kebanci
Zuhrn da lokacin da ya kebanci Asr wannan lokacin ana kiransa mushtarak wato
lkacin Zuhr da Asr ne bai kebanci daya daga cikinsu ba.Saboda haka idan mutm ya
yi sallar Zuhr a maimakon Asr tare da mantuwa a cikin wannan lokacin anan
sallarsa ta inganta.
Masála ta 730:Idan mutum ya manta ya yi sallar Asr kafin ya yi sallar
Zuhr,amma yana cikin sallar sai ya tuna a she bai yi sallar Zuhr ba ya fara
Asr,Idan lokacin ya kasance wanda bai kebanta da wata sallar ba ne wato a
tsakanin lokacin da ya kebanci Zuhr da Asr ne, anan sai ya maida niyyarsa ta
salla Zuhr wato ya yi niyyar cewa sallar da ya yi tun daga farko da nan gaba
sallar Zuhr ce, bayan ya gama sallar sai ya yi sallar Asr.Amma idan ya kasance a
cikin lokacin da ya kebanci sallar Zuhr ne, anan ihtiyat wajib shu ne ya maida
niyyarsa zuwa sallar Zuhr sannan bayan ya gama sallar,sai ya sake yin sallar
daga farko.
Masálata 731:Sallar jumuá rakaá biyu ce,saboda haka a ranar Jumuá za a
yi sallar Jumuá ne maimaikon sallar Zuhr.Sallar jumuá a zamanin manzom Imam
naíbin musamman na Imam a.s. tana zama wajibi aini,wato ta wajaba a yi ta ba za
a iya yin sallar Zuhr ba maimaikon Jumuá sai bisa wata lalura.Amma daga lokacin
gaiba kubra sallar jumuá ba wajiba aini ba ce wato kana da damar ka zabi daya
daga cikin sallar Zuhr ki Jumuá,amma idan akwai hukumar musulunci ta adalci anan
abin da ya fi shi ne mutum ya yi sallar jumuá din matukar ana yin sallar jumuá.
Masála ta 732:Ihtiyat wajib shine kada a jinkirta sallar jimuá daga
farkon lokacin sallar Zuhr,saboda haka idan aka jinkirta sallar daga lokacin
sallar Zuhr anan abin da ya fi shi ne a yi sallar Zuhr maimaikon Jumuá din.
Masála ta 733:kamar yadda aka yi bayani kowace salla tana da lokacin
da ya klebance ta da kuma lokacin da suka hada da watanta,kamar tsakanin sallar
Zuhr da asr kowace tana da lokacinta na musamman wato Zuhr daga farkon lokaci
zuwa kimanin tsawon lokacin da za a iya yi salla rakaá hudu,haka nan Asr idan
lokacin da ya rage zuwa faduwar rana wanda za a iya yin salla rakaá hudu ne
kawai,to wannan lokacin ya kenbanci As kawai.haka nan daga lokaci da rana ta
fadi (lokacin sallar Magrib) Zuwa tsawon loakci da za a iya yin salla rakaá uku
wannan lokacin ya kebanci sallar magrib, haka nan idan lokaci ya rage
kawai wanda za a iya yin salla rakaá hudu zuwa tsakiyar dare. Wannan lokacin ya
kebanci sallar Isha.Saboda haka idan mutum ya yi sallarAsr a lokacin da ya
kebanci sallar Zuhr kuma da gangan,ko kuma ya yi sallar magrib a loacin da ya
kebanci Isha ko kishiyar hakan,Anna sallar mutum ta baci.Amma idan zai yi sallar
ramuwa ne kamar zai rama sallar Zuhr a lokacin da ya kebanci lokacin wata
salla anan sallarsa ta inganta.
|