|
Lokacin sallar Magrib da Isha
Masála ta 734:Lkacin sallar magrib shi ne lkacin da rana ta fadi wani
ja da yake bayyana a gushe daga bisa saitin kan mutum wannan lokacimn
lokacin sallar Magrib ne.
Masála ta 735:Kowace daya daga sallar Magrib da isha suna da
lokacin da ya kebvanci kowace daya daga cikinsu, sannan kuma kowace daya
daga ciki tana da lokacin da ya kebance ta.Saboda haka lokacin sallar magrib yan
farawa ne daga farkon lokacin sallar magarib din kamar yadda muka fada a
sama,zuwa lokacin da za a iya yin salla rakaá uku,Saboda haka idan mutum ya
kasance matafiyi sannan sai ya yi sallar Isha a cike a wannan lokacin da
ya kebanci sallar Magarib a cikin mantuwa, anan sallarsa ta ba ci.Amma
lokacin da ya kebanci sallar Isha shi ne, ya zuwa lokacin da ya rage kawai ana
iya yi salla rakaá hudu zuwa ysakiyar dare.Saboda haka idan ya kasance mutum ya
uwa wannan lokacin bai yi sallar magrib ba anan dole ne ya fara yin sallar isha
Sannan ya yi magrin din ,domin kuwa wannan lokacin ya kebanci sallar Isha
ne.Amma tsakanin lokacin da ya kebanci sallar Magrib da na Isha wannan
lokacin sub hadu akansa wato bai kebanci wata daga cikin ba. Saboda haka idan
mutum sakamakon mantuwa ya yi sallar isha kafin ya yi sallar magrib,sai ya
fahimta bayan ya gama, sallarsa ta inganta, sai ya yi sallar magrib bayan ya
gama din.
Mas'ala ta 736:Lokacin da ya kebanci kowace salla wanda muka ambata a
masála da ta gabata,ya banbanta ga mutane,Saboda haka idan daga farkon sallar
Zuhr lokacin da za a iya yin sallar rakaá biyu ya wuce, anan lokacin da ya
kebanci sallar Zuhr ga matafiyi ya wuce, amma ga wanda ya ke zaune a gida wati
wanda ba matafiyi ba anan sai idan loakcin da za a iya yin salla rakaá hudu ya
wuce sannan lokacin Zuhr ya wuce.Hak nan abin yake ga sauran sallolin.
Masála ta 737:Idan kafin mutu ya yi sallar Magrib sai ya cigaba da
sallar Isha sakamakon mantuwa,yana cikin sallar sai ya tuna cewa bai yi sallar
magrib ba kuma ga shi ya fara sallar isha,Idan ya kasance rakaóin da ya yi a
ciin lokacin da bai kebanci Magrin ba ne,sannan kuma bai kai ga yin rukuú
na hudu ba, anan sai ya maida niyyar sallarsa zuwa ta magrib,sai ya zauna
ya sallame sannan ya yi maida ta Isha,Amma idan ya kasance ciin lokacin da ya
kebanci sallar magrib ne,anan ijhtiyat wajib sallarsa ta baci dole ne ya sake
wata.
Amma Idan mtum ya riga ya yi rukuú na hudu anan sai ya gama
sallar Isha din,sannan sai ya yi sallar Magrib, amma fa idan ba cikin lokacin da
ya kebanci magrib ba ne,Idan kuwa cikin lokaci da ya kebanci Magrib ne anan
ihtiyat wajib sallarsa ta baci.
Masála ta 738:Karshen lokacin sallar Isha shi ne zuwa tsakiyar
dare,Ihtiyat wajib shi ne mutum ya lissafa lokacin da Magrib da isha suka hadu
shi ne daga tsakiyar dare zuwa lokacin sallar Asubah.
Masála ta 739:Idan mtum bai yi sallar Magrib ba har zuwa tsakiyar dare
sakamokn wani uziri,anan sai ya yi sallar kafin kiran sallar asubah ba tare da
niyyar ramuwa ba ko kuma zai yi ta cikin lokaci.
Lokacin sallar Asubah:
Masála ta 740:Kusan kiran sallar Asubah wani haske zai taso daga gabas
ya yo sama, wanna hasken ana kiran alfijir na farko,lokacin da wannan haske ya
yo sam kuma ya mamaye sama, anan kiran wannn haske alfijir na biyu,, kuma shi ne
farkon sallar Asubah,sannan karshen lokacin sallar Asubah shi ne lokacin da ran
ta fito.
|