|
Hukunce-hukunce lokuttan salla:
Mas'ala ta 741:Lokacin da mutum zai iya fara salla shi ne
lokacin da ya tabbatar da cewa lokacin salla ya isa,wannan kuwa yana samuwa ta
hanyoyi guda uku,kodai mutum da kansa ya tabbatar da hakan ko kuwa adalai guda
biyu su tabbatar masa da hakan,wato kamar su badar da shedar cewa sunga inwarsu
ta karkata ko ta kara tsawo,wato lokacin da rana ta karya, wanda ya nuna
lokacin sallar Zuhr ya isa.Ko kuma ta hanyar kiran salla daga mutumin da ake da
tabbas cewa ya san lokacin salla din.
Mas'ala ta 742:Mutumin da ba ya gani ko wanda yake cikin kurkuku
ta yadda ba zai iya sanin lokacin salla ya isa ba da kansa,anan bai kamata
ba ya fara salla ba har sai ya samu tabbas akan cewa lokacin sallar ya
isa.Amma idan ya kasance sakamakon wani dalili kamar giza-gizai a sama ko
makamancinsa ya hana mutum ya samu yakini akan shigar lokacin salla,anan idan
mutum ya yi tsammanin shigar lokacin yana iya yin salla, ba sai ya samu
tabbas ba akan hakan.
Mas'ala ta 743:Idan mutum ya samu tabbas akan cewa lokacin salla ya
isa,amma sai bayan ya fara sallar ya fahimci cewa lallai lokacin sallar
bai isa ba,anan wannan sallar ta baci.Haka nan idan sai da ya gama sallar
ya fahimci cewa lallai ya yi sallar ne kafin lokacin anan ma sallarsa ta
baci,saboda haka dole ya sake sallar.Amma idan yana cikin sallar ya fahimci cewa
lallai lokacin da yake sallar lokacin sallar ya shigo,ko kuma bayan ya gama
sallar ya fahimci cewa a lokacin da yake sallar lokacin sallar ya shigo anan
sallarsa ta inganta kuma ba sai ya sake wata sallar ba.
Mas'ala ta 744:Idan mutu sakamkon mantuwa ya shagala da cewa lallai
dole ne ya samu yakini akan shigar lokacin kafin ya fara salla,saboda haka sai
da ya gama sallar sai ya fahimci cewa ai ya yi wannan sallar tasa ne a ciikin
lokaci,anan sallarsa ta inganta.Amma idan bayan ya gama sallar sai ya fahimci
cewa ai ya yi wannan salla ne dukkanta kafin lokaci ya shiga, ko kuma ya kasa
gane cewa shin ya yi wannan salla ne cikin lokaci ko kuwa kafin lokaci ne,anan
sallarsa ta baci.Koda yake idan bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa
lallai lokacin da yana cikin sallar lokacin sallar ya shigo anan ihtiyat wajib
shi ne ya sake wannan sallar shi ya fi.
Mas'ala ta 745:Idan mutum ya samu yakini akan cewa lokacin salla ya
shiga sannan ya fara salla, sai yana cikin sallar ya samu shakka akan cewa
shin lokacin da ya fara salla shin lokaci ya shiga ko kuwa kafin lokaci ya
fara sallar, anan sallarsa ta baci.Idan mutum yana da yakini akan cewa ya salla
ne a cikin lokaci amma yana shakka akan cewa shin raka'o'in da ya yi baya cikin
lokaci ne ko kuwa kafin lokaci ne, anan sallarsa ta inganta.
Mas'ala ta 746:Idan ya zamana lokacin salla ba shi da yawa ta yadda
mutum ba zai iya yin wasu abubuwa ba na mustahabbi,idan kuwa ya yi su to zai
janyo mutum ya yi wani bangare daga cikin salla a wajen lokacin
sallar,anan sai mutum ya bar abubuwan mustahabbin don ya aiwatar da dukkan
sallar a cikin lokaci.Misali idan mutum sakamkon yin Kunut zai sanya ya yi
wani bangare daga cikin sallarsa a wajen lokaci,anan bai kamata ya
yi kunut din,amma idan ya yi bai yi sabo ba kuma sallarsa ta inganta.
Mas'alata 747:Wanda yake da lokacin yin raka'a daya ta salla kafin
lokaci ya isa,yana iya yin sallar da niyyar yin ta a cikin lokaci,wato ba niyyar
ramuwa ba,Amma fa bai kamata ba mutum da gangan ya jinkirta salla har ya zuwa
wannan lokacin.
Mas'ala ta 748:Wanda ya ke a gida wato ba matafiyi ba, idan yana da
lokacin da zai yi salla raka'a biyar kafin rana ta fadi,anan dole ne ya yi
sallar Zuhr da Asr a lokacin,amma idan lokacin da yake da shi ba zai isa ba ya
yi raka'a biyar,anan dole ne ya yi Asr a wannan lokacin,daga baya sai ya
yi sallar Zuhr a matsayin ramuwa.Haka nan idan ya zamana lokacin da mutum
ya ke da shi zuwa rabin dare zai isa ne kawai ya yi salla raka'a hudu,anan
dole ne ya yi sallar magrib da Isha a lokacin,amma idan lokacin ba zai sa ba ya
yi raka'a hudu,anan wajibi ne ya gabatar da sallar Isha,daga baya sai ya yi
sallar Magrib a matsayin ramuwa.Ihtiyat wajib anan yayin da mutum zai yi sallar
Magrib sai ya yi niyyar yinta a cikin lokaci da kuma niyyar ramuwa baki
daya.
Mas'ala ta 749:Matafiyi idan yana da lokacin da zai yi salla raka'a
uku kafin rana ta fadi,anan dole ne ya yi Zuhr da Asr a lokacin,amma idan
lokacin da yake da shi ba zai isa ba ya yi raka'a uku,anan dole ya fara yin Asr
sannan daga baya ya yi Zuhr a matsayin ramuwa,Haka nan idan ya zamana yana da
lokacin da zai yi raka'a hudu kafin tsakiyar dare,anan dole ne ya yi sallar
Magrib da Isha baki daya,amma idan lokacin ba zai isa ba ya yi raka'a hudu,anan
sai ya yi sallar Isha sannan ya yi ta Magrib da niyyar cikin lokaci da kuma
niyyar ramuwa baki daya.
Mas'ala ta 450:Mustahabbi ne mutum ya gabatar da sallar a farkon
lokaci,an karfafa yin hakan kwarai da gaske don haka duk lokacin da mutum yayi
salla idan ya fi kusa da farko lokaci ya fi,sai ya idan ya zamana ya jinkirta ne
sakamakon wani dalili kamar yana jira ne ya yi sallar cikin jam'i.
Mas'ala ta 451:Duk lokacin da mutu yake da wani uziri,sakamkon hakan
idan yana so ya yi salla a farkon lokaci sai dai idan ya yi ta tare da
taimama,duk da yana tsammanin cewa idan ya jinkirta uzirin zai iya gushewa,anan
yana iya yin sallarsa a farkon lokacin.Amma idan ya zaman sakamkon tufafinsa
suna da najasa ne ba zai ya yin salla ba a farkon lokaci kuma yana tsammanin
cewa idan ya jinkirta zuwa karshen lokacin wannan matsala zata kau,anan sai ya
jinkirta har zuwa karshen lokacin sannan ya yi sallar.Amma anan ba dole ba ne
ya jira har zuwa lokaci da ya zamana kawai ayyukan wajibi na salla ne zai
ya yi kafin lokacin ya fita,saboda haka idan ya ga cewa lokacin da ya rage zai
iya yin sauran abubuwan na mustahabbai,anan yana iya yin sallarsa da najasar ba
wani abu.
Mas'ala ta 752:Wanda bai san hukunce-hukunce salla ba kamar abin da ya
shafi hukuncin shakka da mantuwa,sannan kuma yana tsammanin cewa lallai daya
daga cikin wadan anan suna iya faruwa a lokacin da yake cikin salla,anan dole ne
ya jinkirta domin ya koyi wadan nan hukuce-hukunce.Amma idan yana da tabbas cewa
ba zai samu daya daga cikin wadan nan abubuwan ba yayin da yake salla,anan wato
zai gama sallar ba tare da wata matsala ba,anan yana iya sallarsa a farkon
lokaci,ba dole ba ne ya jinkirta sallar domin ya koyi wadan nan
hukunce-hukunce,amma idan yana cikin salla sai ya gamu da daya daga cikin
abubuwan da bai san hukincinsu ba, anan yana iya yin aiki da daya daga cikin
abubuwan da ake tsamani da niyyar idan ya gama zai je ya tambaya, ta yadda idan
sallarsa ta ba ci sai ya sake.
Mas'ala ta 753:Idan mai bin mutum bashi ya zo yana son kudinsa, ga shi
kuma lokacin salla ya isa,anan idan har lokacin sallar yana da yawa ta yadda zai
je ya biya bashin sannan ya yi salla ba tare da lokacin sallar ya fita ba,anan
dole ne farko ya biya bashin sannan ya zo ya yi sallar.Haka nan idan wani abu ya
faru wanda kuma ana bukatar a gabatar da shi a cikin sauri,misali kamar idan
mutum ya ga najasa a cikin masallaci,anan dole ne farko ya fara tsarakake
masallacin sannan ya yi sallar,amma idan da mutum zai fara yin sallar, a nan ya
yi sabo amma sallarsa ta inganta.
|