Sallolin da dole ne a yi su a jere:
Mas'ala ta 754:Mutum dole ya fara yi sallar Zuhr sannan ya yi Asr,haka
nan dole ya fara yin Sallar Magrib sannan ya yi Isha.Da mutum zai yi sabanin
haka kuma da gangan,a nan sallarsa ta baci.
Mas'ala ta 755:Idan da mutum zai yi niyyar sallar Zuhr,sai yana cikin
sallar ya tuna ashe ya riga ya yi sallar Zuhr ta Asr a6ya kamata ya yi,a nan ba
zai maida wannan niyyar ba ta Asr sai da ya katse sallar ya yi niyya Asr tun
daga Farko.Haka nana yayin sallar Magrib da isha,idan da zai yi niyyar sallar
Magrib sai ya tuna cewa ya yi Magrib ba zai maida wannan niyyar bat a
Isha, sai dai ya yanke sallar ya sake daga farko.
Mas'ala ta 756:Idan da mutum yana cikin sallar Asr sai ya samu yakini
akan ce bai yi sallar Zuhr ba a nan sai ya maida niyyar sallarsa ta Zuhr,sai
kuma kafin y agama sallar sai tuna cewa a she ya yi Zuhr,Anan sai ya maida
niyyarsa zuwa sallar Asr,amma idan ya riga ya yi wani yanki mai yawa daga cikin
sallar Zuhr din kamar ian ya yi ruku'u wanda yake rukuni ne daga cikin salla,a
nan sai dai ya gama sallar sannan ya sake yin ta Asr din daga farko.Amma idan
bai kai ga yin wani rukuni ba,a nan sai ya maida niyyarsa ta Asr kuma
sallarsa ta inganta.Duk da yake dai ihtiyat mustahab shi ne ya sake yin
sallar Asr din shi ya fi.
Mas'ala ta 757:Ian mutum yana cikin sallar Asr sai ya yi shakka akan
cewa shin ya yi sallar Zuhe ko bai yi ba,a nan dole ne ya mayar da niyyar
sallarsa zuwa Zuhr,Amma idan ya zamana lokaci ya kure ta yadda da ya gama
wannan sallar sai lokacin magrib ya yi,annan dole ne ya cigaba da wannan sallar
Asr din bayan ya gama sai ya rama ta Zuhr din.
Mas'ala ta 758: Idan mutum yana cikin sallar Isha kafin ya yi tuku'u
na hudu sai ya yi shakka a kan cewa shin ya yi sallar magrib ko bai yi ba,
sannan kuma lokaci ya kure zuwa tsakiyar dare anan sai ya cigaba da sallarsa
bayan a gama sai rama sallar magrib din.Amma idan akwai lokaci ta yadda zai I
sallarMAgrib sannan ya yi ta Isha,a nan sai yamaida niyyar sallarsa zuwa ta
Magrib bayan ya gama sannan ya yi ta siha.
Mas'ala ta 759:Idan mutum yanacikin sallar Isha kafin ya yi ruku'u na
hudu sai ya yi shakka akan cewa shin ya yi sallar Magrib ko bai yi ba,a nan sai
ya cigaba da sallar Isha dinsa bayan y agama sannan ya yi ta Magrib.Idan kuwa
wannan shakka ta faru ne a lokacin da yake ya kebanta da nasallar isha ne,wato
lokaci ya kure zuwa tsakiyar dare, a nan dole ne ya rama sallar Magrib.
Mas'ala ta 760:Idan mutum ya sake yin sallar day a riga ya yi
ihtiyat,sannan yana cikin sallar sai ya tuna cewa sallar day a kamata ya yi
kafin wannan bai yi tab a,anan ba zai iya maida wannan niyyar ba zuwa waccan
sallar.Misali lokacin da yake cikin sallar Asrta ihtiyat,sai ya tuna cewa bai yi
sallar Zuhr ba,a nan ba zai iaymaida niyyar wannan sallar ba zuwa sallar Zuhr.
Mas'ala ta 761:BAi halitta ba a mayar da niyyar sallar ramuwa zuwa
wadda take a cikin lokacinta,ko kuma a mayar da niyyar sallar mustahabbi zuwa
sallar wajibi.
Mas'ala ta 762:Ihtiyat wajib shi ne idan ana bin mutum wata salla
kafin ya yi wata sallar ta gaba ya rama wannan wadda ake bin sa.Idan da mutum
zai cigaba da sallar da take cikin lkaci sai ya tuna cewa ana binsa wata salla
ta wannan ranar,ihtiyat wajib shi ne ya mayar da niyyar wannan sallar zuwa
sallar day a kamata ya rama.Amma idan da mutum ya fara salla sai ya tuna cewa
ana binsa wata salla amma bata wanna ranar ba,anan mustahabbi ne ya mayar da
niyyar wannan sallar zuwa waccan wadda ake bin sa.Amma abubuwan da mua fadaa
sama sai idan lokaci bai kure ba, ta yadda zai iaya gama wannan sallar sannan ya
yi ta lokacin ba tare da lokacinta ya fita ba, haka idan ya riga ya wuce wurin
da zai iyamaida niyyarsa kamar idan ya riga ya yi ruku'u na uku sannan sai ya
tuna abinsa sallar isha ko ya yi ruku'u na hudu sai ya tuna abinsa sallar
magrib a nan sai ya gama sallar sannan ya rama waccan wadda ake binsa.
|