Sallolin mustahabbi:
Mas'ala ta 764:Sallolin mustahabbi suna da yawa,kuma ana kiransu da
sallolin nafila.A cikin wadan nan salloili na mustahabbi ko na nafila, an
karfafa yin sallolin mustahabbi na dare da rana,wadan nan salloli kuwa ban da
ranar Juma'a raka'a talatin da hudu ne,Wato raka'a Takwas na sallar Zuhr,Raka'a
takwas na sallar Asr,sai Raka'a hudu na sallar Magrib,sannan raka'a biyu na
sallar Isha,sannan raka'a sha daya a matsayin sallar dare,sannan sai raka'a biyu
na sallar asuba, Amma raka'a biyu na sallar Isha ana yinsu ne a zaune suna
matsayin raka'a daya ne.Amma ranar jumu'a ana kara raka'a hudu akan nafilar
sallar Zuhr da Asr.
Mas'ala ta 764:Raka'a takwas daga cikin raka'a sha daya na sallar dare
za a yi su ne,da niyyar sallar nafilar dare sannan raka'a biyu a matsayin sallar
Shafa'I sai raka'a daya a matsayin sallar witri.Sannan an cikakken bayani a kan
yadda ake yin sallolin nafila a cikin littafan addu'asai duba wadab nan littafai
don karin bayani.
Mas'ala ta 765:Na yin sallaolin nafila daga zaune,amma abin da yafi
shi ne a lissafa raka'a biyu da a ka yi daga zaune a matsayin raka'a daya,Saboda
haka wanda yae so aya yi sallaolin nafilar sallar Zuhr daga zaune maimakon
raka'a takwas zai yi raka'a sha shida kenan.Idan kuwa mutum yana son ya yi
sallar Wutiri daga zaune sai ya yi salla mai raka'a daya sau biyu daga zaune.
Mas'ala ta 766:Nafilar sallar Zuhr da asr tana faduwa yayin
tafiya,saboda haka bai kamata ba a yi su yayin tafiya,amma nafilar sallar Isha
ya kamata a yi su koda mutum yana a halin tafiya.
Lokuttan sallolin nafiya na yau da kullum:
Mas'ala ta 767:Nafilar sallar Zuhr a na yinta ne kafin sallar Zuhr
sboda haka lokacinta yana farwa yayin sallar zuhr ta isa har ya zuwa lokacin da
inwar mutum zata bayyana.
Mas'ala ta 768:Nafilar Asr itama kafin sallar Asr din za a gabatar da
ita,wato lokacin ta daga lokacin da inwar mutum zata bayya bayan sallar Zuhr
lkacin da tsawon inwar ya kai hudu bisa bakwau na tsawon mutumin,amma idan mtum
yana so ya yi nafilar bayan sallar ihtiyat wajib shi ne mutum ya yi nafilar Zuhr
bayan sallar Zuhr sannan ta Asr Bayan sallar Asr.Sannan ihtiyat wajib kada ya yi
niyyar ramuwa ko niyyar zai yi su ne cikin lokaci.
Mas'ala ta 769:Lkacin Nafilar sallar magrib kuwa bayan an gabatar da
sallar magrib din ne,sannan yana cigaba har ya zuwa lokacin da jan nan zai
bace wanda yake bayyana a yamma bayan faduwar rana.
Mas'ala ta 770:Amma lokacin nafilar Sallar Isha,har ya zuwa tsakiyar
dare.Duk da yake abin da ya fi shi ne a gabatar da ita bayan gama sallar isha
din.
Mas'ala ta 771:Ana yi nafilar sallar Asuba kuwa kafin sallar Asuba
din,sannan lokacinta yana farawa daga bayan tsakiyar dareda misalin lokacin da
za a iya yin sallar dare raka'a sha daya, amma ihtiyat mustahab shi ne,an yi
nafilar sallar Asuba bayan bullowar Alfijir na farko,wato a kauce ma hakan kafin
bullowar alfijir na farko.
Mas'ala ta 772:Lokacin sallar dare yana farawa daga tsakiyar dare, har
zuwa lokacin sallar Asuba.
Mas'ala ta 773:Matafiyi ko kuma wanda yin sallar dare zaya yi masawuya
idan ya kasan ce sai bayan tskiyar dare, ko kuma yana jin tsoron kada ya kasa
farkawa,yana iya yi sallarsa farkon dare .
|