Sallar Gufaila:
Mas'ala ta 774: daya daga cikin sallolin mustahabbi ita ce sallar
Gufaila,wannan sallae kuwa a na yinta tsakanin sallar magarib da Isha,Lokacin
wannan salla si ne bayan gama sallar Magrib har ya zuwa lokacin da jan rana na
yamma zai bace,sannan wannan salla raka'a biyu ce,a raka'a ta farko bayan
karanta fatiha ana karanta wannan aya maimakon sura, kamar haka:
«وَذَاالنُّونِ اِذْ ذَهَبَ
مُغاضِباً فَظَنَّ اَنْ لَنْ نَقْدِرَ عَلَيْهِ فَنَادَى فِى الظُّلُماتِ اَنْ لا
اِلهَ اِلاّ اَنْتَ سُبْحانَكَ اِنّى كُنتُ مِنَ الظّالِمينَ فَاسْتَجَبْنا لَهُ
وَنَجَّيْناهُ مِنَ الغَمِّوَكَذلِكَ نُنْجِى الْمُؤمِنينَ».
A raka ta biyu kuwa bayan an karanta fatiha ana karanta wannan aya maiamakon
sura kama haka:
«وَعِنْدَهُ مَفاتِحُ الْغَيْبِ لا
يَعلَمُها اِلاّ هُوَ وَيَعْلَمُ ما فِى البَرِّ وَالْبَحْرِ وَما تَسْقُطُ مِنْ
وَرَقة اِلاّ يَعْلَمُها وَلا حَبَّة فىِ ظُلُماتِ الاَرْضِ وَلا رَطْب وَلا يابس
اِلاّ فِي كتاب مُبين».
Sannan ana karanata wannan addu'ar a yayin Kunut kamar haka:
«اَللّهُمَّ اِنّى اَسأَلُكَ بِمَفاتِحِ الغَيْبِ
الَّتى لا يَعْلَمُها اِلاّ اَنْتَ اَنْ تُصَلِىّ عَلى مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد
وَاَنْ تَفْعَلَ بى كذا وكذا.....
Sai mutum ya fadi bukatarsa idan ya isa wajen da da sanya kaza wa kaza.
«اَللّهُمَّ اَنْتَ وَلِىُّ نِعْمَتى وَالْقادِرُ
عَلى طَلِبَتى تَعْلَمُ حاجَتى فَأساَلُكَ بِحَقِّ مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد
عَلَيْهِ وَعَلَيْهِمُ السَّلامُ لَمَّا قَضَيْتَها لى».
Hukuncin alkibla:
Mas'ala ta 775:Dakin Ka'aba wanda yake a garin makka shi ne alkibala
kuma wanda ake fukanta yayin da matum yake salla.Saboda haka wanda yake nesa da
shi idan ya fuskanci wajensa ta yadda za'a iya cewa ya kallai wajen ka'aba ya
wadatar.Haka nan sauran wasu ayyukan kamar yanka dabba, dole ne a kallai kiblar
yayin aiwatar da shi.
Mas'ala ta 776:Mutum zai yi sallar wajibi daga tsaye,dole ya
fuskanci kibla ta yadda za a ce yana kallon alkiba,amma ba wajibimba ne
guyawunsa da "yan yaztsunsa su zama suna kallon kiblar.
Mas'ala ta 777: Mutum da zai yi salla daga zaune sannan kuma ba zai
iaya zama ba kamar yadda kowa yake zama,ta yadda idan zai zauna sai dai ya kafa
kafafunsa a kasa, anan dole ne ya kasance kirjinsa,fuskarsa da cikinsa
suna kallon kibla yayin da yake yin salla.Saboda haka ba dole ba ne kwaurin
kafarsa ya zama yana kallom kiblar.
Mas'ala ta 778: Mutumin da kuwa ba zai iya yin salla ba daga zaune,a
nan sai ya kwanta bisa kafadar dama ta yadda fuskarsa zata kalli kibla yayin da
yake salla.Idan kuwa hakan ba zai yiwu ba yana iya kwantar kafadarsa ta hagu ta
yadda gabansa zai kalli kiblar,Idan kuwa hakanma ba zai yiwu ba sai ya kwanta
rigingine ta yadda tafin kafarsa zai kalli kiblar.
Mas'ala ta 779:Idan mutum zai yi sallar ihtiyat ko ramuwar tahiya ko
sujjada,dole ya zama yana kallon kibla,haka nana yayin sujjadar Sahawu.
Mas'ala ta 780:Idan mtutm yana bisa abin hawa kamar mota,jirgi ko
jirgin ruwa, yana iya sallar mustahhabi a wannan lokacin ba tare da ya kalli
kibla.
Mas'ala ta 781:Mutumin da yake so ya yi salla dole ne ya yi kokari ya
gano kibla, idan mutum yana so ya samu tabbas akan hakan yana iya samu adalai
guda biyu su tabbatar masa da hakan wato wadan da zasu ba da shaidar ne bisa
la'akari da abin da suka lura da shi na cewa lallai nan ne kiblar, ko kuma ta
hanayr mutumim da yake da ilimin hakan,wato masanin hakan ta hanyar ka'idar
ilimi.Idan kuwa hakan ba ta samu ba,sai mutum ya yi mafani da abin yake zaton
hakadin ne, ta hanyar masallatan musulmi ko makanartasu, ta yadda mutum zai samu
natsuwa a kan hakan.koda kuwa ta hanyar Fasiki ko kafiri idan har sun amfani da
ka'idar ilimi uska fadawa mutum cewa nan ne kibla kuma mutum yana ganin haka ne
koda bai samu tabbas ba, wannan ya wadatar.
Mas'ala ta 782:Mutum da yake tsammanin kibla idan har yana iya
samuntsammanin da yafi wannan karfi,anan ba zai yi mafani da wannan tsammanin
nasa ba,misali idan bako ya samu tsammanin cewa nana= ne kibla ta hanyar fadar
mai masaukinsa,idan yana wata hanyar da zai kara samun nastuwar da fi wanna
kamar ta hanyar yin amafani da na'urar gane kibla,anan dole ne ya yi mafani da
ita domin hakan,bai kamata ya dogara da maganar mai masaukinsa ba.
Mas'ala ta 783:Na'urar da ake amfani a su wajen gano kibla idan har
lafiya lau suke suna daya daga cikin hanyar da ake bi wajen gane kibla,saboda
haka dogara da abin da suka nuna yafi sauran hanyoyin da za a iya bi wajen gano
kiblar.
Mas'ala ta 784:Idan mutum ba sai inda kibala take ba,yana gano hakan
ta hanyar duba inda masallatai suke kallo ko kuma ta hanayr Makabartar
musulmi,amma idan mutum ya gano kibla sabanin inda masallatai suke nunawa,
misali idan yayi amfani da na'urar gano kibla,anan ihtiyat wajib shi ne yayi
amfani da abin wannan na'urara ta nunamasa kda kuwa ya sabawa Masallatan.Amma
idan mutum samu tsammanin cewa musulmi da suke zaune a wannan wuri ba su taka
tsantsan ba wajen gano kibla yayin da suke gina mallatansuda makabartunsu
ba,anan mutumyana iya yin salla fuskar da ya ga ya fi natsuwa akan cewa ita ce
kibla.
Mas'ala ta 785:Idan ba shi hanyar da zai yi ya gano kibla ko kuma ya
yi kokarin ya gano amma ya kasa bada karfi waje guda,a nan idan akwai lokacin
sai ya yi sallar har sau hudu wato ya yi salla hudu kowa ne bangare,amma
idan ba shi da cikkaken lokacin da zai yi salla guda hudu anan sai ya yi wadn da
suka sawaka,wato idan kawai salla daya zai iya yi kowane bangare sai ya yi
dayan,ta yadda dai zamu tabbas a kan cewa cikin wadan nan sallolin tabbas ya yi
wata daga ciki ta fuskar alkibla.
Mas'ala ta 786:Idan mutum ya samu tabbas a kan cewa lallai kibla tana
daya daga cikin bangarorin biyu,a nan dole ne mutum ya kalli wadan bangarorin
guda biyu ya yi sallar,ihtiyat mustahab kuwa shi ne ya kalli dukkan bangarorin
guda hudu ya yi sallar.
Mas'ala ta 787:Mutum da ya wajaba ya yi salla ta bangarori fiye
da daya,idan yana so ya yi sallat Zuhr,Asr, Magri da Isha, Abin da ya fi shi ne
ya yi sallar farko ta dukkan fuskokin da suka wajaba ya yi sallar,sannan
ya yi salla ta biyu da haka dai har ya gama.
Mas'ala ta 788:Mutum da ba shi tabbas a ka n kibla idan zai yi wani
abiu wanda kallon alkibla ya wajaba,misali idan zai yakka wata dabba,anan sai ya
yi yankan ta bangaren da yake zaton nan ne kiblar,idan kuwa babu wani bangare da
yake tsammani a nan sai ya kalli duk bangaren da yake so ya inganta.
Mas'ala ta 789:Idan mutum yana zaton wani bangare nan ne kibla sai ya
fara salla,yana cikin salla sai kuma zatonsa a kan kibala ya koma zuwa ga wani
bangaren,a nan dole ne ya juya ya ida sallar ga wannan bangaren na biyu da yake
tsammani nan ne kibla.Amma idan ya zamana raka'o'in da ya riga ya yi sun kasance
bayan kibla ta biyu da yake tsammani ne, ko kuma dama ko hagunta, a nan ihtiyat
wajib shi ne ya sake wannan sallar zuwa kiblar da yake tsammani ta biyu.
Mas'ala ta 790:Idqan mutum ba tare da kula ba ya fara salla,sai bayan
ya gama salla sai ya fahimci cewa ya yi sallar ne yana kalloon kibla,sannan ya
yi sallarsa ne tare niyyar kusanci zuwa ga Ubangiji, a nan sallarsa ta
inganta.Amma idan bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa wajen da ya yi salla
ba kibla ba ce,a nan sallar ta baci kuma dole ya sake ta wajen da kibla
take.Amma a nan Alkibla ana ba wai sai dari bisa dari mutum ya kalli saitin
Ka'aba ba, idan mutum ya kalli wajen da take koda ya dan kauce kadan babu laifi.
Mas'ala ta 791:Idan mutum ya yanka wata dabba sabanin kibla kuma da
ganganci naman wannan dabbar ya haramta,amma idan mutum bai san inda kibla take
ba ko kuma ya manta ko kuma sakamakon wani uziri bai san kiblar ba, idan ya
yanka wata dabba a nan ya halatta a ci namanta.
|