Suturta jiki yayin salla:
Mas'ala ta 792:Dole ne mutum (namiji)
yayin da yake salla koda wani ba ya ganinsa ya rufe al'urarsa guda biyu(wajen
fitsari da kashi)amma abin da ya fi shi ne ya mutum ya rufe tun daga cibiyarsa
zuwa guiwa.
Mas'ala ta 793:Dole ne mace ta rufe
dukkan jikinta yayin salla har da gashin kanta,amma ba dole ba ne ta rufe
fuskarta iya inda ta wankewa yayin alwalla,haka nan tafin hannu zuwa wuyan
hannaye da kuma tafin kafa zuwa wuyan kafar.Amma don mace ta samu yakin cewa
ta rufe dukkan inda ya wajaba ya kamata ta rufe wani abu daga cikin fuskarta
domin ta samu tabbas a kan hakan, ta dan rufe wani bangare daga tafin hannun da
na kafa don samun yakini.
Mas'ala ta 794:Yayin da mutum zai rama
sujjada ko tahiyar da ya manata yayain salla ya wajaba ya rufe jikinsa kamar
lokacin da yana salla,haka nan a wajen rama sujjadar Ba'adi ya kamata mutumya
rufe jikinsa.
Mas'ala ta 795:Ba dole ba ne mace ta
rufe gashin da ba na asali ba wati gashin da ta kara, haka nan adon da ta yi
kamar abin ya shafi "yan hannu ko sarka ko kuma kwalliyar fuska.Amma ya
wajaba ta rufe wannan kwalliyar ga wanda ba muharraminta ba.
Mas'ala ta 796:Idan da gangan mutum
ya bar al'urarsa a bude yayin salla,sallarsa ta baci.Haka nan da mutum zai bar
al'aurarsa a budeyayi salla a kan rishin sani, ihtiyat shi ne ya sake wannan
sallar.
Mas'ala ta 797:Idan mutum yana cikin
salla sai ya fahimci cewa al'aurarsa tana bude ya wajaba ya gaggauta wajen
suturtata.Sannan ihtiyat wajib shi ne ya karasa wannan sallar sannan ya sake
ta.Amma idan mutum bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa lokacin da yake
salla al'aurarsa ta kasance a bude,a nan sallarsa ta inganta.
Mas'ala ta 798:Idan ya zamana tufafin
da mutum yake dashi zai iya rufe al'aurarsa idan yana tsaye amma idan da zai yi
ruku'u ko sujjada al'aurarsa zata iya budewa,Idan mutum ya san yadda zai iya
rufe al'aurar yayain da zata bude sallarsa ta inganta.Amma ihtiyat a nan shi ne
mutum kada ya yi salla da wannan tufafin.
Mas'ala ta 799:Mutum zai iaya rufe
al'aurarasa yayin salla daciyawa ko ganyan itaciya.Amma ihtiyat mustahab shi
ne a lokacin da zai yi mfani da wannan sai idan ya rasa tufafin da zi yi salla.
Mas'ala ta 800:Idan mutum ba ya da
wani abu da zai iya rufe jikinsa ya yin salla sai furen kwalliya, a nan yana
iya yi sallarsa ba tare da wani abu ba(a tsirara).Amma ihtiyat mustahab shi ne
mututm yayi sallar sau biyu wato ya yi tare da wani abu ba a jikinsa sannan ya
rufe al'aurarsa da furen.
Mas'ala ta 801:Idan mutum ba ya da
abin da zai rufe jikinsa yayin salla, idanmutum yana tsammanin zai iya samu,
ihtiyat wajib shi ne mutum ya jinkirta sallar har ya samuabin da zai rufe
jikinsa,Amma idan bai samu ba har zuwa karshen lokaci yana iya sallarsa tare da
kiyaye abin da ya hau kansa kamar yadda a ka yi bayani a baya.
Mas'ala ta 802:Idan zai yi salla
sannan bai samu abin da zai rufe jikinsa ba koda ciyawa ko ganyan
itaciya,sannan ba ya tsammani cewa zai iya samu har zuwa karshen lokacin
salla,idan wani wanda ba muharraminsa ba zai iay ganinsa a nan sai ya yi
sallarsa daga zaune,sannan ya rufe al'aurarsa da cinyoyinsa.Amma idan ba bu
wani wanda yake ganinsa,yana iya sallarsa daga tsaye,amma sai rufe gabansa da
tafin hannunsa.Amma a nan sai ya yi ruku'u da sujjada ta hanyar nuni,wato wajen
ruku;u ya dan duka kadan,sannan wajen sujjada ya duka fiye da na ruku'un.
|