Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Tufafin mai salla:

Mas'ala ta 803:Tufafin mai salla yana da sharudda guda shida:

Na daya:Dole ne ya kasance mai tsarki.

Na biyu:Ihtiyat wajib ya kasanci na halas.

Na uku:Kada ya kasance an yi shi ne daga mushe.

Na hudu: kada ya kasance an yi shi ne daga fatar dabbar da ta haramta a ci.

Na biyar da na shida:Idan  mai salla ya kasance namiji,Kada tufafinsa ya kasance an yi sa daga alharir zalla ko an gauraya sa da zinari kamar yadda za a yi  bayanin hakan a nan gaba.

 Sharadi na daya:

Mas'ala ta 804:Dfole tufafin mai salla ya kasance mai tsarki,idan mutum da gangana ya yi salla da tufafin ko jikinsa mai najasa,sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 805:Mutumin da bai san cewa ba salla da tufafi mai najasa yana bata salla ba,idan ya yi salla da tufafi ko jiki mai najasa sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 806:Idan mutum sakamakon ridhin sanin hukunci,sannan bai san cewa ba wani abu najasa ne kamar zufar rakumin da yake jin najasa, ko zufar Mushiriki,idan ya yi salla da daya daga cikinsu sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 807:Idan mutum bai san cewa ba tufafinsa yana da najasa sai bayan ya gama salla sai ya fahimci cewa tufafinsa yana da najasa, sallarsa ta inganta.Amma ihtiyat mustahab shi ne idan akwai lokaci ya sake sallar.

Mas'ala ta 808:Idan mutum ya manta da cewa akwai najasa a tufafinsa ko jikinsa sai ya tuna a lokacin da yake salla ko bayan ya gama sallar,a nan sallar sai ya sake sallar idan kuma lokaci ya wuce ya rama ta.

Mas'ala ta 809: idan mutum yana da isasshen lokacin yayin da yake cikin salla sai  jikinsa ko tufafinsa ya samu najasa, idan mutum kafin ya yi wani abu daga cikin sallar sai ya fahimci cewa jikinsa ko tufafinsa yana da najasa,amma sai mutum ya yi shakka a kan cewa shin yanzu ya samu najasar ko kuwa tun lokacin da ya gabata ne, idan wanke wannan najasar ko fitar da wadannan  kayan ko canza su ba zai bata sallar ba(wati ya fita daga halin salla)a nan yana iya wanke tufafin ko jikinsa ko canza wani tufafi kuma ya cigaba da sallarsa,amma idan hakan zai fitar damutum daga halin sallar ko kuma idan da zai fitar da tufafi zai kasnce tsirara, a nan dole ne ya karya sallar ya sake tufafi mai tsarki ko ya wanke jikinsa domin ya yi salla da tufafi ko jiki mai tsarki.

Mas'ala ta 810:Mutumin da yake cikin salla a cikin kurarren lokaci idan tufafinsa ya samu najasa yana cikin salla idan kafin yayi wani abu daga cikin sallar ya fahimci cewa tufafinsa ya samu najasa,amma sai ya yi shakka a kan cewa shin ya samu wannan najasa ne kafin ya fara salla ko kuwa,idan zamana wanke tufafin ko canza wani tufafi ko cire wannan tufafi ba fitar da mutum ba daga halin salla,to a nan yana iya cire tufafin idan akwai wani abu wanda zai rufe masa al'aurarsa  kuma ya cigaba da sallarsa,amma idan babu wani abu wanda zai rufe masa al'urarsa sannan ba zai iya wanke ko ya canza wannan tufafin ba tare da sallarsa ta baci ba,a nan sai cire tufafin sannan ya cigaba da sallarsa ba tare da tufafi ba sannan ya kiyaye hukuncin da a ka fada wajen wanda yake salla ba tare da tufafi ba.Amma idan ya kasance idan ya tsaya domin ya fitar da tufafin ko canza wani sallarsa zata baci ko kuma ba zai iya yin sallar ba a tsirara sakamakon sanyi ko wani dalili,a nan sai ya ida sallar da wannan tufafin mai najasa, kuma sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 811:Mutumin da yake cikin halin salla a cikin kurarren lokaci idan jikinsa ya samu najasa yana cikin salla idan wanna ya faru ne kafin ya yi wani abu daga ciin sallar sai ya fahimci cewa jikinsa ya samu najasa,sannan yana shakka a kan  cewas shin ya samu wannan najasa ne yana cikin salla ko kuwa kafin ya fara salla ne,Idan ya kasance wanke wannan najasa ba bata sallar ba a nan dole ne ya wanke najasar,amma idan zai bata sallarsa wajen wanke najasar, a nan sai ya  ida sallarsa  a haka kuma sallarsa ta inganata.

Mas'ala ta 812:Mutumin da yake shakka a kan tsarki jikinsa ko tufafinsa,Idan ya yi salla a wannan halin,amma bayan ya gama sallar sai ya fahimci cewa ya kasance yana da najasa ya yi sallar,a nab ihtuyat mustahab shi ne,idan a kwai sauran lokacin sallar ya sake sallar,idan kuwa lokaci ya wure sai ya rama.

Mas'ala ta 813:Idan mutum ya wanke tufafinsa kuma ya samu yakini a kan cewa ya wanku,sannan ya yi salla da wannan tufafin ,bayan ya yi sallar sai ya fahimce cewa  ba wanku ba, anan ihtiyat waji shi ne ya sake sallar idan da sauran lokaci,idan kuwa lokacin sallar ya fita sai ya rama sallar.

Mas'ala ta 814:Idan mutum ya ga jini a jiki ko tufafinsa sannan ya samu yakini a kana cewa  wannan jinin ba na najasa ba ne wato na wani abu ne kamar sauro,amma sai bayan da ya gama salla sai ya fahimci cewa wannan jinin na najasa ne wato ba zai yiwu a yi salla ba da shi,a nan sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 815:Duk lokacin da mutumya samu yakini a kan cewa jinin da yake a kan jikinsa ko tufafinsa na najasa ne wanda ya halatta a yi salla da shi, kamar jinin ciwo ko makamancinsa,amma bayan ya gama salla sai ya fahimci ce wannan jinin yana daga cikin jinin da ba zai yiwu a yi salla ba da shi,a nan ma sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 816:Idan mututm ya manta da cewa wani abu yana da najasa idan jikin mutum ko tufafinsa masu lema suka taba  wannan abin sai ya manta ya yi salla da wanna abin,bayanya gama sallar sai ya tuna sallarsa ta inganta.Idan mutum ba tare da ya wanke wannan wurin da najasa ta taba ba, sai ya yi wanka da ruwa dan kadan ya yi salla, a nan sallarsa ta baci.Amma idan mutum ya yi wanka ne da ruwa mai yawa kamar ruwa mai gudu ko wanda yawansa ya kai na kur,wanka ya inganta,domin sakamakon tabawar farko wurin najasar zai tsarkaka,saboda haka sallarsa ma ba ta wata matsala.Amma idan wurin da yake da najasa daya daga cikin gabban al'walla ne idan ya zamana mutum kafin ya wanke wannan wurin sai ya yi alwalla kuma ya yi wanke daya ne kawai a nan alwallarsa ta baci kuma sallarsa da wannan alwalla ta baci,amma idan ya yi alwalla ne da ruwa mai yawa kamar ruwan Kur ko mai gudu, ko kuma ya wanke sau uku ne yayin alwlla,a nan alwallarsa ta inganta kuma sakamkon hakan  sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 817:Mutumin da yake da tufafi guda daya,Idan jikinsa ko tufafin ya samu najasa,sannan kawai yana da ruwan da zai iya wanke daya daga cikinsu ne kawai Idan zai iya cire wannan tufafi a nan sai ya wanke jikinsa da wannan ruwan sannan sai ya yi aiki da hukuncin yadda wanda ba shi tufafi zai yi salla,sannan sai ya yi sallarsa ba tare da tufafi ba.Amma idan ba zai yiwu ya cire kayansa ba sakamakon sanyi ko makamancin hakan a nan sai ida ya ka sance najasar jikin da tufafin duk daya ne,wato duka biyu fisari ne ko jini ko kuma najasar jikin tafi tsanani misali najasar da take bisa  jikinsa fitsari ne wanda dole ne ya wanke sa sau biyu idan dsa ruwa kadan ne,ihtiyat wajib shi ne ya wanke jikinsa da ruwan.Amma idan najasar da take a kan tufafin tafi tsanani kotafi yawa, a nan yana da zabi a kan ya wanke ko wane daya daga cikinsu wanda  yake so.

Mas'ala ta 818:Mutumin da ba shi da wani tufafi wanda ba shi da najasa kuma lokacin salla ya kure,kuma ya tsammanin zai iay samun wani tufafi mai tsarki,a nan sai ya yi aiki da hukunci wanda yake tsirara ya yi sallarsa a tsirara,amma idan ba zai iya yin sallar ba a tsira sakamakon sanyi ko wani dalili, a nan yana iya yin sallarsa da wannan tufafin kuma sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 819:Mutumin da yake da tufafi guda biyu,idan ya san daya daga cikinsu yana da najasa amma bai san wane ne daga cikinsu ba yake da najasar,idan yana da lokaci dole ne ya yi sallar da kowane daya daga cikinsu,misali idan yana so ya yi sallar Zuhr da Asr da su dole ya yi kowace salla sau biyu wato da kowane tufafi daga cikinsu.Amma idan ya kasance ba shi da lokacin da zai yi sallo biyun,a nan ihtiyat wajib shi ne ya yi aiki da hukuncin sallar wanda ba shi tufafi sai ya yi sallarsa  a tsirara,ihtiyat wajib kuma shi ne ya rama wannan sallar da tufafi mai tsarki.

Sharadi na biyu:

Mas'la ta 820:Ihtiyat wajib dole ne tufafin mai salla ya kasan ce na halas(wato ba ta hanyar haram ba ne a ka same shi ba).saboda haka wanda ya san cewa amfani da tufafin da a ka kwata daga wani haramun ne,idan da gangan ya yi salla da tufafin da a ka samu ta hanyar kwace ko kuma an saka wannan tufafin ne daga abin da a ka kwata,ihtiyat wajib sallarsa ta baci.Saboda haka dole ne ya sake wannan sallar da tufafin da yake ba na haramun ba,haka nan idan mutum bai san hukunci sanya tufafin da suke na kwace ba,idan ya yi salla da su dole ne ya sake sallarsa.

Mas'ala ta 821:Mutumin da ya san cewa amfani da tufafin kwace haramun ne,amma ban cewa ba yana bata salla,idanya yi salla da tufafin kace kuma da gangan,ihtiyat wajib sallarsa ta baci,sannan dole ya sake wannan sallar da wani tufafin wanda ba na kwace ba.

Mas'ala ta 822:idan mutum ya manta ko bai san cewa ba tufafinsa na kwace ne,sai ya yi salla da tufafin,sallarsa ta inganta,amma idan da kansa ya kwaci tufafin sai ya manta yayi salla da su ihtiyat wajib sallarsa ta baci,sanna dole ne ya sake wannan sallar da wni tufafin da ba wannan ba.

Mas'ala ta 823:Idan abin da aka kwata sun kasance tare da mutum amma,abin dan karami ne kamar hankici ko tasbaha,idan mutum ya yi salla da su ba su ba ta masa salla.

Mas'ala ta 824:Idan mutum sakamakon kiyaye ransa sai ya yi salla da tufafin kwace,misali cikin tsananin sanyi da ba zai yiwu ya yi salla ba tare da tufafi ba,ko kuma yana gudun kada barawo ya sace wannan tufafin na kwace sai ya yi salla da shi,a nan sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 825:Idan mutum ya manta ko bai san cewa ba tufafinsa na kwacene,sai yana cikin salla sai ya fahimci hakan,idan yana tare da wani abu wanda zai rufe masa al'aurarsa,idan zai yiwu ya fitar tufafin  ba tare da ya  fita daga halin salla ba, a nan dole ne ya fitar da wannan tufafin kuma sallarsa ta inganata.Amma idan babu wani abu wanda zai rufe masa al'aurarsa, ko kuma ba zai yiwu ba ya ire wannan tufafin a cikin sauri ba tare da ya bata sallarsa ba,idan har akwai lokaci koda na yin raka'a daya ne a nan dole ne ya yanke sallar domin ya yi sallarsa ba tare da wannan tufafin ba,amma idan ba shi da lokaci ko wanda zai isa ya yi raka'a daya ta salla,a nan dole ne ya fitar da wannan tufafin ya yi sallar a tsirara tare da kiyaye hukunci wanda ke salla tsirara kamar yadda muka fada a baya.

Mas'ala ta 826:Idan mutum ya sayi tufafi da kudin da ba fitar musu zakka ko Khumusi ba,wannan tufafin hukuncin tufafin kwace yake da shi,don haka yin salla da shi yana bata sallar.Haka nana idan mutum ya sayi kaya bashi amma niyyarsa ita ce ya biya kudin wannan kayan da kudin da ba a fitar da masu da zakka ko khumusi ba, ko kuma kudin haram,idan mutum ya yi salla da wadan nan kayan sallarsa ta baci.

Sharadi na uku:

Mas'ala ta 827:Dole ne tufafin mai salla kada ya kasance an yi sa da wani yanki daga mushe(na dabbar da take jinin yana tsartuwa idan an yanka ta)amma idan dq  wani yanki ne na  mushen wata dabbar  dq ana cin namanta  kamar kifi wanda ba shi da jini mai tsartuwa,ihtiyat mustahab a nan shi ne kada mutum ya yi sallar ma da irin wannan tufafin.

Mas'ala ta 828: Idan ya kasance wani abu daga cikin mushe kamar nama ko fatar dabbar wadan da akwai rayuwa cikinsu,wato ba kamar gashi ba wanda da za a yanke shi koda yana da rai ba zai ji komi ba,to idan mutum ya yi salla da wani yanki na mushe wanda yake da rai,sallarsa ta baci,koda kuwa tufafin ba nasa ba ne.

Mas'ala ta 829: Idan ya kasance wani abu daga cikin jikin mushe kamar gashi da makamancinsa wadan da babu rayuwa a cikinsu ida mtutm ya yi salla da tufafin da a ka yi da wadan nan abubuwan sallarsa ta inganata.

Mas'ala ta 830:Idan mutum ba shi da wani tufafi sai wanda yake nakwace ko wanda aka yi daga wani abu daga mushe,a nan dole ne ya yi salla ba tare da tufafi ba, tare da kiyaye hukuncin wanda zai yi salla tsirara.

Sharadi na hudu:

Mas'ala ta 831:Dole ne tufafin mai salla kada ya zmana an yi sa ne daga wani abu daga dabbar da namanta yake haram,don haka koda gashin wannan dabbar ya kasance tare da mutum idan ya yi salla da shi sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 832:Idan yawu ko wani abu makamancin haka daga dabbar da ba cin namanta kamar Mage ko kare suka taba jiki ko tufafn mutum madar suna nan da lemarsu idan mutum ya yi salla a haka sallarsa ta baci,amma idan sun bushe ta yadda babu su a jikin mutum ko tufafinsa idan ya yi salla ta inganata.

Mas'ala ta 833:Idan gashin wani mutum ko yawunsa ya kasance a jikin mai salla ko tufafinsa babu wata matsala,haka idan zuma ko makamancinta suka taba mutum.

Mas'ala ta 834:Idan mutum yana shakka a kana cewa shin wannan tufafin an yi sa daga wani na dabbar da ake ci ko kuwa da ga wata dabbar da ba a  ci ne,wannan tufafin koda kuwa an yi sa cikin ko waje,salla da shi babu wata matsala.

Idan mutum yana tsammanin cewa baballinsa an yi sa daga wani abu daga dabbar da ake cin namanta,babu laifi ya yi salla da shi.

Mas'ala ta 837:Idan mutum bai sani ba shin wannan tufafin an yi sa daga fatar dabbar da ake ci ko kuwa da fatar dabbar da take haramun ne,idan ya yi salla da wannan tufafin sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 838:Babu laifi ayi salla da tufafin fatar da aka yi daga roba da makamancinta.Saboda haka duk lokacin da mutum yake shakka akan cewa shin wanna fatar da gaske ce ko kuwa an yi ta ne daga wani abu,ko kuwa fatar dabbar dake ci ko kuwa daga dabbar da ba a ci,idab kuma wadda ake ci ce shi nan yanka ta ko kuwa, a nan idan mutum ya yi salla da wannan tufafin sallarsa ta inganata.

Mas'ala ta 839:Idan mutum ba shi da wani tufafi sai wanda aka yi daga fatar da dabbar da ba a cin namanta,idan ya zamana babu makawa sai ya sanya tufafi,a nan yana iya yin salla da wannan tufafimn babu wata matsala,amma idan ba dole ne ba ne sai ya sanya tufafin a nan sai ya yi sallarsa a tsirara tare da kiyaye hukuncin wanda zai yi salla a tsirara.Sannan ihtiyat wajib shi ne ya sake yin wata salla da wannan tufafin.

Sharadi na biyar da na shida:

Mas'ala ta 840:Haramun ne namiji ya sanya tufafin da aka saka da zinari,amma babu matsala ga mace a cikin salla da ba lkacin sallar ba.

Mas'ala ta 841: Haramun ne namimji ya sanya sarka, agogo ko zobe da makamancinsa,don haka idanmutum ya yi salla da su sallar sa ta baci.haka nana wajibi ne namiji ya kaurace wa sanya tabrau da aka sanya wa zinari.Amma babu laifi ga mace ta ti ado da zinaria cikin salla ne ko ba cikin sallar ba.

Mas'ala ta 842: Idan namiji sakamakon mantuwa ko rishin sani ya yisalla da wani abu da aka yi da zinari ihtiyat wajib sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 843: Sanya wani abu da aka yi da zinari ya haramta ga namiji wannan kuwa ya faru ne a fili ne ko a boye,sannan idan ya yi salla da shi sallarsa ta baci.Saboda haka koda rigar cikin da mutumya sanya ta kasance an saka ta ne daga wani abu daga zinari,ko kuma ya sanya sarka ne koda ba a ganin ta,haramun ne kuma salla da daya daga ciki yana bata salla.

Mas'ala ta 844: Haka nan tufafin mai salla namiji kada ya zamana alhariri zalla,sannan kuma ihtiyat wajib shi ne,koda abu karami ne wanda ba zai isa a sutueta al'aurada shi ba,idan dai an yi sa ne daga alharir zalla yana bata salla.sannan kuma ya haramta ga najimi ya sanya shi koda ba a cikin salla ba.

Mas'ala ta 845: Idan ya zamana an yi nunkin riga da wani abu wanda yake alhariri ne zalla ko kuma wani abu daga cikin rubin rigar,ya haramta ga namiji ya yi amfani da shi,kuma idanya yi salla da wannan tufafi sallarsa ta baci.

Mas'ala ta 846: idan ya zamana sarka ko zoben zinari yana cikin aljihun namiji ba wata matsala,don haka idan mutum ya yi salla a haka sallarsa ta iganta.

Mas'ala ta 847: Babu matsala mutum ya sanya tufafin da bai sani shin an saka shi ne daga alharir zalla ko kuwa,don haka idan ya yi salla da shi sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 848: Idan mututm ya sanya hankicin da aka yi daga alharir a cikin aljihu,sannan sai ya yisalla a haka,sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 849: Babu laifi mace ta sanya tufafin da aka yi daga alharir zalla a cikin salla ne ko ba a cikin salla ba.

Mas'ala ta 850: Babu laifi mutum ya yi amfani da tufafin da uyake na kwace ko wanda aka saka daga alharir ko aka yi sa daga wani abu na dabbar da baa cin namanta ko kuma mushe,idan mutum babu yadda zai yi sai ya yi amfani da su din,wato ba shi da wani tufafi sai wanna din.Haka nana idan ya zama dole ya sanya tufafi a lokacin salla kuma ba shi da ani tufafi sai wannan yana iya yin salla da shi kuma sallarsa ta inganta:

Mas'ala ta 851: Idan ya zamana tufafin mutum yana da gauraye da alharir,babu laifi mutum ya yi salla da shi,da sharadin idan ya kasance abin da aka gauraya da shi ya halatta ayi salla da shi,amma ya zamana alharir din ya fi yawa abin da aka hada shi kuwa dan kadan ne,a nan  bai halitta ba namiji ya yi salla ya da shi.

Mas'ala ta 852:Idan namiji ya kasance ba shi da wani tufafi sai wanda aka saka da alharir zalla,kuma bai zama dole ba ya sanya tufafi a lokacin,a nan sai ya yi salla a tsirara tare da kiyaye hukuncin mai salla a tsirara.

Mas'ala ta 853:Idan mutum ba shi da wani abu wanda zai rufe al'aurarsa yayinsalla,wajibi ne ya yi kokari ya samrda shi koda ta hanyar haya ne ko aro,ammaidan ya zamana mutum sai ya kashe kudi da yawa wajen tanadar tufafin ta yadda zai iya cutawa sakamakon hakan,ta yadda idan ya yi amfani da kudinsa wajen tanadar kayan da zai yi salla,wanda sakamakon hakan zai cutu,a nan sai ya yi amfani da hukuncin mai salla a tsirara ya yi sallarsa a hakan.

Mas'ala ta 854:Idan mutum ba shi da kayan da zai sa ya yi salla,sai wani ya ba shi kyauta ko aro kuma ya zamana idan ya masa ya yi amfani da su ba zai matsala gare shi ba daga baya,a nan dole ne ya amsa ya yi amfani da su.Haka nana idan ba zai matsala ba yana nemana aron da kansa don ya sanya ya yi salla da tufafi.

Mas'ala ta 855:Ihtiyat wajib shi ne mutum ya kaurace wa sanya kayan da suke zasu fitar da mutum daga cikin mutane,wato kalar kayn ne ko kuwa yanayin dinki da ya yi msu da yadda zai fita daban daga cikinmutune,amma idan mtum ya salla da wadan nan kayan babu laifi sallarsa ta inganta.

Mas'ala ta 856: Abin da ake nufi da tufafin da zai sa mutum ya sha bamban da mutane kuwa shi ne ta yadda mutanen da mutum da yake rayuwa a cikinsu idan ya sanya wadan nan kayan zasu ganshi wani mutum daban a cikinsu wanda ya zo da wani sabo wanda ya sabawa mutane ta yadda za a rika nuna shi.

Mas'ala ta 857: Ihtiyat wajib shi ne,kada namiji ya sanya kayan mata kuma mace kada ta sanya kayan maza,wato namiji kada sanya kayan da za a iya cewa wadan nan kayan mata ne,haka nan ita ma mace kada ta sanya kayan da za a iya cewa wadan nan kayan maza ne.Saboda haka idan namiji ya sanya sifas kawai na mata babu wata matsala haka nan ita ma,amma idan namiji ya yi salla da kayan mata babu wata matsala haka nan ita ma.

Mas'ala ta 858: Mutum da ba shi da abin zai suturta al'aurarsa,idan yana tsammanin zai iya samu zuwa nan gaba kafin lokacin salla ya fita,yana iya jinkirta sallarsa har zuwa karshen lokacin da zai iay samu abin zai rufe al'aurarsa da shi sannan ya yi sallar.

Mas'ala ta 859: Mutum da yake babu yadda zai yi ya yi salla sai a kwance,Idan ya kasance a tsairara sannan abin shinfidarsa yana da najasa ko kuma an yi sa ne daga alharir zalla ko kuwa an shi ne daga wani daga dabbar da bai halitta  a ci namanta ba,ihtiyat wajib shi ne kada ya rufe jikinsa da wadan abubuwan wato sai ya yi sallarsa a tsirara.