Wuraren da suke ba wajibi ba ne tufafin dq jikin mai salla ya zama mai tsarki:
Mas'ala ta 860: Wurare guda uku ne kamar yadda zasu zo idan
mutum ya yi salla tare da jiki ko tufafin mai najasa bamatsala ku,kuma sallarsa ta inganta:
Na daya: idan ya zamana sakamakon ciwo ko kurji a jikin mutum
sai jikinsa ko tufafinsa suka samu najasa da jini.
Na biyu:Idan bisa jikin mutum ko tufafinsa akwai akwai jini
wanda girmansa bai wuce kan dan tyatsa ba,sai dai idan ya kasance daya ne daga jininanen da
zamu fada a ciin mas'ala ta 861.
Na uku:A inda ya zama dole mutum ya yi salla da tufafi mai
najasa.
A wurare biyu kawai idan mutum ya yi salla da tufafi mai najasa
sallarsa ta inganta.:
NA daya Idan ya zamana abin da yake da najasar karami ne safa ko safar
hannu.
Na biyu:Idan ya zamana tufafin mai najsa na mace mai goyo ne,kamar
yadda zamu fadi hukuncinsa a nan gaba ta fuskoki guda biyar.
Mas'ala ta 861: Idan ya zamana tufafin mai salla ko jikinsa ya samu jini
ta hanyar ciwon da yake da shi,ta yadda wanke jinin ko canza wasu kaya zai zama
wahala ga mutumin,Har ya zuwa lokacin da raunin zai warke mutum yana da uziri
ya yi salla da wannan jinin da ya bata masa jiki ko tufafi.Haka nan idan jinin
ya bata abin da aka daure ciwon da shi ko kuma maganin da yake a kan ciwon sai
ya taba jikin mutum ko tufafinsa.
Mas'ala ta 862: Idan jinin ciwo karami wanda bai shiga cikin jiki ba
sosai ya bata jikin mutum ko tufafinsa kuma yawansa ya kai ko ya dara kan dan yatsa, ta yadda wanke sa ba zai zama da wahala ba,idan mutum ya yi salla da shi
sallarsa ta baci.
Mas'ala ta 863: Idan ya zamana wirin da yake da nisa tsakaninsa da inda
yake da ciwo sai ya samu najar wannan ciwon,a nan bai halitta ba mutum ya yi
salla da wannan najasar,amma idan ya zamana kusa da ciwon ne ta yadda ya kan
taba lemar ciwon ko kuma idan tufafi ne ya kan taba ciwon, anan salla da shi
babu matsala.
Mas'ala ta 864: Jinin da yake fitowa da dadashin mutum ko hancinsa ba su
da hukuncin jinin ciwo,don haka idan daya daga cikin ya taba jiki ko tufafin
mutum bai halitta ba ya yi salla da shi,sai dai idan yawansa bai kai girman dan
yatsa ba.Amma jinin basir da yake fitowa ta duburar mutum yana da hukuncin jinin
ciwo don salla da shi babu matsala.
Mas'ala ta 865: Mutum da yake da ciwo a jikinsa idan ya ga jinin a jikinsa ko
tufafinsa,sannan ya kasa gane cewa shin wannan jinin daga ciwon ne ko kuwa wani
jini ne daban,babu laifi yana iya yin salla da shi babu matsala.
Mas'ala ta 866: Idan mutum yana ciwuka a jiki da yawa sannan kuma suna
kusa da kusa,ta yadda za a iya cewa ciwo daya ne,har ya zuwa lokacin da zasu
warke salla da jininsu babu matsala.Amma idan suna da nisa da juna ta yadda za
a iya cewa ko wane daya daga cikin ciwo ne mai zaman kansa,don haka lokacin da
daya daga cikinsu ya warke dole ne mutum ya wanke jinin wannan wanda ya warke
din daga jikinsa ko tufafinsa kafin ya yi salla.
Mas'ala ta867:Idan jinin haila
dai-dai da kan allura ya kasance a kan tufafin mai salla,idan ya yi salla da shi
sallarsa ta baci.Sannan ihtiyat wajib bai kamata ba jinin biki ko na istihala su
kasance bisa tufafin mai salla,sannan ya kamat a kaurace wa jinin dabbar daq ba
a ci,amma jinin dabbada a ke ci ko na mutum koda ya kasance a wurare da yawa ta
yada idan da za a tattara shi wuri guda ba zai kai fadin kan dan yatsa ba,idan
mutum ya yi sala shi babu matsala sallarsa ta inganta.
Mas'ala ta868:Jinin da ua zubabisa
tufafin da ba ya da shafi sannan jinin ya isa zuwa bayan tufafin,za a lissafa
wannan jinin na gaba da na baya matsayin jinin guda,amma idan ya kasance tufafi
yana da shafi ta yadda bayan tufafin ya bambanta da gabansa, anan dole ne a
lissafa kowa ne jinin daban.Saboda haka idan jinin da yake gaba da baya baki
daya bai kai girmana kan danyatsa ba salla da shi babu matsala,amma idan an hada
su duka gida biyu sun kai yawan kan dan yatsa a nan salla da shi ba ya inganta.
Mas'ala ta869:Idan jini ya zuba bisa
tufafin da yake da shafi sannan jinin ya isa zuwa ga shafin,ko kuma jinin zuwa
ne bisa shafin sannan ya isa har zuwa ga wajen tufafin,a nan idan duka jinin da
yake bisa tufafin da wanda ya isa zuwa shafin tufafin ko kuma wanda yake bisa
shafin da wanda yake bisa tufafin ba su kai girman kan dan yatsa ba babu matsala
yin salla da shi kuma sallar ta inganta,ammam idan ya wuce haka salla da shi ba
ya inganta.
Mas'ala ta870:Idan jinin da ya ke
bisa tufafin ko jikin mai salla ya gaza wa girman kan dan yatsa,idan lema ta isa
zuwa ga wannan jinin sannan jinin da lemar da ta taba shi sun kai girman kan
yatsa,sannan wannan lemar ta bata gefen wurin,bai halitta ba mutum ya yi salla a
haka idan mutum ya yi salla haka sallarsa ta baci.Kai kodama lemar da jinin ba
su girmana kan dan yatsa ba kuma ba su bata gefen wurin da suke ba,salla da shi
haka yana da matsala,amma idan lemar ta hadu da jinin ta yadda yanzu ba a ganin
jinin idan mutum ya yi salla da shi babu matsala kuma sallarsa ta inganta.
Mas'ala ta871:Idan jilin mutum ko
tufafinsa ba su baci da jini ba amma ta hanyar taba jini sai suka kasance masu
najasa,a nan koda wurin da ya zama mai najasa bai kai girmana yatsa ba bai
halitta ba a yi salla da shi ba.
Mas'ala ta872:Idan jinin da ya
kasance a bisa tufafi ko jiki bai kayi girmana yatsa ba amma sai wata najasa ta
taba wajen misali kamar fitari ya taba wajen.a nan bai halitta ba mutum y a yi
salla da wannan tufafi ko jikin da ya samu wanna najsar.
Mas'ala ta873:Idan najasa ta taba
daya daga cikin kanan tufafin mai salla kamar diko ko safa da makamantansu wato
abubuwanda bai yiwuwa a rufe al'aura da su, sannan kuma ba an yi su ba ne daga
fatar dabbar da take haram,a nan ya halitta mutum ya yi salla da su kuma
sallarsa ta inganta.Haka nana idan mutum ya yik salla da gilashi ko zobe mai
najasa sallarsa ta inganata.
Mas'ala ta874:Ihtiyat wajib shi ne
kada mutum ya yi salla da abu mai najasa kuma wanda zai yiwu a rufe al'aura da
shi,amma babu laifi don mutum ya yi salla da abu mai naja sa amma wanda ba zai
yiwu ba mutum ya rufe al'aurarsa da shi ba, kamar hankici ko mabudi ko wuka masu
najasa, haka babu laifi don mutum ya yi salla da kudi masu najsa.
Mas'ala ta875:Matar da take rainon
yaro,ihtiyat wajib idan yaron ya kasance namiji kuma ba ta da tufafi fiye da
guda daya idan ba zata iya sayen wani tufafin ba ko kuma ba zata iya aron wani
ko ta amso haya ba,Idan ta wanke tufafin sau daya cikin tawon kwana daya koda
kuwa yaron ya yi mata fitsari ne a rana ta biyu tana iya yin salla da wannan
tufafin babu matsala.Amma ihtiyat wajib shi ne matar ta wanke tufafi sau daya a
cikin kwana da yini,sannan ya kasance ta wanke tufafin ne a farkon sallar da
zata yi bayan tufafin ya samu najasa.Haka idan ta kasance tana da fiye da tufafi
guda amma dole ne ta yi amfani da su baki daya a lokacin sallar,saboda haka idan
a tsawon kwana da yini ta wanke tufafin kamar yadda muka fada a sama ya
wadatar.Amma idan tana iya sayen wani tufafin ko kuma ta amso haya,ihtiyat wajib
shi ne ta yi salla a cikin tufafi masu tsarki.
Abubuwan da suke mustahabbi ne dangane da tufafi ga mai salla:
Mas'ala ta876:Musatahabbi
ne sanya rawani tare da sako wutsiyarsa a gaba,haka nan an so mutum ya sanya
abaya musamman limami,sannan musatahabbi ne mutum ya sanya fararen kaya yayin
salla kuma suka kasance a cikin tsabta,Sannan mustahabbi ne mutum ya sanya
turare kuma sanya zoben akik a dan yatsansa yayin da yake salla.
Abubuwanda suke makaruhi dangane da tufafin mai salla:
Mas'ala ta877:Makaruhi ne
mutum ya yi salla da bakaken kaya,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla da kaya
wadan da suke sun matsa jinkin mutum,kuma makaruhi ne mutum ya yi salla da
tufafin mai shan giya,Sannan makaruhi ne mutum ya sanya tufafin mutumuimin da
bai kula ba da kiyaye najasa,haka nana makaruhi ne mutum ya sanya tufafi masu
zanen hotuna, kuma makarihi ne mutum ya bude maballensa yayin salla,haka nan
makaruhi ne mutum ya sanya zoben da yake da zanen hoto a hannunsa ya yin salla.
|