| 
		
	 | 
	
	
  Wurin mai salla:
Wurin da mutum zai yi salla yana da sharudda kamar haka:
Sharadi na daya:
Mas’ala ta 878:Mutumin 
da ya yi salla a cikin gida ko makamancinsa na kwace koda bisa shinfida ne ko 
wani abu makamancin hakan, sallarsa ta baci,amma mutum yana iya yin salla 
karkashin rufin da yake ba na halas ba ne kuma sallarsa ta inganta.
 Mas’ala ta 879:Idan 
mutum ya yi salla a gida yake wani ne yake amfani da gidanyin salla ba tare da 
neman izininsa ba yana bata salla,haka nan idan mutumu yana salla a wani gida 
bai kamata ba wani ya yi salla a gidan sai da izinin wanda yake hayar, idan 
mutum ya yi salla a gidan ba tare da izininsa ba sallarsa ta baci.Haka nan yin 
salla a gidan wani yake da hakkia cikinsa ba tare da izininsa ba yana bata 
salla’misali idan wani ya yi wasiyya a kaba wani gida cewa daya bisa ukkun 
wannan gidan ya bayar da shi zuwa ga wani to madamar ba a cire hakkin wancan din 
ba bai halita a yi salla a cikinsa ba.
 Mas’ala ta 880:Idan 
mutum yana zaune a cikin masallaci sai wani mutum ya zo ya kwace masa wuri,idan 
wannan mutumin ya yi salla a wajen, ihtiyat wajib shi ne ya sake sallarsa a wani 
wurin na daban wanda ba wannan ba.
 Mas’ala ta 881:Idan 
mutum ya yi salla a wurin da yake na kwace sai bayan ya gama salar ya fahimci 
hakan,ko kuma ya manta da cewa na kwace sai bayan ya gama sallar ya tuna, a nan 
sallar ta  inganata  sai dai idan da kansa ya kwaci wannan wajen, a nan Ihtiyat 
wajib shi ne ya sake sallarsa.
 Mas’ala ta 882:Idan mtum ya san cewa wannan wurin na kwace ne,amma bai san  cewa  salla a wurin da 
yake na kwace yana bata salla ba,a nan sallarsa ta baci.
 Mas’ala ta 883:Ya 
halita a yi sallar nafila a bisa abin hawa yayin da mutum yake cikin tafiya,koda 
kuwa mutum yana da zabin ya sauka daga bisa abin hawan domin ya yi sallar,haka 
nan ya halita mutum ya yi sallar wajibi a bisa abin hawa yayin da mutum ba shi 
da zabi a kan ya sauka  domin ya gabatar da sallar.Saboda haka a cikin wannan 
halin idan ya kasance abin zaman doki ko kujerar mota,jirgin kasa ko jirgin 
saman  da mutum yake zaune ta kwace ce,a nan sallar mutum ta baci.
 Masa’ala ta 884:Bai 
halita ba mutum ya yi salla  a gida na kwace wanda ba a san ko na wane ne 
ba,saboda haka salla a cikin wannan gida ta baci,saboda haka domin sanin nauyin 
da ya hau kan wanda ya yi salla a irin wannan wurin sai a koma wajen marja’in da 
yake da sharudda.Haka nan amfani da  gidan da yake an gina shi ne da abubuwan da 
suke na kwace ne yana da hukuncin gidan kawace kuma bai halita a yi slla ba.Amma 
yin salla a irin wannan gidan idan dai filin ba na kwace ba ne, kuma ba a  yi 
masa shinfida ba da darduma ta haram, a nan babu laifi a yi salla a ciki kuma 
sallar ta inganta.
 Mas’ala ta 885:Mutumin da suka hada gida da wani,idan bangaren nasa ba yana daban ba ne,ba tare da 
izinin dan’uwansa ba,ba zai iya amfani da wannan gidan ba kuma ba zai yi salla 
ba a cikinsa.
 Mas'ala ta 886:Idan 
mutum ya sayi gida da kudin da ba a  fitar wa khumusi  ko zakka ba,a nan yin 
amfani da wannan gidan ga wannan mutum ya haramta, haka nan idan ya yi salla a 
cikinsa sallarsa ta baci,haka nan ihtiyat wajib idan mutum ya sayi gidan a kan 
cewa zai biya daga baya, amma nufinsa shi ne zai biya da kudin da zai fitar na 
zakka ko khumusi,shima a nan yana da wannan hukuncin.
 Mas'ala ta 887:Idan 
mai gida ya ba mutum izini ya yi salla a cikin gidansa,amma mutum  ya san a 
cikin zuciyarsa bai amince ba,a nan idan mutumya yi salla a cikin gidan sallarsa 
ta baci.Haka nan koda mai gidan bai bayar da izini ba da baki amma mutum ya san 
cewa a cikin zuciyarsa ya amince,a nan idan mutum ya yi salla a cikin gidan 
sallarsa ta inganta.
 Mas'ala ta 888:idan mutum ya mutu 
sannan ana binsa bashi kuma kudin da a ke binsa bashi sun fi karfin dukkan kudin 
da garesa ko kuma sun yi dai-dai ada abin da yake da shi,a nan bai halitta ba 
masu gadonsa su yi salla ko amfani da wadan nan dukiyar sai tare da iziznin 
wadan da suke binsa bashi.Amma idan bashin da ake binsa bai kai yawan kudin da 
ake binsa ba a nan  masu gadonsa suna iya yin amfani da dukiyar ko salla a cikin 
gida ko filin da ya bari amma tare da sharudda guda biyu kamar haka:
 1-Idan sun fahimci cewa masu binsa kudi sun aminta da suyi 
amfani da dukiyarsa.
 2-Masu gadonsa su yi niyyar biya masa bashin da a ke 
binsa.
Mas'ala ta 889:Amfani da gida ko 
yin salla a cikin gidan mamacin da ake binsa bashi haramun ne kuma idan mutum ya 
yi salla a cikinsa sallarsa ta baci.Amma idan bashin da ake binsa bai kai yawan 
dukiyar da ya bari ba kuma wadan da suke binsa bashin sun aminta da a yi amfani 
da dukiya ko gidan, sannan kuma masu gadonsa sun yi niyyar biyan bashin da ake 
binsa a nan salla a cikinn wannan gida ko amfani da dukiyar babu laifi.Amma 
idan  ya  kasance haka dole ne a nemi izini daga masu gadonsa don yin amfani ko 
salla cikin gidan da ya bari.
 Mas'ala ta 890:Idan mamaci ba a 
binsa bashi amma a cikin masu gadonsa akwai kananan yara ko wanda ba shi da 
hankali, ko kuma  wani daga cikin magada ba ya nan, a nan kawai za a iya afani 
da dukiyar mamacin wajen yi masa likkafani da abin da ake bukata awajen rufe 
mamaci ta yadda ba za a barshi ba a rufe sa ba,amma sauran amfani da dukiyar da 
yin salla a cikin gidansa bai halitta ba,idan aka yi salla a gidan sallar t 
abaci,sai dai idan mai kula da dukiyar ya bad a izinin yin hakan.
 Mas'ala ta 891:Babu laifi yin 
salla a wurare kamar gidan abinci da gidajen baki da makamantansu wadan da aka 
tanada domin amfanin mutanen da suka sauka a wajen ko suka zo doin cin 
abinci,ammaidan mutum bay a zo ba ne a wajen domin cin abinci ko kuma domin 
sauka a wajen, madamar babu amincewar masu wajen bai halittaba ya yi salla a 
wajen ba.Amma ba ya halitta yin salla a wuraren da suke na mutane ne  kamar 
gidajen mutane ko shaguna ba  tare da izinin masu wurin ba,amma idan mai wurin 
ya ba da izinin cewa wasu suna iya yin amfani da wurinsa kamar yin salla  a nan 
babu laifi,misali kaar mutum ya gayyaci wani zuwa gidansa domin cin abinci, a 
nan tabbas ya yarda mutumin ya yi salla a gidan.
 Mas'ala ta :892:Babu laifi yin 
amfani da gona ko fili mai fadi ta yadda kafin mutum ya fita daga cikinta akwai 
wahala,a nan don mutum ya yi salla ko ya kwanta ya yi barci a ciki babu wani 
laifi koda kuwa mai filin bai aminta ba,a nan koda kuwa masu wannan fili yara ne 
ko kuma marar hankali,duk da cewa idan har mutum ya san cewa masu wurin ba su 
amince a yi amfani da shi ba ihtiyat shi ne kaurace wa amfani da wurin.
 Sharadi na biyu:shi ne tabbatuwar wuri wato ya zama ba ya motsi:
 Mas'ala ta 893: dole wurin mai 
salla ya kasance a tabbace wato b aya motsi,saboda haka yin salla a bisa abin 
hawa wanda zai sanya mutum ya rika motsi yayin da yake yin sallar,sallarsa ta 
baci,sai idan babu wata makawa dole ne mutum ya yi sallar a nan wato bas ho da 
wani zabi a kan hakan,wato kamar karancin lokaci,saboda haka idan hakan ta 
kasance dole ne mutum ya kiyaye dukan sharuddan salla wato kada ya yi karatu ko 
zikiri yayi da abin wahan yake motsi,sannan duk lokacin da abin wahan ya juya to 
shi dole ne ya juwa ya kalli kibla.
 Mas'ala ta 894:Babu laifi mutum ya 
yi salla a bisa abi waha wanda bay a motsi ta yadda mutum zai iya samun natsuwa 
kamar jirgin ruwa da na sama da jirgin kasa tare da kiyaye sauran sharuddan 
salla kamar alkibla.Amma idan har mutane sun tafi a kan natsuwar abin hawa kamar 
kwalo-kwalo ko mota a nan bai halitta ba mutum ya yi salla a bisa sai dai bisa 
lalura kamar karancin lokaci.
 Mas'ala ta 895:Ba ya halitta a yi 
salla a bisa bagar alkama ko acca da tarin yashi wanda ba zai  yiwu ba ,mutum ya 
samu natsuwa da tabbatuwa a kansa. saboda haka yin salla a bisa ba ta 
inganata.Amma idan ya kasance motsin da suke ba shi da yawa ta yadda ba zai iya 
hana mutum ya aiwatar da wajiban salla da sauran sharuddanta ,a nan mutum yana 
iya yin sallarsa babu matsala.
 Mas'ala ta 896:Idan mutum ba ya 
tsammani samuwar ruwa da iska ko taron mutane ta yadda zasu iya hana shi 
sallarsa cikin natsauwa,idan  mutum ya fara sallarsa da fatar cewa zai iya gama 
sallar,sannan kuma har ya gama sallar bai hadu da wani abu ba wanda ya bata masa 
sallarsa,a nan sallarsa ta inganta.bai kamata ba mutum ya yi salla a wurin da 
yake tsammani faduwar rufi ko kuma inda duwatsu sukan iya zubowa,amma idan mutum 
ya yi sallarsa a wurin sallarsa ta inganta,amma ya aikata haram.Haka nan idan 
mutum ya yi salla a kan abin bai halitta ba a zauna a kansa kamar dardumar da 
take dauke da sunan Allah,idan mutum ya yi sallar ta inganta amma ya aikata 
haram. 
 Mas’ala ta 897:Ihtiyat wajib bai 
halitta ba a yi sallar wajibi a bisa rufin ka’aba sai dai a lokacin da mutm ba 
shi da zabi a nan babu matsala.
 Mas’ala ta 898:Babu matsala don 
mutum ya yi sallar mustahabbi a basa rufin ka’aba,amma mustahabbi ne mutu ya yi 
salla a cikin daki ka’aba ya kalli ko wane rukuni ya yi salla raka’a biyu.
 Sharadi na uku:Dole mutum ya yi 
salla a wuri da zai iya aiwatar da wajiban sallar:
 Mas’ala ta 899:Bai halitta ba 
mutum ya yisalla a wurin da rufisa yake kasa-kasa ta yadda mutum ba zai iya 
mikewa tsaye ba,ko kuma wurin dan kadan net a yadda mutum ba zai iya yin ruku’u 
da sujjada ba.Amma idan ya kasance mutum babu yadda zai yi dole ya yi salla a 
irin wannan wurin,a nan sai mutum ya yi kokari iya yadda zai iya ya yamike tsaye 
sannan ya yi ruku’u da sujja.
 Mas’ala ta 900:Dole mutum ya 
kiyaye ladabi ya yin da yake cikin haraminma’asumai.don haka bai halitta ba 
mututm ya yi salla gaban kabarin manzo s.a.w.a.sannan ihtiyat wajib shi ne ya 
kiyaye hakan a kabarin a’imma a.s.
 Mas’ala ta 901:Idan ya kasance 
tsakanin kabarin manzoko kona  Imam akwai abinda ya shiga tsakaninsu kamar bango 
komakamancinsa, a nan don mutu ya yi salla a gaban kabarin babu laifi.Amma 
akwatin da kabarin yake ko mayafin da ake sanyawa a rufe kabarin bai wadatar ba.
 Sharadi na hudu: wurin da mutum 
zai yi salla ya kasance zai iya bata wa mutum tufafi da najasa:
 Mas’ala ta 902:Idan ya zmaana 
wurin da mutum zai yi salla yana da najasa, to anan kada ya kasance najasar tana 
da lema ta yadda najasar zata iya samun jiki ko tufafin mai sallar,sai dai  idan 
nau’in najasar da babu matsala ko da taba tufafi ko jikin mai sallar.Amma dolre 
wurin da mutum zai aza gishinsa ya zama mai tsarki,saboda haka idan ya kasance 
mai najasa sallar mutum ta baci,koda kuwa najsar ba irin wadda zata cirata zuwa 
ga goshin mai sallar ba ce.Amma idan gwargwadpon wurin da yake wajibi a cikin 
sujjadar ya kasance mai tsarki ya wadatar.Amma dai ihtiyat mustahab shi ne wurin 
da mutum zai yi salla ya kasance mai tsarki.
 Sharadu na biyar:Dole  namiji ya 
kasance gaban mace yayin salla
 Mas’ala ta 903:Dole ne mace ta 
zama a bayan namiji a lokacin salla,sannan abin da yafi shi ne,ya kasance wurin 
da mace zata yi sujjada ya zama bayan wurin da namiji yake tsaye,a wannan 
hukuncin babu bambanci tsakani muharrami da ba muharrami ba,haka nan tsakanin 
miji da mata.Sannan babu bambanci tsakanin sallar mustahabbi ko ta wajibi.
 Mas’ala ta 904:Idan mace ta tsaya 
a gefen namiji a lokacin salla kuma sun fara sallar ne a lokaci guda,a nan 
dukansu sallarsu ta baci.Amma idan daya ya riga daya farawa na farkon sallarsa 
ta inganta amma na biyun sallarsa ta baci.
 Mas’ala ta 905:Idan ya kasance 
tsakanin namiji damace akwai abin ya raba tsakaninsu kamar bango ko wani abu 
makamancinsa ta yadda ba su ganin juna, ko kuma tsakaninsu akwai tazara kamar 
mita biyar, a nan sallarsu ta inganta. 
 Mas’ala ta 906:Idan mace ta yi 
salla a hawa na biyu, koda kuwa ta kasance kafada da kafada ko kuma tana 
gabansa,madamar yana kasanta ne salarsu ta inganta a nan koda kuwa bisan da yake 
tsakaninsu bai fi mita biyar ba.
 Sharadi na shida:Dole ne wurin mai 
salla ya kasance ba ya da tudu da kwari:
 Mas’ala ta 907:Bai halitta ba 
tsakanin wurin da mutum zai aza hannunsa da inda zai aza guyawunsa ya zamana 
bisansa ya dara tudun yatsun hannu guda hudu da mutum zai tsaida yatsunsa guda 
hudun.
   |