Wuraren da suke mustahabbi ne a yi salla a wajen:
Mas’ala ta 908:A cikin shari’ar musulunci an yi kwadaitarwa da
dama a kan yin salla a cikin masallaci,sannan wanda ya fi kowa ne daga cikin
masallatai shi ne masallacin ka’aba; sannan masallacin manzo a Madina, bayan
wannan kuwa sai masallavin Kufa,sai mai biye masa shi ne masallacin Qods, Bayan
wannan kuwa masallacin da ya fi girma shi ne masallacin Juma’a na kowane gari
sannan sai sauran maallatan unguwa,bayan masallanta unguwa sai na karshe shi ne
masallacin kasuwa.
Mas’ala ta 909:Amma dangane da mata kuwa shi ne abin ya fi shi
ne su yi sallarsu a cikin gida kuma cikin dakunansu na musamman,amma idan ya
kansance ta wata kowa ce fuska salla a cikin masallaci yana da fifiko wato
saboda wani abu ba wai don yin salla a cikin masallacin ba,wato kamar yin sallar
jam’I ko yin sallar zai sanya mace tafi samun natsuwa,saboda haka mace don ta
samu wannan falalalar tana iya zuwa masallaci tare da kiyaye hijabi,sannan idan
ma ba wata hanya wadda zata iya sanin hukunce-hukuncen addini sai ta hanyar zuwa
masallaci, a nan ya wajaba ma mace taje masallacin.
Mas’ala ta 910:Mustahabbi ne yin salla a haramin Imamai,kai ya
fi ma yin salla a masallaci,sannan yin salla a haramin Imam Ali a.s. yana
dai-dai da salla dubu dari biyu.
Mas’ala ta 911:Mustahabbi ne mutum ya rika yawan zuwan
masallaci,haka nan zuwa masallacin da mutane ba sa yawan zuwa.Mutumin da yake
makwabtar masallaci makaruhi ne ba tare da wani uzuri ba ya yi salla ba a
masallaci ba.
Mas’ala ta 912:Mustahabbi ne mututm ya kauracewa mutumin da ba
tare da wani uzuri ba, ba ya halattar masallaci domin salla,haka nan bai
halitta ba mutum ya ci abinci da irin wannan mutumin ko ya rika shawartar sa
wasu abubuwansa na rayuwa.Haka nan makaruhi ne mutum ya zama makocin irin wannan
mutumin wanda ba ya halattar masallaci,haka nan bai kamata ba a yi aure daga
gare shi ko kuma a auratar masa da mace.
Wuraren da suke makaruhi ne mutum ya yi salla:
Mas’ala ta 913:Makaruhi nemutum ya yi salla a wadan nan wuraren
masu zuwa:
Magewayi,kasa mai gishiri,a gaban wani mutum, a gaban kofar da
take a bude,a bisa kan titi ko hanya a nan idan ya kasance bai zai takura masu
wuce ba,saboda haka idan har ya kasance za takura amsu wucewa a nan haramun ne
mutum ya yi salla a wurin,sannan kuma sallarsa ta baci.Haka nan makaruhi ne
mutum ya yi salla a gaban wuta ko fitila ko a wurin dafa abinci da duk wurin da
yake da muehun wuta,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla a gaban rijiya ko
kwatamin da a ke yin fitsari,haka nanmakaruhi ne mutum ya yi salla a gaban hoto
ko butum-butumi abin da yake da rai,sai dai idan an rufe wannan butun-butumin da
wani kyalle,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla a dakin da mai janaba
yake,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla inda hoto yake koda ba wajen da ake
kallo yake ba,haka nan makaruhi ne mutum ya yi salla yana kallon kabari ko a
bisa kabarin,haka nan tsakanin kabura guda biyu ko makabarta.
Mas’la ta 914:Mustahabbi neMutumin da yake salla a wurin da
mutane suke wucewa,ko kuma a gaban wani mutum ya sanya wani abu wanda zai raba
tsakaninsa da masu wucewar ko kuma wanda yake a gabansa din, ko kuwa abin wata
sanda ce ko tasbi.
Hukunce-hukuncen masallaci:
Mas’ala ta 915:Haramun ne sanya najasa a cikinmasallaci ko
bangon cikin masallaci da rufin masallaci,sannan duk wanda ya fahimci cewa akwai
najasa a cikin masallaci dole ne ya yi sauri ya gusar da ita.Sannan ihtiyat
wajib shi ne a kaurace wa sanya najasa a bangon wajen masallaci,sannan idan ya
samu najasa dole ne a gusar da ita,sai idan wanda ya gina masallaci bai sanya
wannan wurin ba a cikin masallacin.
Mas’ala ta 916:Idan mutum ya kasa gusar da najasa daga masallaci
ko kuma ya nemi wanda zai taimaka masa amma bai sami ba, a nan tsarkake
masallacin bai wajaba ba a kansa,amma a nan dole ne ya sanar da wanda zai iya
gusar da najasar.
Mas’ala ta 917: Idan wani wuri a cikin maslalaci ya samu najasa
sannan ba zai yiwu ba a tsarkake shi sai dole an rusa wani wuri a nan sai cire
wajen kuma idan rusawar ba zata yi yawa ba sai a rusa sannan gyara inda a ka
rusa din bai zama wajibi ba,amma idan wanda ya sanya najsar shi ne ya rusa wajen
domin tsarkake najasar a nan dole ne ya gyara wajen day a rusa idan har yana da
ikon hakan.
Mas’ala ta 918:Idan aka kwaci masallaci sai aka gina gida ko
wani abu makamancinsa,ko kuma sakamakon a fadada hanaya a ka rusa wani bangare
na masallaci,ihtiyat wajib shi ne a kaurace wa sama wajen najsa,sannan idan ya
samu najasa wajibi ne a tsarkake wajen.
Mas’ala ta 919:Ajiye mamaci a cikin masallaci kafin a yi masa
wanka idan dai bazai janyo kwarara najasa ba a cikin masallaci ko kuma ba za a
kirga shi ba a matsayin tozarta masallaci ba,a nan ba wani abu a na iya sanya a
cikin masallaci ba wani abu.Amma abin day a fi shi ne a kaurace wa agawar a
cikin masallaci amma bayan an yi masa wanka babu matsala.
Mas’ala ta 920:Haramun ne sanya najasa a haramin manzo
s.a.a.w.saboda haka idan ya samu najasa idan dai najasar zata sanya ya zama
rishin girmamawa ga haramin manzon a nana wajibi ne a tsarkake najsar,ihtiyat
mustahab koda ba zai zama rishin girmamawa ba ne a gusar da najasar shi ne ya
fi.
Mas’ala ta 921:Idan shinfidar masallaci ta samu najasa ihtitay
wajib shi ne a wanke wannan shinfidar.
Mas’ala ta 922:Haramun ne mutum ya shiga da nasaja kamar jinni
ko fitsari a cikin masallaci idan dai har zai zama rishin girmamawa ga
masallacin,haka nan kai bain da yake da najasa a cikin masallaci idan har zai
zama rishin girmamawa ga masallacin haramun ne.
Mas’ala ta 923:A lokacin da ake aiwatar da wasu taruka kamar na
Ashura da dai makamantansu,idan zuwa da abubuwa kamar abinci da abin sha ba zai
zama kawar da al’farmar masallacin ba kamar hana yin salla a a cikin, babu wani
aibu a yin hakan.
Mas’ala ta 924:Ihtiyat wajib bai kamata ba a yi wa msallaco ado
da zinari,sannan bai kamata ba a yi zanen abu mai rai kamar mutum ko wani abumai
rai a cikin masallaci,amma zanen abin dab a shi da rai kamar hurannin kwalliya
makaruhi ne.
Mas’ala ta 925:koda masallaci ya rushe ba za iya saida shi ba ko
a yi hanya a inda yake.
Mas’ala ta 926:Haramun ne sayar da kofa ko tagar masallaci,don
haka koda sun lalace dole ne a gyara su domin yin amfani da su a wannan
masallacin,sannan idan ba zasu yi amfani ba a wannan masallacin dole ne a yi
amfani da su a wani masallacin daban wanda yake nukatar su.Amma idan ba zasu iya
yin amfani bag a wani masallacin a nan ana iya sayar da su sai a yi amfani da
kudinsu ga wannan masallacin ko kuma wani masallaci na daban.
Mas’ala ta 927:Mustahabbi ne gyara masallacin day a lalace ko
kuma wanda yake gaba da lalacewa,idan kuwa masallaci ya rushe ta yadda ba za a
iya gyara shi a nan ana iya rushe shi domin a sake gina wani.Sannan ana iya rusa
masallaci ma domin fada shi sakamakon kadan da ya yi kuma mutane suna bukatar
hakan.
Mas’ala ta 928:Mustahabbi ne a tsabtace masallaci,haka nan yi
masa kwalliya da fitilu,mustahabbi ne mutumin da yake son zuwa masallaci ya yi
sanya turare,mustahabbi ne ya sanya tufafi masu tsabta kuma masu kyau,sannan
mustahabbi ne mutum ya goge kasan takalminsa ta yadda zai kasance babu najasa a
kasanshi yayin da zai tafi masallaci.Mustahabbi ne mutum ya gara sanya kafar
damarsaa sannan ta hagu yayin da zai shiga masallaci,haka an so mutum ya fata
fito da kafar hagunsa yayin da zai fito daga masallaci,sannan mustahabbi ne
mutum ya riga kowa zuwa masallaci sannan kowa ya riga shi fita daga masallaci.
Mas’ala ta 929:Mustahabbi ne lokacin da mutum ya shiga masallaci
ya yi sallar nafila raka’a biyu a matsayin gaisuwa da girmamawa ga
masallaci,amma idan da mutum zai yi wata sallar wajibi ko wata nafila ta daban
ta wadatar.
Mas’ala ta 930:Makaruhi ne mutum ya yi barci a cikin masallaci
ba tare da wata lalura ba,haka nan makaruhi ne a yi labarin duniya ko na
kasuwanci a cikin masallaci,haka nan makaruhi ne a yi waka wadda ba tana isar da
wata nasiha ba ce, da dai makamancin wannan. Haka nan makaruhi ne zubar da yawu
ko majina ko yin kaki a cikin masallaci,sannan makaruhi ne a yi cigiyar wani abu
da ya bata,haka nan makaruhi ne daga murya a cikin masallaci,amma babu laifi a
daga murya domin kiran salla.
Mas’ala ta 931:Makaruhi ne a bar yaro ko mahaukaci ya shiga
masallaci,amma musatahhabi ne a je da yaro idan yaron ba zai yi hayaniya ba a
masallaci, sannan kuma zai kasance matsayin kwadaitarwa ne ga yaron domin ya
saba da zuwa masallaci.
Mas’ala ta 932:Makaruhi ne mutumin da ya ci albasa ko tafarnuwa
ya je masallaci madamar zai damu sauran mutane da warin bakinsa.
Kiran Salla da Ikama:
Mas’ala ta 933:Musatahabbi ne mace da namiji kafin su gabatar da
sallar yau da kullum su gabatar da kiran salla da Ikama.Amma kafin sallar Idi
mustahabbi ne mutum ya ce Assalatu,assatu,assatu har sau uku,haka nan kafin
sauran sallar wajibi mutum y ace Assalatu har sau uku da niyyar fatar neman lada
ga Ubangiji.
Mas’ala ta 934:Mustahhabi ne ranar da aka haifi jariri kafin
daurin da aka yi wa cibiyarsa ya fadi a yi masa kiran salla a kunnensa na dama
sannan a yi masa Ikama a kunnensa na hagu.
Mas’ala ta 935:kiran salla kalma sha takwas kamar haka:
اَلله اكبرُ sau huduَ ا شهدُ
اَنْ لا الهَ اِلاّاللهُ، اَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَّداً رسولُ الله ـ حىَّ عَلَى
الصَّلوةِ ـ حَىَّ عَلَى الفَلاحِ ـ حَىَّ عَلى خيرِ العملِ، الله اكبرُ ـ
لااِلَه اِلاّالله
wadan nan kuma ko wane sau biyu.
Amma Ikama kuwa za a ce Allahu Akbar na farko sau biyu ne
mai-makon sau hudu,haka nan la’ilaha illallah na kar she sau daya,sannan
bayan hayya ala khairil amal za a kara Kad kamatissalah sau biyu.
wannan bay a daga cikin kiran salla ko Ikama sai dai yana
اَشْهَدُ اَنَّ عَليَّاً وَلىُّ
اللهِ
Mas’ala ta 936:da kyau a fade she bayn Asshahadu anna muhammadarrasulullah a
matsayin neman kusanci da Allah madaukaki,( Ma’anar wannan kuwa shi ne, Ina
shaidawa lallai Ali waliyyin Allah ne).
Fassarar Kiran Salla da Ikama
اللهُ اكبرُ: Allah shi ne wanda ya fi
gaban a siffan ta shi.
اَشْهَدُ اَنْ لاالهَ الاّاللهُ
Ina shaidawa babu wani Ubangiji bayna Allah madauakai
wanda ya cancanci a bauta ma sa
اَشْهَدُ اَنَّ مُحَمَّداً
رسُولُ اللهِ: يعنى شهادت مى دهم كه حضرت محمد بن عبدالله(صلى الله عليه وآله)Ina
shaidawa manzo Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata agare sa ma’aikin
Allah ne
اَشْهَدُ اَنَّ عَليَّا
اَميرالمؤمنين وولىُّ اللهِ:Ina
shaidawa Ali shugaban Muminai waliyyin Allah ne.
حَىَّ عَلَى الصَّلوةِ:
A yo gaggawa zuwa wajen salla
حَىَّ عَلَى الفلاح:A
y0 gaggawa zuwa babban rabo
حَىَّ عَلَى خيرِ العَمل:A
yo gaggawa zuwa fiyayyen Aiki
قَد قامتِ الصَّلوة: ta tsaya
Hakika salla
لااِلهَ الاَّالله:Babu
wani abin bauta sai Allah
Mas’ala ta 937:Bai kamata ba a samu tsakani mai tsawo tsakanin
kiran salla da Ikama,idan kuwa haka ta faru to sai a sake kiran sallar daga
farko.
Mas’ala ta 938:idan kira salla ya kasance da murya irin yadda za
a iya cewa kamar ana waka irin wadda ake yi a wuraren shakatawa, wannan kiran
sallar ya haramta kuma ya baci dole ne a sake wani.
Mas’ala ta 939:Duk sallar da za yi tare da wadda ta gabace ta, a
nan kiransallarta ya fadi,a nan yin sallar tare da wadda ta gabace ta mustahabi
ne ko ba mustahabbi ban e,saboda haka kiran salla yana faduwa a wadan nan
wuraren kamar haka:
1-Kiran sallar la’sar a ranar jumu’a yayin day a kasance za a
hada sallar jumu’a da ta asr ko ta zuh da asr din.
2-Sallar asr a ranar Arfa,idan ya kasance za a yi tan e tare da
ta zuhr din ranar Arfa di.
3-Sallar Isha a daren Idin Babbar salla ga mutumin da yake a
Mash’aril haram kuma zai hada sallar Magarib da isha ne.Don haka hada salla a
wuraren da muka ambata a sama mustahabbi ne.
4-Sallar Asr da Isha ga mace mai istihala,domin tana gama zuhr
zata maida Asr ne haka nan Magrib da Isha.
5-Sallar Asr da Magrib ga mutumin dab a ya iya rike fitsari ko
kashi,a wadan nan wurare da muka ambata a sama kiran salla yana faduwa idan ya
kasance ba tare da tazara ba a ka yi wadan nan sallolin guda biyu.Amma idan ya
kasance akwai tazara a tsakani dole ne a yi kiran sallar,saboda haka yin nafila
tsakanin sallolin yana iya haifar da tazarar da ake nufi a nan.
Mas’ala ta 940:Idan aka yi iran salla a sallar Jama’I, ba dole
ban e ga mutumin da zai yi sallar jam’In ya sake wani kiran salla daban koda
kuwa bai ji kiran sallar da Ikama ba,wato sakamakon ba ya nan ne aka yi ko kuma
akwai nisa a tsakaninsu da mai iran sallar ko Ikama.
Mas’ala ta941:Idan mutum ya tafi masallaci domin ya yi sallar
jam’I,amma day a isa sai ya tarar an kare sallar,a nan matukar dai mutane ba
baje ba daga cikin sahu, ba zai yi wani kiran salla ba ko Ikama Idan dai har an
yi yayin sallar jam’in.
Mas’ala ta 942: a wurin day a kasance an yi sallar ana
sallar jam’I ko kuma ba dade bad a gama sallar jam’I idanmutum yana so ya yi
sallarsa shi kadai ko kuma zai yi a cikin wani jam’I wanda za a fara a
wurin,mutum zai iya yin sallarsa ba tare da Kiran salla ko Ikama ba,amma tare da
kiyayen wadan sharudda guda biyar:
1-Idan ya kasance an yi kiran salla da Ikama a sallar Jam’in.
2-Idan ya zamana wannan sallar Jam’in da a ka yi ta inganta.
3-Ya zamana a wuri daya ne da inda aka yi salla jam’in,don haka
idan da an yi sallar jam;I ne a cikin masallaci shi kuma zai sallarsa daga waje,
a nan sai ya yi kiran Salla da Ikama.
4-ya kasance sallarsa da ta jam’I duka an yi su ne na lokacin ba
matsayin ramuwa ba.
5-Ya zamana lokacin sallarsa da na jam’I duk daya ne,misali
kamar ya zamana an yi sallar Zuhr ne ko Asr shi kuma zai gabatar da daya daga
cikinsu ne ko Magrib da Isha.
Mas’ala ta 943:Idan mutum ya yi shakka a kan sharadi na na biyu
da muka fada a sama,wato ya yi shakka a kan shin sallar da a ka yi ta inganta ko
kuwa,a nan ba sai ya yi Kiran salla da Ikama ba,amma da zai yi shakka a cikin
sauran guda hudun,abin day a fi shi ne ya yi Kiran salla da Ikama tare da niyyar
fatan neman lada ga Ubangiji.
Mas’ala ta 944:wanda yake jin kiran salla mustahabbi ne ya rika
mai-maitawa daga hayya ala salla har ya zuwa hayya ala khairil amal.
Mas’la ta 945:Wanda ya j kiran salla da Ikama da shi ne ak yi su
ko bad a shi ba,idan ya na so ya yi salla idan dai babu tazara a tsakanin yana
iya yin salla ba tare day a sake kiran salla da Ikama ba.
Mas’ala ta 946:Idan namiji ya saurari kiran sallar mace domin ya
ji dadin muryarta, a nan kiran salla bai fadi ba a kansa,amma idan mace ta ji
kiran sallar namiji ya fadi a kanta.
Mas’ala ta 947:Kiran salla da Ikama na jam’I dole ne namiji ya
gabatar da su.
Mas’ala ta 948:Dole a gabatar da Ikama bayan kiran salla,don
haka idan aka yi Ikama kafin kiran salla bat a inganta ba.
Mas’ala ta 949:Idan aka gabar da kalmomin kiran salla ba a jere
ba,misali a fara cewa hayya al al falah kafin hayya alas salla, a nan dole ne a
dawo a fara fadar hayya alas sallah sannan a cigaba.
Mas’ala ta 950:Dole ne a kiyaye samara da tazara tsakanin kiran
salla da Ikama,idan kuwa ya kasance an samara da tazara a tsakani ta yadda ba
za a kissafa wannan kiran sallar a matsayin na wannan Ikamar ba,to dolene a
sake wani kiran sallar sannan a yi Ikama a yi salla.Haka nan idan a ka dade
bayan an yi Ikama ba a gabatar da sallar ba, a nan mustahabbi ne a sakekiran
salla da wata Ikamar sannan a gabatar da sallar.
Mas’ala ta 951:Dole ne a yi kiran salla da Ikama a cikin harshen
larabci kuma bisa ka’idojin larabcin,don haka idan aka yi kiran salla ko ikama
da wani harshe na daban ko kuma ba bisa ka’idojin larabci ba,ko kuma aka sanya
wani harafin a wajen wani,a nan wannan kiran salla ko ikama bas u inganta ba.
Mas’ala ta 952:Ana kiran salla da Ikama ne bayan shigowar
lokacin sallar,don haka idan a ka yi kiran salla ko Ikama kafin lokacin salla
sun baci.
Mas’ala ta 953:Idan mutum ya yi shakka kafin ya yi Ikama akan
shin ya yi kiran salla ko bai yi ba,a nan dole ne ya yi kiran salla sannan ya yi
Ikamar.Amma idan mutum ya riga ya fara Ikama sai ya yi shakka a kan cewa shin ya
yi Kiran salla ko bai yi ba, a nan ba dole bane ya ya yi kiran sallar.
Mas’ala ta 954:Idan mutum yana cikin kiran salla ko Ikama kafin
ya fadi bangare daga cikin kiran salla ko Ikam sai ya yi shakka shin ya fadi na
kafinsa ko kuwa,a nan sai ya koma ya fadi na kafinsa sannan ya cigaba.Amma
idanyana cikin wanibangare na kiran salla ko Ikama ne sai ya yi shakka a kan
shin ya fadi na kafinsa kuwa ko bai fada ba,a nan ba zai kula da wannan shakkun
nasa ba.
Mas’ala ta 955:Mustahabbi nemutum ya kalli alkibla yayin kiran
salla ,haka mustahabbi ne mutum ya kasance yana da alwalla ko wanka,haka nan
mustahabbi ne mutum ya sanya yatsansa a ckin kunnuwa ya yin kiran salla, sannan
mustahabbi ne mutum ya daga muryarsa,sannan kada ya sanya tsakani mai tsawo
tsakanin jimlolin kiran salla, sannan kada mutu ya yi Magana tsakanin jimlolin
kiran sallar.
Mas’ala ta 956:Mustahabbi ne jikin mutum ya kasance a natse ya
yi tada Ikama,sannan mustahabbi ne kada mutum ya daga muryarsa kamar yadda yake
kiran salla,sannan kada ya bada tazara tsakanin jimlolin Ikama kamar yadda yake
badwa a cikin kiran salla.
Mas’ala ta 957:Mustahabbi ne mutum ya yi taki daya tsakanin
kiran salla da Ikama ko kuma mutum ya dan zauna ko ya yi sujjada ko ya yi zikiri
ko kuma ya yi addu’a ko ya dan yi shiru ko kuma ya yi Magana ko kuma ya yi salla
raka’a biyu,amma mustahhabi ne mutum ya yi Magana tsakanin kiran sallar Asuba da
ikamarta,haka nan ba mustahabbi ba ne mutum ya yi nafila tsakanin kiran sallar
magrib da Ikamarta.
Mas’ala ta 958:Mustahabbi ne a sanya wanda zai yi rika kiran
salla ya zama adali kuma wanda ya san lokaci,sannan ya zamana yana da murya mai
kara,kuma mustahabbi ne ya zama inda ake kiran salla yana da bisa,amma idan da
lasifika ake yin kiran sallar babu laifi idan mai kiran salla ya kasance a wurin
da ba ya da bisa.
Mas’ala ta 959:Kiran salla daga rediyo ko rikoda bay a wadatarwa
don haka dole masu salla su kira salla da kansu.
Mas’ala ta 960:Ihtiyat wajib dole ne a yi niyyar yin salla yayin
kiran salla, don haka idan aka yi kiran salla da niyyar sanar da lokaci,yin
salla ba tare da sake wani kiran salla ba yana da matsala.
Mas’la ta 961:Idan aka yi kiran salla da niyyar yin salla ba a
cikin jma’I ba, sai mutanen suka bukaci mutum day a yi musu limanci ko shi da
kansa ya yana so ya bi sallar jam’I a nan wannan kiran sallar da ya yi bai
wadatar ba, don hakamustahabi ne a sake wani kiran sallar.
Abubuwan da suke wajibi a cikin salla:
Abubuwa sha daya ne wajibi a cikin salla:
1-Niyya 2-tsayuwa 3-kabbarar harama 4-Ruku’u 5-Sujjada 6-karatu
7-zikiri a cikin ruku’u da sujjada 8-tahiya 9-sallama 10-jerantawa tsakanin
ayyukan salla 11-yin ayyukan salla ba tare da tazara ba.
Mas’ala ta 962:Wsu daga cikin wajiban salla rukunai ne,wato idan
mutum bai yi daya daga ckinsu ba ko kuma ya kara wani abu ko ya rage,da gangan
ne ko cikin kuskure sallarsa ta bacci,sannan akwai wadan dab a rukunai ban e
wato idan mutum a cikinmantuwa ya kara ko rage wani daga ciki sallarsa ba ta
baci ba.Sannan wadn rukunai guda biyar ne kamar haka:
Niya-Kabbarar harama-tsayuwa domin kabbarar harama da tsayuwa
wanda yake za a yi ruku’u-Ruku’u-Sujjada guda biyu.
Niyya:
Mas’ala ta 963:Dole mutum ya yi niyyar aiwatar da salla
sakamakon umurnin Ubangiji,sannan ba dole bane mutum ya yi wannan niyyar da
lafazin baka,kudurawa cikin zuciya ya wadatar,sannan ba dole ba ne mutumya ce
zan yi salla zuhr raka’a hudu domin aiwatar da umurnin Allah.
Mas’ala ta 964:Idan mutum ya yi niyyar yin salla raka’a hudu a
salla zuhr ko Asr Amma bai bayyana wace salla ce ba zai aiwatar wato Zuhr ce Ko
Asr, a nan sallarsa t abaci.Sannan wanda yake da ramuwar sallar Zuhr a kansa, a
nan zai yi sallar Zuhr idan bai ayyana ba ba cewa zai yi Zuhr nr ko kuma zai yi
ramuwar wadda ake binsa ne, a nan sallarsa t abaci.
Mas’ala ta 965:Dole ne mutum ya dawwama a cikin niyyarsa daga
farkon salla har zuwa karshenta,don haka idan hankalin mutum ya tafi a kan yana
cikin salla ne ta yadda idan da za a tambaye sa me kake yi ba zai bad a amsa ba,
a nan sallarsa t abaci.
Mas’ala ta 966:Dole mutum ya yi salla da niyyar aiwatar da
umurnin Allah kawai,don haka idan mutum ya yi salla da wata manufa ko don ya
nunawa mutane yana yin salla,sallarsa ta baci,wannan kuwa ya yi ne kawai domin
mutanen ko kuma domin Allah da kuma mutane wato ya yi da niyya biyu.
Mas’ala ta 967:Idan mutu ya yi wani bangaren salla domin wani ba
Allah ba, a nan ma sallarsa ta baci,wato ya yi kamar fatiha da sura wadn da suke
wajibi ne ko kuma yi wani abu wanda yake mustahabbi ne,ko kuma mutum ya yi
dukkan sallarsa domin Allah amma ya yi sallar ne a wani wuri na musammankamar
masallaci ko kuma ya yi sallarsa ne farkon lokaci domin ya nunawa mutane ko kuma
ya yi sallarne a cikin jama’a domin hakan, a nan duka sallarsa ta baci.
Kabbarar harama:
Mas’ala ta 968:Fadin Allahu Akbar a farkon kowace salla wajibi
ne,Sannan dole ne fadi Allahu akbar ba tare da tazara ba tsakanin kalmomin guda
biyu,sannan dole a kiyaye ka’idojin larabci wajen fadar wadan nan kalmomi guda
biyu ta yadda zamu fade su kamar yadda larabawa suke fada.Saboda haka idan uka
fade sub a dai-dai ba,ko kuma muka fadi ma’anarsu da wani harshe wato
fassararsu wannan kabbarar ba ta inganta ba.
Mas’ala ta 969:Ihtiyat wajib shi ne kada hada kabbarar harama da
abin za a yi kafinta misali Ikama, dole ne a samu tazara tsakaninsu.
Mas’ala ta 970:Idan mutum yana so ya hada kabbarar harama da
abin da zai yi bayan kabbarar kamar karatun fatiha,a nana bin day a fi shi ne
sai hade “RA’un” din cikin akbar da bismillah,duk da cewa ihtiyat mustahab shi
ne kada a hada kabbarar da abin da yake bayanta.
Mas’ala ta 971:Dole ne jikin mutum ya zama ya natsu yayin fadar
kabbarar harama,saboda haka idan mutum ya yi kabbarar harama yayin da jikinsa
yana rawa kuma da gan-gan wannan kabbarar ta baci,sannan idan a cikin kuskure
mutum ya motsa jikinsa yayin kabbarar ihtiyat wajib shi ne ya yi wani abu mai
bata salla sannan ya sake wata kabbarar haramar.
Mas’ala ta 972:Dole ne mutum ya yi kabbarar harama,karatun
fatiha da zikirin ruku’u da sujjada da addu’a ta yadda shi da kansa zai iya
ji,amma idan ya kasance akwai hayaniya ko wani abu makamancin hakan wanda zai
iya hana shi ya ji,a nan sai ya yi ta yadda idan babu abin da zai hana ya ji zai
iya ji.
Mas’ala ta 973:Mutumda yake bay a iya yin Magana sakamakon wata
matsala ba zai iya fadar Allahu Akbar ba da kyau a nan duk yadda yake iyawa sai
ya fada ya wadatar,sannan idan bay a iya fada a nan sai ya yi nuni a cikin
zuciyarsa sannan idan zai iya motsa harshen sai ya yi hakan.
Mas’ala ta 974:Mustahabbi mutum ya karanta wannan addu’ar kafin
kabbarar harama kamar haka:
يا مُحْسِنُ قَدْ اَتَاكَ الْمُسِيَىءُ
وَقَد اَمَرْتَ الْمُحْسِنَ اَنْ يَتَجاوَزَ عَنِ الْمُسِيىء أنْتَ الْمُحْسِنُ
وَاَناَ المُسِىءُ بِحَقِّ
مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد صَلِّ عَلَى
مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد وَتَجاوَزَ عَنْ قَبيحِ ما تَعْلَمُ مِنِّى
Ma’anarta, ya ubangiji wanda yake kayutatawa ga bayinsa,bawanka
mai yawan sabo ya zo a wajenka,ya ubangiji ka yi umurni da kyautatawa wato
bayinka su yafe wa masu munanawa,ya ubangiji ni mai sabo ne, domin darajar manzo
da alayensa (tsira da amincinka su tabbata garesu) ka yafe mani munana da
zunubban da ka san na aikata ya ubangiji.
Mas’ala ta 975:Mustahabbi ne mutum ya daga hannayensa yayin
kabbarar salla har zuwa saitin kunnuwa,haka nan a sauran kabbarorin da yake yi a
cikin salla.
Mas’ala ta 976:Idan mutum ya yi shakka a kan ya yi kabbarar
harama ko bai yi ba,sannan ya riga ya fara wani abu kamar karatun fatiha ko wani
zikiri da ake yi kafin karatun, a nan kada ya kula da shakkunsa,amma idan bai
riga ya fara wani abu ba a nan dole ne ya sake kabbarar harama sannan ya cigaba
da sallarsa.
Mas’ala ta 977:Idan mutum bayan y agama kabbarar harama sai ya
yi shakka a kan cewa shin kabbararsa ta inganta ko kuwa,a nan kada mutum ya kula
da wannan shakkun nasa.Amma mustahabbi ne mutum bayan gama sallar ya sake yin
wata.
Tsayuwar salla:
Mas’ala ta 978:Tsayuwa domin kabbarar harama da tsayuwa wanda
yake hade da ruku’u wajibi ne na rukuni,amma tsayuwa yayin karatun fatiha da
sura da kuma tsayuwa bayan ruku’u ba rukuni ba ne,saboda haka idan mutum ya bar
shi a kan mantuwa sallarsa ta inganta.
Mas’ala ta 979:Wajibi ne mtum ya dan tsaya kafin kabbar hakan
bayan kabbarar harama ta yadda zai samu yakini a kan cewa ya yi kabbarar a
tsaye.
Mas’ala ta 980:Idan mutum ya manta bai yi ruku’u ba bayan ya
gama karatun fatiha da sura,sai mutmya duka domin yinsujjada,sai mutum ya tuna
da cewa bai yi ruku’u ba,a nan sai mutu ya mike daga dukawar da ya yi sannan ya
gabatar da ruku’un domin idan ba a yi tsayuwa ba kafin ruku’u, ruku’u bai
inganta ba,sannan sallar ta baci.
Mas’ala ta 980’981:Yayin da mutum yake a tsaye odle ya kiyaye
kada ya motsa jikinsa sannan kada ya lankwasa wani sashe,sannan kada mutum ya
jingina da wani abu,amma idan wata masatala ta sa mutum sai jingina ko kuma
yayin ruku’u ya zama dole ya damn motsa jikinsa,a nan babu matsala.
Mas’ala ta 982:Idan mutum yayin da yake tsaye sai ya manta ya ya
motsa jikinsa,ko kuma dan rankwasa a wani sashe,ko kuma ya dan jingina da wani
abu,a nan babu wani abu.Amma idan ya zamana wannan ya faru ne a lokacin da yake
kabbarar harama da lokacin da yake shirin ruku’u,a nan koda a halin mantuwa ne
ihtiyat wahib shi ne ya sake sallarsa.
Mas’ala ta 983:Dole ne yayin da mutum yake a tsaye duka
kafafunsa guda biyu su zama suna bisa kasa,amma ba dole a ne nauyin jikinsa ya
zama bisa duka guda biyun,don haka idan ya zamana nauyin jikinsa yana bisa kafa
daya ne babu wani laifi.
Mas’ala ta 984:Mutumin da yake iya tsayuwa da kayu idan ya ware
kafafunsa da yawa ta yadda ba za a iya cewa yana tsaye ba, a nan sallarsa ta
baci.
Mas’ala ta 985:Lokacin da mutum yake cikin salla idan yana so ya
dan tafi gaba ko baya ko ya dan rankwasa hagu ko dama, a nan yayin da yake cikin
wannn halin,sai dai yayin da mutmzai tashi tsaye bayan ya gama sujja ko tahiya,
a nan sai ya ce” BIHAULILLAHI WA KUWWATIHI AKUMU WA AK’UD”Sanann dole jikin
mutum ya zmaa a natse ba tare da motsi ba yayin da yake zikirin wajibi sannan
ihtiyat wajib ya kiyaye hakan yayin zikiri na mustahabbi.
Mas’ala ta 986:Idan mutum yayin zikiri ya motsa jikinsa misali
lokacin da mutum yake tafiya ruku’a ko lokacin da mutum yake tafiya zuwa sujjada
sai ya yi kabbara sannan kuma da niyyar ya yi wanda ya kamata ya yi ne a lokacin
da yayin sujjada a nan dole ne mutum ya sake sallarsa,amma idan mutum ya yi
nekawai da niyyar ya yi zikiri a nan sallarsa ta inganta.
Mas’ala ta 987: Babu laifi don mutum ya Motsa hannu ko dan yatsa
yayin karanta fatiha duk da cewa ihtiyat mustahab shi ne barin haka shi ya fi.
Mas’ala ta 988:Idan yayi motsi da jikinsa ba tare da sonsa ba
yayin karanta fatiha da sura ko zikirin wajibi ta yadda jikinsa ya fita daga
natsuwar ta kamata,ihiyat wajib shi ne ya sake karanta abin da ya karanta
lokacin da jikinsa yake motsi.
Masa’ala ta 989:Idan mutum ya kasa tsayuwa yana cikin salla a
nan dole ya zauna ya yi sallar daga zaune,idan kuwa mutum ya kasa zaman,sai ya
yi sallarsa daga kwance amma ya loakacin da jikinsa bai samu natsuwa ba kada ya
karanta wani abu daga abubuwan wajibai na salla.
Mas’ala ta 990:Madamar mutum yana iya tsayuwa wajen salla to bai
halitta bay a zauna domin ya yi salla misali mututmin da jiknsa yakerawa idan
yana tsaye, ko kuma jikin dole sai ya duka ko kuma dole sai ya jingina da wani
ko kuma dole ya bude kafafunsa da yawa fiye da yadda aka saba a nan dai duk
yadda yake iyawa sai ya gabatar da sallarsa a hakan, amma idan ba zai iay yin
kowane daya daga abin da muka fada a sama ba, wato ba zai iya tsayuwa ba ko
kamar yadda mutum yake ruku’u, a nan sai mutum ya zauna ta bangaren dama domin
ya yi sallarsa.
Mas’ala ta 991:Matukar mutum yana iya zauniya ba zai yi salla
daga kwance ba,sannan idan utumba zai iya zauniya ba ta bangaren dama ba sai ya
zauna ta hagu ko kuma duk yadda yake iyawa,,sannan idan mutumba zai iya zama ba
ko ta yaya, a nan sai ya yi amfani da hukuncin da a ka fada a cikn hukuncin
Alkibla,wato mutum ya kwanta ta bangaren dama idankuwa bay a iya yin hakan sai
ya kwanta ta bangaren hagu,idan kuwa haka ba zai yiwu ba, sai mutum ya kwanta da
bayansa,ta yadda tafukan kafarsa zasu kalli Alkibla.
Mas’ala ta 992:Mutumin da yake yin salla a zaune, amma bayan
ya karanta fatiha da sura sai ya ji yana iya tashi tsaye ta yadda zai iya yin
ruku’u daga tsaye a nan dole ne ya tashi tsaye domin ya yi ruku’un daga
tsaye,amma idan mutumba zai iya tashi a tsaye ba, sai ya yi ruku’n daga zaune.
Mas’ala ta 993:Mutumin da yake salla a kwance sai ya samu dama
zai iya tashi tsaye, a nan dole ne ya tashi tsayen domin ya gabatar da abin da
yke iya yi daga tsaye,amma madamar jikinsa bai samu natsuwa ba kada ya karanta
wani abu daga cikin wajiban salla.
Mas’ala ta 994:Mutumin da yake iya tsayuwa amma sai ya ji tsoron
kada wani abu ya cutar da shi,a nan yana iya yin sallarsa a zaune,idan ya ji
tsoron hakan daga zaune sai ya kwanta ya yi sallar daga kwance.
Mas’ala ta 995:Idan mutumya samu yakinin cewa kafin lokacin
salla ya fita zai samu sauki a ihtiyat wajob shi ne ya jinkirtawa ta yadda zai
yi sallarsa daga tsaye a karshen lokacin,a nan ma idan ya kasa sai ya gabatar da
salarsa daga zaune,amma idan mutum yana tsammani ne matsalarsa zata gushe zuwa
karshen lokaci,a nana bin ya fi shi ne ya jinkirtawa zuwa karshen lokacin.
Mas’ala ta 996:Mustahabbi ne mutum ya rike jikinsa ta bangaren
dama yayin da yake tsaye yana salla sannan ya dan rankwasa kafadunsa zuwa
kasa,sanna mustahabbi ne mutum ya a za hannuwansa bisa cinyoyinsa,sannan mtum ya
matsa yatsunsa,sannan mustahabbi ne mutum ya rika kallon wurin da yake sujjada
yayin da yake tsaye,sannan mustahabbi ne mutum ya raba nauyinsa ga kafafuwansa
guda biyu ta dama da ta hagu,sannan mutumya kasance a cikin kaskantar da kai da
natsuwa,sannan kada ya saba kafafuwansa gaba da baya,idan mai salla namiji ne ya
dan ware kafafuwansa mafi karanci kamar fadin yatsa uku zuwa kamun hannu
guda,amma idan mace ce dole ne ta hade kafafunta yayin salla.
|