Da sunan Allah mai rahama
Godiya ta tabbat ga Allah Ubangujin halittu, tsira da minci sun tabbata ga
manzonsa Muhammad s.a.w.a da iyalansa tsarkaka.Sannan hushin Allah ya tabata ga
makiyansu har zuwa ranar tashin kiyama.
Hukuncin Taklidi
Mas'ala ta 1: dangane da abinda ya shafi akida dole ne mutum ya samu
yakini akan duk abin day a shafi wannan bangaren, wannan yakini kuwa ta
kowace hanya ya samu ya wadatar.wato ko ta hanyar dalilai na hankali ko
kum tahnayar iyay ne, muhimmmi dai mutum ya amu yakini da tabbas akan abin.ko
kuma daga malamai masu kiran al'umma zuwa ga ddinini Allh., ko da kuwa su ka sa
kawo dalilan hankali masu karfi.
Mas'la ta 2: mutum akan abin da bai shafi akida ko shika-hikan
adini ba, kodai ya kasance mujtahidi wato wanda yake iya fito da hukunce hukunce
da kansa aga kur'ani da sunna, ko kuma ya zama ya samu wanda yake iya yin hakan
ta yadda zai rika taklidi (koyi) da shi.ko kuma hanya ta uku shi ne ya ksance
mai ihtiyat(wato kamar idan malamai sun yi sabani akan wani abu kamar wasu sub a
da hukuncin cewa wannan abin haram ne wasu kuma su ce ba haram ba ne, sai ya
zabi cewa haram ne. ko kuma wasu su ce wannan abin wajibi ne wasu kuma su ce
mustahabi ne zai ya zabi cewa wajibi ne) yin haka kuwa yana da wahala kuma
dole sai mutum ya san wadannan sharudda da fatawoyin malami akan hakan.
Mas'ala ta uku 3:mutumin dab a mujtahidi ban e kuma ba ya taklidi a
cikin ayyukansa, to ayyukansa sun baci, saiya yi aiki da mas'ala ta 15.
Mas'ala ta 4:Taklidi a cikin ayyuka shi ne aiki da fatawoyin
mujtahidin da ya cika sharudda.mujtahidin da kuwa ya dace ayi taklidi da shi ne
kamar haka:Namiji, baligi, mai hankali, Dan shi'a imamiyya,dan halas,rayayye
kuma ya ksance adali.Abin kuwa ake nufi da adalci anna shi ne ya ksance yana
karfin zuciya ta yadda yana iya aikata wajibai sannan ya kauracewa kaba'ira.Abin
da ya fi shi ne mujtahidi kuma ya kasance mai gudun duniya.Sannan kuma
daga cikin sharudda ya kasance ya fi duk sauran mujtahidai ilimi ato ya fi
sauran malaman zamaninsa sanin hukunce-hukunce.
Mas'ala ta 5:Daya daga cikn hanyar gane mutum adali ne shi ne
zahirinsa ya zama mai kyau ne, wato ta hanyar ma'amala da shi mutum ya gane cewa
mutumin kirki ne wanda ba ya sabon Allah Sannan kuma yana aikata abin ya
wajaba a kansa, kuma na tare da shi su tabbatar da hakan.
Mas'ala ta 6:Idan ya ksance tsakanin malami biyu duk ilminsu daya
ne,to abin day a fi ka yi takalidi da wanda ya fi tsorn Allah da gudun duniya.
Mas'ala ta 7:Ana sani wanda ya fi kowa ilimi daga cikin mujtahida ta
hanyoyi gudu uku kamar haka:
Ta daya:mutum ya samu yakini ko natsuwa da kansa a State>place>kanplace>State>
cewa wannan malamim ya fi saura, kamar idan mutum ya kasance yana da ilimin da
zai gane hakan.
Ta biyu:mutum biyu masana sub a da shedar cewa lallai wannan malamin shi ne
wanda ya fi kowa ilimi, sannan kuma babu wanda ya yi sabani da su akan cewa ya
fi kowa din.
Ta uku:Ya zama labari ya yadu akan cewa shi mjtahidi ne kuma yafi kowa ilimi
daga cikin malaman zamaninsa, Ta yadda mutum zai samu yakini akan hakan.
Mas'ala ta 8:Idan gane cewa wannan malami ya fi kowa ilimi ya wuyata,
to mutum yana iya yin taklidi da duk malamin da yake kyautata zaton cewa shi ne
ya fi kowa ilimin. Sannan idan mutum yana ganin cewa mutum biyu dai-dai suke a
cikin liimi yana iya zabar ko wan e ya ga dama a cikin su. Haka kuma mutum Idan
ya fahimci cewa daya ya fi ilimi a cikin wasu abubuwa na musamman a cikin fikhu
to sai ya yi taklidi da shi a cikin wadannan abubuwan.
Mas'ala ta 9: Ana samun fatwar mujtahidi ta hanyoyi guda uku:
A:mutum ya ji daga mujtahidin.
B:mutum yaji ta hanyar adali biyu wadan suka ji fatwar; amm dogara da maganar
mutum dya yana da matsala, sai dai idan mutum yana da tabbas akan cewa mutumim
ba zai fada masa karya ba.
D:,utu, ya ga fatawar daga littafin da malamin ya rubuta sannan ya amu yakini
akan cewa shi ya rubuta hakan.
Mas'ala ta 10:Takalidi yana zama dole ne kawai a cikin abubuwan da
suka wajaba, Amma sauran abubuwan da suke ,mustahabai; ba dole ne ba mutum ya
yi takalidi a cikinsu, sai dai idan ya kasance yana tsammanin cewa wannan
mustahabbin mai yiwuwa wajibi ne.
Mas'ala ta 11:Ya zuwa lokacin da mutum bai samu yakini ba akan cewa
mujtahidi ya canza fatwarsa to iya amfani da abin malamin ya rubuta a cikin
littafinsa.sannan ba dole ban e mutum ya yi bincike akan hakan.
Mas'ala ta 12:Ya halitta mutum ya cigaba da taklidi da malamin da yake
taklidi da shi ko da Allah ya yi masa cikawa, ko da kuwa sun yi dai-dai da
malamin da yake raye a cikin ilimi.Sannan idan daya daga cikin ya fi ilimi
wajibi ne ya zabi wanda ya fin.Sannan babu bambanci a ciki ci gaba da taklidi da
mas'alolin da ya yi aiki da su a lokacin da yake darai ko kuma bai yi aiki da su
ba.
Mas'ala ta 13:Ya halitta mutum ya koma zuwa ga wani mujtahidi rayayye
daga wani mujtahidi makamancinsa idan sun kasance dai-dai suke a cikin
ilimi.Amma idaya ya fi ilimi to ya wajaba ya koma zuwa gare shi.
Mas'ala ta 14: idan mujtahidi ya canza fatawarsa yin aiki da fatawar
farko;amma idan fatawar farko yin aiki da ita ya ksance ihtiyati ne to ya kamata
mutum ya yi aiki da ita. Wato kamar da ya yi fatawa da wajibci yanzu kuma sai ya
yi fatqwa da cewa mustahabi ne.
Mas'ala ta 15:Idan mutum ya yi ibada lokaci mai tsawo day a gabata ba
tare da tahlidi ba, sannan bai san yawan wannan ibada day a yi ba tare da
taklidi ba, idan ya gane cewa wannnan ibadar day a yi ta dace da fatawar wanda
ya kamat ya yi taklidi da shi to ibadarsa ta inganta, amma idan ba haka ba to
dole ne ya rama abin da ya gabata, amma fa wannnan idan yakasance wannan
mujtahidin da ya kamata yayi taklidi da shi ya yi fatawa da cewa sai an
rama hakan.Sannan zai rama abin da yake ganin cewa lallai ya biya abin da ake
binsa.
Mas'ala ta 16:Wajibi ne mutum ya yi taklidi da mujtahidin da
yake yafi kowa ilimi akan mas'alar taklidi da wanda ya fi kowa ilimi.
Mas'la ta 17: Idan yaksance wannan malamin ya fi ilimi akan abin da ya
shafi ibada wani kuma ya fi ilimi akan abin ya shafi ma'amala to yan iya
taklidi da kowa wane daga cikinsu akan abin da yafi ilimi a cikinsa.
Mas'ala ta 18:Wajibi ne mutum ya yi aiki da ihtiyat a lokacin da yake
neman wanda ya fi ilimi.
Mas'la ta 19:Idan mujtahidi ya bad a fatwa akan wajibci, bai halitta
ba wanda yake taklidi da shi ya yi taklidi da wani mujtahidi daban, amma idan
wannan malamin ba fatwa ya ba da ba ya kasance ihtiyat wajib ne, to mutum yana
iya taklidi da fatawar wani malamin akan wannan abin.
|