Hukunce-hukuncen tsarki
Rabe-raben ruwa
Mas'ala ta 20: Ruwa kodai ya kasance zalla ne ko kuma ya zama an
gauraya shi da wani abu, misalin ruwa wanda ba zalla ba kamar lemmun kwalba ko
kuma ruwan da aka tatsa daga 'ya'yan itatuwa.ko dai makamancinsa ruwan da aka
gauraya shi da wani abu daban, ta yadda ba za a kira shi ruwa ba. Amma
wanda ba wannnan ba ana kiransa ruwa zalla wato marar gauraye. Ruwa zalla ya
kasu zuwa gida biyar:1ruwan kur.2Ruwa kadan. 3:Ruwa maigudu.3:Ruwan
sama.3:Ruwan rijiya.
A:ruwam kur:
Mas'ala ta 21: Ruwan kur shi ne, ruwan da idan za'a zuba shi a cikin
wani wuri wanda fadinsa,tsawonsa da zurfinsa ya kai kamun hannu guda uku da
rabi, ana kiaran wannan ruwan kur.
Mas'ala ta 22:Idan najasa ta shiga cikin wannan ruwan kamar fitsari ko
jini da makamntansu, sannan ruwan sakamakon hakan ya canza launi ko kanshi to
wannan ruwan ya zama najasa ba za'a iya aikin ibada da shi ba. Amma idan launi
ko kanshinsa bai canza ba to bai zama najasa ba, kuma ana iya amafani da shi a
wajen ayyukan ibada.
Mas'ala ta 23: Idan ruwan kur ya canza sakamakon wani abu wanda ba
najasa ba to ba ya zama najasa sakamakon hakan.
Mas'ala ta 24:Idan ruwa ya kasance fiye da kur, kuma wani bangare daga
cikinsa ya canza sakamakon najasa, to wannan bangaren kawai zai zama najasa.
Amma idan ruwa bai kai kur ba kuma ya canza sakammkon najasa dukkansa ya zama
najasa.
Mas'ala ta 25:Ruwan da ake sawa yana tashi sama kamar wajen rawun na
kan titi da makamantansa yayin da ya yi sama kafin ya zama digo-digo idan ya
hadu da ruwa mai najasa yana tsarkake ruwan mai najasa, amma da sharadin shi
wannan ruwan mai tashi sama ya zama yana hade da ruwan da yawansa ya kai kur
daya kamar yadda muka yi bayani a sama. Amma idan ya kasance ruwan da yake tashi
sama ya zama digo-digo sannan ya hadu da ruwa mai najasa, to a wannan halin ba
ya tsarkake ruwa mai najasa.
Mas'ala ta 26:Idan wani abu ya kasance mai najasa aka wanke shi
karkashin fanfo, sai ya kasance yayin wanke wannan abun ruwa ya billar ma mai
wanke wannan abin, idan ya kasance launi ko dandanonsa bai canza ba to wannan
wanda ya billa din ba najasa ba ne.
Mas'ala ta 27:Idan ruwan kur wani bangarensa ya zama kankara
sauran idan najasa ta shiga cikinsa ya zama najasa.
Mas'ala ta 28:Idan ruwa ya ksance yawansa ya kai yawan kur, amma sai
mutum ya yi shakka akan cewa shin yanzu ya rage ko kuwa yana nan matsayinsa na
da?hukuncinsa zai kasance kamar yadda ya san shi a da matsayin kur, sakamakon
hakan idan najasa ta shigacikinnsa sai kawai idan ya canza siffofinsa sakamakon
hakan zai zma mai najasa.. Amma ida ya kasance ruwan bai kai yawan kur ba sai
mutum yanzu yake shakka akan cewa ko ya zama kur yanzu ko bai zama ba? Hukuncin
zai zama kamar na da wato a matsayin bai kai kur ba har sai ya samu yakini ya
kai yawan kur.
Mas'ala ta 29:Ana tabbatar da kasancewar ruwa yawansa ya kai kur ta
hanya guda biyu:
A; mutum ya sami yakini da kansa akan cewa yawansa ya kai kur.
B:Adalai guda biyu su ba da shaidar cewa ya kai yawan kur.
B:Ruwa dan kadan
Mas'ala ta 30:Ruwan da bai yawan kur ba, sannan ba na sama ko rijiya
ne ba, ana kiransa ruwa dan kadan.
Mas'ala ta 31:Idan najasa ta shiga cikin ruwa dan kadan yana zama
najasa ba tare da sharadin cewa sai ya canza siffofinsa ba.Idan ruwan ya kasance
yana zuba ne daga sama wanda baikai kur ba sannan ba nasama ne ba, wanda kawai
ya taba najasa yake zama najasa.Sannan idan ya kasance kamar ruwan da yake tshi
sama ne sakamkon turo shi da ake yi sai ya hadu da najasa a sama, to na saman ne
kawai zai zama najasa, amma na kasan ba najasa ba ne.
Mas'ala ta 32:Ruwa dan kadan idan ya billa bisa najsa sannan ya sake
billa bisa wani wuri, to wannan ruwan shi ma najasa ne.Sannan ruwan da ake
amfani da shi wajen wanke abu mai najasa bayan gusar da ita kanta najasar lallai
a kaurace masa. Amma ruwan da ake wanke wurin kashi da fitsari yana zama mai
tsarki tare da sharudda kamar haka.
1-Idan bai canza kala ko dandano irin na najasar ba.
2-Idan ya zama najasar ba fita daga wadannan wuraren guda biyu ba, wato ta
kasance ta watsu a wani wuri sai ya wanke.
3-Ya zama wata najasar ba ta hadu da wannan ba daga waje.
4-ya zama babu karorin najasar a cikin ruwan.
5-Kada najasar dake wadannan wuraren guda biyu ta wuce yawan da aka saba.
C:Ruwa maigudu
Mas'ala ta 33:Ruwa maigudu shi ne ruwan da yake yana wani wuri wanda
daga can yake zuwa kamar ya zama yana bubbugowa ne daga kasa, sai ya kwarara
zuwa wani wuri.
Mas'ala ta 34:ruwan mai gudu koda yawansa bai kai kur ba, ko da najasa
zata shiga a cikinsa amma bai canza launi ko dandano ba, to yana nan matsayin
maitsarkinsa.
Mas'ala ta 35:Idan najasa ta shiga cikin ruwa maigudana bangaren da
kala ko dandanosa ya canza yana zama najasa amma sauran wanda yake hade da
inda asalinsa yake, yakan tsaya a matsayin mai tsarki, duk da yake bai kai
yawankur ba.
Mas'ala ta 36:Ruwan da yake bubbugowa amma ba ya
gudu, koda ya hadu da najasa idan siffofinsa ba su canza ba, yana nan matsayin
maitsarki.
Mas'ala ta 37: ruwan da yake kusa da kogi sannan yana hade da ruwa
maigudana, idan najasa ta hadu da shi , idan siffofinsa ba su canza ba yana nan
matsayin maitsarki.
Mas'ala ta 38:Ruwan da ke bubbugowa kamar da damina amma da bazara ba
ya bubbugowa, kawai lokcin da yake bubbuga idan najasa ta shiga cikinsa
maitsarki ne, da sharadin siffofinsa ba su canza ba.
Mas'ala ta 39: ruwan da ke cikin fayif idan sun kasane sun hade da
ruwan kur ne, koda sun hadu da najasa matukar siffofinsa ba su canza ba mai
tsarki ne.
Mas'ala ta 40:ruwan da yake gudana bisa kasa amma ba daga kasa yake
bubbugowa ba, idan ya kasance bai kai yawan kur ba, sakamakon haduwarsa da
najasa yana zama najasa.Amma idan yana gangarowa daga sama ne, to wanda ya hadu
da najasar ne kawai yake zama najasa,amma sauran da ke sama yana nan
maitsarkinsa.
D:Ruwan sama:
Mas'ala ta 41:Idan ruwan sama ya sauka a bisa abin da yake da najasa
sau daya, idan babu ainahin najasar, abin ya tsarkaka.Sannan idan ruwan saman ya
sauka bisa kamar darduma da makamantansa ba sai an matse ba yakan zama mai
tsarki.Amma fa wannan ba wai digon ruwa sau uku ba, sai ya kai yadda za'a iya ce
masa ruwan sama, kuma ya ratsa ko'ina.
Mas'ala ta 42:Idan ruwan sama ya zuba bisa abin da yake da najasa
sannan sai ya billa bisa wani abu daban, idan dai bai kasance tare da ainahin
najasar ko daya daga cikin siffofin najasar ba to maitsarki ne. Saboda haka idan
ruwan sama ya zuba bisa jinni sannan sai ya billa bia wani abu daban sai ya
kasance akwai jan jinin ko kanninsa akan abin da ya billa din, to shima ya zama
mai najasa.
Mas'ala ta43:Idan ya kasance akwai najasa akan gini sai ruwan sama ya
zuba bisa najasar har ya zuwa lokacin da ake yin ruwan, ruwan da yake zubowa
daga indararo mai tsarki ne.Amma idan aka dauke ruwan kuma an tabbatar da cewa
ruwan da yake zubowa daga indarro ya bi ta bisa najasar to shima najasa ne.
Mas'ala ta 44: kasar da ta kasance mai najasa idan ruwan sama ya zuba
a bisa ta zama mai tsarki,Idan ruwan samana ya gudana bisa kasa sannan ya isa ga
wurin da yake mai najasa, kuma yana karkashin rufi shi ma ya zama mai tsarki.
Mas'al ta 45:kasar da ta kasance mai najasa sai furanni suka fito akan
ta idan ruwan sama ya zuba akai ta tsarkaka.
Mas'ala ta 46: Idan ruwan sama ya taru a wani wuri koda bai kai yawan
kur ba, sannan lokacin da ake ruwan sai aka wanke wani abu mai najasa a cikinsa,
sannan siffofinsa ba su canza ba, abin da aka wanke din ya tsarkaka.
Mas'ala ta 47:Idan ruwan sama ya sauka akan dardumar da take akan kasa
mai najasa sannan ruwan saman ya yi gudu to dardumar ba ta zama mai najasa kuma
kasar ma ta tsarkaka.
Mas'ala ta 48: Idan ruwan sama ya taru a cikin wani wuri wanda yawansa
bai kai kur ba, sai najasa ta shiga cikinsa bayan dauke ruwan, to ya zama
mai najasa.
E-Ruwan rijiya
Mas'ala ta 49: Ruwan rijiyar da yake bubbugowa daga kasa koda bai kai
yawan kur ba, idan najasa ta shiga a cikinsa mmatukar bai canza ba yana nan
matsayin mai tsarkinsa.Amma kamar yada aka fada a cikin manyan littafai
mustahabbine a janye wannan ruwan.
Mas'ala ta 50: Idan najasa ta shiga cikin ruwan rijiya sai kuma
sifofin ruwanta ya canza.to yana zama mai tsarki ne yayin da ruwan da yake
bubbugowa daga kasa ya gauraya da mai najasar ta yadda babu sauran alamarta.
Hukunci ruwa
Mas'ala ta 51: Ruwa mai gauraye ba ya tsarkake komi, alwalla da wanka
da ruwan bay a inganta.
Mas'ala ta 52: Idan najasa ta shiga cikin ruwa mai gauraye koda kadan
ce ruwan ya zama mai najasa.
Amma idan ruwan daga sama yake zuba bisa abin yake da najasa
kawai wanda ya taba najsar ya zama mai najasa amma wanda yake sama ba zama mai
najasa ba.misali kamar idan lemun kwalba aka zuba shi cikin wani abu mai najasa
to kawai an cikin abin da ya zama mai najasa, amma sauran yana nan mai
tsarkinsa.Haka ma idan ana tura shi ne da wata na'ura ya ta shi sama, idan ya
tabo najasa kawai na saman ne zai zama mai najasa, amma na kasan yana nan mai
tsarkinsa.
Mas'ala ta 53:Idan aka zuba ruwa mai gauraye cikin ruwa mai yawa wanda
ya kai yawan kur ta yadda ba za a ce ma wannan ruwan ba ruwa gaurayayye to idan
ya kasance mai najasa kuma babu alamar najasar, to ya tsarkaka.
Mas'ala ta 54:Ruwan da ya kasance zalla amma yanzu mna shakku ko yana
nan matsayinsa na da ko yanza, hukuncinsa yana nan kamar da yana iya tsarkake
najasa.Sannan alwalla da wanka da shi yana inganta.Sanna ruwan day a kasance mai
gauraye amma yanzu muna shakku akan cewa ko ya koma zalla, shi ma hukuncinsa
kamar dai da zai kasance wato mai gauraye, kuma ayyuakan ibada da shi ba ya
inganta..
Mas'ala ta 55:Ruwan dab a a sani ba shin zalla ne ko mai gauraye ba yq
tsarkake najasa zqto hukuncinsq kamar hukuncin ruwa mai gauraye, ammma idan
yawansa ya kai kur ba a yi masa hukunci da najasa.
Mas'ala ta 56:ruwan da najasa ta shiga cikinsa kamar ka shi ko fitsari
kuma siffofinsa suka canza koda ya kasance yawansa ya kai kur ko kuma mai gudu
ne, ya zama najasa ba ya tsarkake komai.
Amma idan siffsrsa ta canza ne sakamakon wata najasa da ke kusa da shi amma
ba cikinsa ta ke ba, to ba a yi masa hukunci da najasa.
Mas'ala ta 57:Ruwan da najasa ta zuba a cikinsa kamar fitsAri ko jini,
sannan suka canza siffarsa, sai ya hadu da ruwan kur ko mai gudu ko muma ruan
sama ya zuba cikinsa, ko kuma ruwan indararo ya zuba a cikinsa yayin da ake
ruwan sama wato ta yadda ya mayar da shi kamar day a cire canjin da ua samu
yakan tsarkaka, Amma dai fi dacewa shi ne sai idan ruwan sama ko kuma wanda
yawansa ya kai kur, ya hadu da shi, sannan yake tsarkaka.
Mas'ala ta58: idan aka anke abin da ba ya bukatar a matsa shi a cikin
ruwan da ya kai yawan kur, ruwan da ya ke zuba bayan fito da shi daga ruwan mai
tsarki ne.Amma abubuwan da suke bukatar a matse su kamar kayan sawa mafi dacewa
a kauce ma wannan ruwan najasa ne.
Mas'ala ta 59:Ruwan da ya kasance mai tsarki amma yanzu muna shakku
akan tsarkinsa, hukuncinsa mai tsarki ne.Haka ruwan da ya kasance mai najasa
yanzu muna shakku akan najasarsa, hukuncinsa kamar dai da wato mai najasa ne.
Mas'ala ta 60:Abin da kare ko alade da kafiri suka ci suka rage najasa
ne; kuma cinsa haramun ne. sauran dabbobin da cinsu haramun ne, abin da suka
rage mai tsarki ne amma cinsa makaruhi ne
|