|
||||||||||||||||||||||
|
Hukuncin wuraren zuba abinci da makamantansuMas'ala ta 230: Abin da aka yi daga fatar kare ko alade ci ko shan wani abu a ciki haram ne.Sanna bai halitta ba ayi amfani da su a wajen alwalla ko wani abu da yake sharadi ne sai abu mai tsarki ake amfani da shi.Abin ya fi shi ne, har abin da ba sharadi ba ne sai da abu mai tsarki a kaurace wa amfani da su.Haka nan fatar ko kare , alade da abin da yake mushe a kaurace ma ta. Mas'ala ta 231:Ci ko shan wani abu a cikin kwanon da ka yi da zinari ko azurfa haramun ne,amma aji je su don kwalliya ko wani daban babu laifi. Mas'ala ta 232:kera kwano ko amsar lada wajen kera shi ba bu laifi. Mas'ala ta 233:Hakan saye ko satar da kwanon zinari ko azurfa bay a da laifi. Mas'ala ta 234:Hanun kofi da ake yi da zinari ko azurfa idan da za a cire kofin a bar hannun kawai ta yadda za,a ce masa kofi, amfani da shi haramun ne, amma ba za'a iya ce ma sa kofi ba, to amfani da shi babu wani abu. Mas'ala ta 235:Amfani da kwanon da aka yi wa kwalliya da ruwan zinari ko azurfa babu laifi. Mas'ala ta 236:Idan aka cakuda azurfa ko zinari da karfe aka kera kwano ko tukunya ta yadda karfen yana da yawa ba za a iya cewa wannan kwanon na zinari ba, amfani da shi ba shi da wani laifi. Mas'ala ta 237:Idan mutum ya sanya abinci a cikin kwanon zinari ko azurfa da nufin cewa idan zai ci zai maida a cikin wani kwanon da ba wannan ba, yin wannan amfani haramun ne, amma idan ya canza kwano ne da nufin cewa bai san cewa ba cin abinci a cikin kwanon zinari haramun ne ba, sai ya canza zuwa wani kwanon da ba haram ba, to wannan babu laifi. Mas'ala ta 238:Yin amfani da zinari wajen kan takobi ko abin shafa kwalli ko marfin kwalbar turare da makmantansu babu laifi. Mas'a'al ta 239:Idan mutum ya yi amfani da kwanon zinari ko azurfa a halin da babu yadda zai yi, babu laifi.Amma yin wanka ko alwalla a cikin irin wadan nan wuraren ko cikin halin da ba wani sai su, yana da matsala. Mas'ala ta 240:Yin amfani da abin da mutum yake shakku akan cewa shin zinari ne ko wani daban babu matsala.
|