Home Page
 Tarihin rayuwarsa
   Akidojin Shi'a
   Littafansa
   Fatawoyi
   Sakonni
   Darussa
   Littafan dansa
   Dakin karatu
   Hotuna


Affiliate Websites
Affiliate Websites

   E-Mail Listing:


 

Baya kanu Gaba

Alwalla

Mas'ala ta 241: Wajibi ne a wanke hannu ka fuska sannan a shafi gaba kai da kafa a wajen alwalla.

Mas'ala ta 242:Tsawon fuska yana faraway ne daga inda gashi yake fitowa zuwa karshen haba,sanann fadinta yana farawa ya hada ne da iyakar inda babban yasaa da na tsakiya suke rutsa, saboda haka dole a wanke nan yayin alwalla,sannan don samu tabbas ya kamata mutum ya wanke har zuwa wajen kunne.

Mas'ala ta 243:Idan ya kasance hanuwa ko fruskar mutum ta kasa ko ta wuce yadda aka sab sai mutum ya wanke iyaka inda sauran mutane suke wakewa.Amma idan hannu da ukarka duk sun wuce na sauran mutane,amma sun dace da juna, to anan ba dole ba ne ya kula da inda sauran muatne suke wankewa,sai kawai ya yi amfani da yaddamuka fada a mas'alar da ta gabata.Sanana idan gashi ya fito a bias goshinsa ko kuma baya da gashi a gaban kansa, ana sai ya yi aiki da misalin inda ya kamata a ce ya fito.

Mas'ala ta 244:Idan mutum ya yi tsammanin cewa akwai maiko a bias gira ko wani wurin da kae wanke wa yayin alawalla kuma ya yi dai fai da sauran mutane cewa ruwa ba zai iya isa ba ba bias fata, to a nan sai ya gusar da wannan maikon kafin ya yi alwalla.

Mas'ala ta 245: Idan babu gashi a wurin da ya kama ya fito a bias fuska dole ne ya isar da ruwa a bias fata yayin alwalla, amma idan akwai gashin a wurin ba dole ban e sai isar da ruwa bias fatar, wanke saman gashin ya wadatar.

Mas'ala ta 246:Ammam idan mutum yana shakku akan cewa shin akwai gashi ko babu a wurin day a kamata a ce ya fito, a nan abin day a fi shi ne ya wanke sman gashin kuma ya isar da ruwa bisa fatar.

Mas'ala ta 247:Ba dole ba ne wanke cikin hanci ko idanu ta yadda idan an rufe bai ko hanci ba za gan wurin ba

Mas’ala ta 248:Dole a wanke fuska daga sama zuwa kasa,Idan aka  wanke daga kasa zuwa sama akwai matsala dangane da alwallar,Haka nan ma hannuwa dole a wamke daga guiwar hannu zuwa ‘yan yatsau.

Mas’ala ta 249: Idan bayan an wanke fuska sai aka shafa hannu a kan fuskar ta rowan da ke akan fuska ya jika hannu ta yadda har ruwa ya yi gudu akan hannun ya wadatar a wanke hannun da shi ba sai an zuba wani ruwa ba na musamman a kan hannun.

Mas’la ta 250: Bayn an wanke fuska dole ne a farad a wanke hannun dama daga guiwar hannu zuwa “yan yatsu sannan hagi kamar hakan.

Mas’ala ta 251: Don mutum ya samu tabbas aka cewa ya wanke hannunsa daga guiwa ya kamata ya wanke daga saman guiwar ta yadda zai samu yakini ya wanke da kyau.

Mas’ala ta 252: Wanda ya wanke hannayensa zuwa wuyan hannu kafin ya wanke fuska Lokacin day a zo wanke hannaye yayin alwalla dole ne ya wanke hannayensa har zuwa ‘yan yatsu,Idan kuwa ya wanke hannayensa kawai zuwa wuyan hannu alwallarsa ta baci.

Mas’ala ta 253:Ya yin alwalla wanke fuska sau daya wajibi ne sau ya halitta a wanke sau biyu,amma sau uku da saman hakan haramun ne, Idan aka iya wanke dukkan gabban alwalla da ruwa tafin hannu daya,za,a lissafa shi akan wankewa sau daya, koda ya yi nufin sau daya ne ko bai yi ba.

Mas'ala ta 254:Idan mutum y agama wanke hannayensa yayin alwalla, sai ya shafi kansa da lemar dake jikin hannun, ba dole ba ne ya zma da hannun dama ko ya fara daga sama zuwa kasa.

Mas'ala ta 255:Daya daga cikin hudu idan aka raba kai hudu bangaren da goshi yake nan ne wajen shafa yayin alwalla.Ko ya, ya kasance mutum ya shafa daga cikin wannan bangaren ya wadatar,duk da cewa mustahabbi ne mutum ya yishafar tsawonta ya kai tsawon dan yatsa, fadinta kuwa ya kai fadin yatsu uku.

Mas'ala ta 256: Ba dole ba ne shafar kai ya zama akan fatar kai,Ya wadatar a shafi gashin gaban kai.Amma idan ya kasanshe gashin mutum yana da yawa ta yadda idan ya zubo shi gaba zai rufe har zuwa goshinsa, anan abinda ya fi shi ne ya shafi gindin gashin yayin alwalla, ko kuma ya buda gashin ya shafi fatar kan.Idan kuma gashin ya kasance yana zuba bisa fuska ne anan, sai ya tattara gashin ya yi shafar a gaban kai kamar yadda muka yi bayani a baya..Idan mutum ya yi shafa akan gashin dab a na gaban kai ba wato gashin wani wuri ne ya zubo bisa gaban kai, anan shafarsa ta baci.

Mas;ala ta 257:Bayan gama shafar kai ,za'a shafi kafa da wannan  lemar da ta rage wajen shafar kan, yadda ake yin shafar kafar kuwa shi ne za'a shafi kafar ne da kan yatsun hannu.

Mas'ala ta 258:Fadin wurin da za'a shafa yayin shfar kfa ya kasance ta yadda za'a iya cewa yana da fadi, duk da yake ihtiyat  mustahabbi shi ne, ya kasance ya kai fadi tafin hannu.

Mas'ala ta  259:Ihtiyat wajib shi ne yayin shafar kafa ya zama mutum ya dora tafin hannunsa bisa kan yatsun kafa ya jawo zuwa  wuyan kafa, saboda haka idan mutum ya dora duka hannunsa ya dan  shafa kadan akan kafar shafarsa ba ta inganta ba.

Mas'ala ta 260:Dole ne yayin shafar kai ko kafa, a shafa hannu akan kafar ko kai, amma idan mutumya a za hannunsa akn kafa ta yadda ya goga kansa ko kafarsa alhali hannunsa kawai yana akna kafar ko kan, wato aki ko kfa su ya goga bisa hannu, ba hannun ya shafa ba akan kafa ko kai, anan shafarsa ta baci.Amma idan kadan kafar ta motsa ko kai babu matsala.

Mas'ala ta 261:Dole ne wurin shafa ya kasance busasshe, idan ya kasance mai lema ta yadda lemar hannu ba zata bayya nab a kan kafa ko kai,wannan shafar t abaci. Amma idan ya zamana lemar kadan ce ta yadda lemar hannu zata bayyan akan kafa ko kai,ana babu matsala.

Mas'ala ta 262:Idan ya zamana babu lema kan hannu ta yadda za'a yi shafa da ita, bai halatta ba a tabo ruwa daga waje,dole ne a shahi lemar daga wani wuri jikin gabban alwalla,sai ayi shafar da ita.

Mas'ala ta 263:Idan ya zamana lemar dake jikin hannu zata isa ne kawai a yi shafar kai da ita , to sai a yi shafar kan da ita, sannan a gogo lema daga wani wuri daga cikin gabban alwalla a shafi kafafu da ita.

Mas'ala ta 264:Yin shafa akan safa ko takalmi ba ta inganta,amma idan ya kasance sakamakon tsorn "yan fashi ko wata dabba mai cutarwa ya yi shfa akan takalmi ko safa, ba matsala.Amma idan ya kasance saman takalmin akwai najasa dole ne ya dora wani abu mai tsarki akan takalmin sannan ya yi shafar.

Mas'ala ta 265:Idan ya kasance akwai najasa akan kafa kuma babu rowan da za'a wanke,anan dole ne mutum ya yi taimama.

Baya kanu Gaba