|
||||||||||||||||||||||
|
Alwallar irtimasMas'ala ta 266:Abin da ake nufi da alwallar irtimas shi ne, mutum ya sa hannunsa ko fuskarsa a cikin ruwa da nufin alwalla, tare da kiyaye sharuddan alwalla, wato ya fara sanya fudkar ta goshinsa zuwa habarsa dai-dai inda ake wankewa,haka hannunsa ma ya fara sanya guiwar hannun zuwa 'yan yatsu . Idan da hannun mutum ya kasance cikin ruwa ko fuskarsa sai ya yi nufin ya yi alwalla, idan lokacin da fito da hannunsa ko fuskarsa kafin ruwan ya gama zuba ne daga fuskarsa, sai ya yi niyyar alwallar ta inganta.Mas'ala ta 267:A wajen alwallar irtimasi dole kamar wadda ba ta irtimasi ba a fara wamke fuska daga sama, haka ma hannuwa.Saboda haka lokacin da mutum ya sanya fuskar a cikin ruwa idanm ya kasan ce da nufin alwalla ne dole ya fara sanya sama goshinsa zuwa gemunsa haka shima hannu kamar dai yada ake alwalla ta koda yaushe. HAka nana ma dole ne a fara dago bangaren goshin da kuma guiwar hannu, yayin fito da hannu ko fuska daga daga ruwan. mas'ala ta 268:Idan mutum ya yi alwallar irtimasi a wani bangare ya yi wadda ba irtimasi ba a wani bangare babu matsala alwallarsa ta inganta. Addu'oi'in da suke mustahabbi ne wajen yin alwalla: Mas'ala ta 269: Wan da ya ke nufin yin alwalla mustahabbi ne ya karanta wannan addu'a «بِسْمِ اللهِ وبِاللهِ وَالْحَمْدُللهِ الّذى جَعَلَ الْماءَ طَهوُراً وَلَم يَجْعَلْهُ نَجِساً» sannan idan zai fara wanke hannu ya ce « اللّهمَّ اجْعَلنى مِنَ التّوّابِينَ وَاجْعَلْنِى مِنَ المُتَطَهِّرينَ» haka nan idan zai kuskurwe baki sai ya ce, «اَللّهُمَّ لَقِّنِىِ حُجَّتِى يَوْمَ اَلْقاكَ وَاَطْلِقْ لِسانِى بِذِكْرِكَ» idan zai shaka ruwa a hanci sai ya ce: «اَللّهُمَّ لا تُحَرِّمْ عَلَىَّ ريحَ الْجَنَّةِ وَاجْعَلْنِى مِمَّن يُشُمُّ ريحَها وَروْحَها وَطيبَها» Sannan idan zai fara wanke fuska sai ya ce: « اللّهُمَّ بَيِّضْ وَجْهى يَوْمَ تَسْوَدُّ فيهِ الْوُجوُهُ وَلا تُسَوِّدْ وَجْهى يَوْمَ تَبْيَضُّ فيهِ الْوُجوُهُ» haka nan idan zai wanke hannun dama sai ya ce: «اللّهُمَّ اَعْطِنِى كِتابِى بِيَمينى وَالْخُلْدَ فِى الجنانِ بِيَسارى وَحاسِبْنى حِساباً يَسيراً» haka nan idan zai wanke hannun hagu sai ya ce: «اللّهُمَّ لا تُعْطِنِى كِتابىِ بِشمالىِ وَلا مِنْ وَراءِ ظَهْرِى وَلا تَجْعَلْها مَغْلوُلَةً اِلى عُنُقِى وَاَعوذُبِكَ مِنْ مُقَطِّعاتِ النِّيرانِ» sannan wajen shafar kai sai ya ce: «اللّهُمَّ غَشِّنِىِ بِرَحْمَتِكَ وَبَرَكاتِكَ وَعَفْوِكَ» haka nana idan zai shafi kafa sai ya ce: «اللّهُمَّ ثَبِّتْنِى عَلَى الصِّراطِ يَوْمَ تَزِلُّ فِيْهِ الاَْقْدام وَاجْعَلْ سَعْيِى فى ما يُرْضيكَ عَنِّى يا ذَالْجَلالِ وَالاِْكْرامِ»
|